Yadda yaƙin Iran zai sanya ƙasashe rige-rigen mallakar makamin nukiliya

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, Alessandra Corrêa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, From Washington (USA) to BBC News Brazil
- Lokacin karatu: Minti 6
Tun bayan da Amurka da Isra'ila suka fara kai hare-hare kan Iran a ƙarshen watan Fabrairu, ɗaya daga cikin hujjojin da ake bayarwa shi ne hana Tehran ƙera makamin nukiliya.
Sai dai fiye da wata ɗaya bayan fara yaƙin, ana fargabar cewa ɗaya daga cikin abin da rikicin zai haifar shi ne sanya ƙasashe rige-rige mallakar makamin nukiliya.
A cewar masana kan yaɗuwar makaman nukiliya da BBC ta tattauna da su, idan aka duba halin da ake ciki yanzu, ba gwamnatin Iran kaɗai ba ce za ta iya yin wannan tunani, wasu gwamnatoci ma na iya tunanin cewa babbar hanyar kariya daga samame ba ta hanyar diflomasiyya ko amfani da makaman da aka saba da su ba ne, sai dai tan hanyar mallakar nukiliya domin kare kai daga ƙasashe masu ƙarfi.
Bugu da ƙari, yaƙin ya haifar da rashin tabbas game da ƙarfin Amurka na tabbatar da tsaron ƙawayenta, musamman a lokacin da ƙasashen Gabas ta Tsakiya kamar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Saudiyya suka fuskanci hare-haren ramuwar gayya daga Iran.
A irin wannan yanayi, dogaro da kariyar Amurka kasada ce, kuma mallakar makamin nukiliya domin tsoratarwa da hana hari, na iya ƙara samun karɓuwa.
"Abin takaici ne ƙwarai cewa ɗaya daga cikin hujjojin fara yaƙin shi ne hana Iran mallakar makamin nukiliya," in ji Reid Pauly, farfesa a fannin tsaron nukiliya da manufofi a Jami'ar Brown da ke Amurka, a hirarsa da BBC.
Ya ƙara da cewa, "idan gwamnatin Iran ta tsira daga wannan yaƙi, to za ta yi nazari sosai kan yadda za ta kare kanta daga hare-hare a nan gaba. Kuma mallakar makaman nukiliya na iya zama ɗaya daga cikin hanyoyin da za su ɗauka."
"Sakamakon wannan yaƙi, akwai yiwuwar gwamnatin Iran za ta ci gaba da ƙudurinta na ƙera makaman nukiliya," in ji Pauly, marubucin littafin The Art of Coercion: Credible Threats and the Assurance Dilemma.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
John Erath, babban darakta a Cibiyar Kula da Makamai da Hana Yaɗuwar su, ya nuna damuwa kan abin da ya kira "ci gaba da jerin wasu munanan shawarwari da shugabannin ƙasashe daban-daban ke yankewa."
Erath ya bayyana cewa ana tsaka da tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran a lokacin da Isra'ila da Amurka suka kai mata hari a bara. A wannan shekarar ma, an kai mata hare-haren ne duk da cewa ana ci gaba da tattaunawa.
Ya ce maimakon a yi amfani da dukkan hanyoyin sulhu da tattaunawa, Amurka da Isra'ila sun zaɓi kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran a bara.
A cewarsa, idan aka ci gaba da ɗaukar irin waɗannan matakai marasa kyau, akwai yiwuwar Iran za ta kai ga yanke shawarar cewa abin da ya fi dacewa da ita shi ne mallakar makaman nukiliya, sannan ta fara ƙera su domin kare kanta.
Haka kuma ya ƙara da cewa Saudiyya ta riga ta bayyana cewa idan Iran ta mallaki makaman nukiliya, ita ma za ta bi sahu. Ya ce wasu ƙasashen yankin ma na iya yin koyi da hakan.
Wuraren nukiliya da Ilimin kimiyya
Shirin nukiliyar Iran ya daɗe yana zama abin damuwa ga Amurka, da Isra'ila da sauran ƙawayensu.
Iran na daga cikin ƙasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya, wata yarjejeniya ta ƙasa da ƙasa da aka fara aiki da ita tun a shekarar 1970, wadda ƙasashe kusan 190 suka amince da ita domin hana yaɗuwar makaman nukiliya da kuma ƙarfafa amfani da makamashin nukiliya don zaman lafiya.
Tehran ta daɗe tana musanta cewa tana ƙoƙarin ƙera makaman nukiliya, tana mai cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne.
Sai dai tattaunawar da ake yi kan shirin ta daɗe ba a amince da ita ba musamman kan matakan sarrafa yureniyom da kuma hanyoyin sanya ido da sauran muhimman batutuwa.
A shekarar 2018, a lokacin wa'adin mulkinsa na farko, Donald Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliya da Iran, wadda magabacinsa Barack Obama ya ƙulla.
Ana ganin cewa a ƙarƙashin jagorancin marigaryi Ali Khamenei, ƙasar na da kayan aiki da za ta iya ƙera makamin nukiliya, amma har yanzu ba ta kai wannan mataki ba.
Rahotanni daban-daban, ciki har da na jami'an Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya, sun nuna cewa babu wata hujja da ke tabbatar da cewa Iran na dab da ƙera makamin nukiliya.
Sai dai tun bayan hare-haren bara, musamman bayan rikicin wannan shekara, wasu manyan mutane a cikin gwamnatin Iran suna kira da a fice daga yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya.
John Erath ya ce, "Tabbas an lalata wasu wuraren da ake gudanar da shirin nukiliyar amma ilimin kimiyyar da ake buƙata domin ƙera makamin nukiliya yana nan daram.
A nan gaba, Iran na iya sake gina waɗannan wurare tare da amfani da wannan ilimi."
'Yaɗuwa a jere'
Reid Pauly na Jami'ar Brown ya ce idan har Iran ta mallaki makamin nukiliya, akwai haɗarin hakan zai haifar da abin da ya kira "yaɗuwar makaman nukiliya a jere" a yankin.
A halin yanzu, an amince cewa ƙasashe tara ne ke da makaman nukiliya: wato Amurka da Rasha da China da Faransa da Birtaniya da Pakistan da Indiya da Isra'ila da kuma Koriya ta Arewa. Ana kyautata zaton cewa Isra'ila ma ta mallake shi, sai dai ƙasar ba ta taɓa fitowa ta tabbatar da hakan ba.
Rahotannin jin ra'ayin jama'a a ƙasashe daban-daban, daga Koriya ta Kudu zuwa Turkiyya da Poland, na nuna cewa ana samun ƙarin goyon baya ga samar da makaman nukiliya na cikin gida.
Mutane da dama na ganin wannan a matsayin wani lokaci na rauni ga tsarin hana yaɗuwar makaman nukiliya, suna danganta hakan da ƙoƙarin China na faɗaɗa da sabunta makamanta, da kuma sanarwar da Faransa ta yi kwanan nan cewa tana son ƙara ƙarfin nata.
Alicia Sanders-Zakre ta bayyana cewa, "Matakan da waɗannan ƙasashe tara masu makaman nukiliya suka ɗauka na sabunta makamai da ƙara yawansu, ko kuma ƙirƙirar sabbin nau'o'i, sun raunana tsarin hana yaɗuwar makaman nukiliya sosai."
A farkon watan Fabrairu, yarjejeniyar New START, wadda ke tsakanin Amurka da Rasha domin rage makaman nukiliya, ta ƙare ba tare da an sabunta ta ba, bayan fiye da shekaru 50 na wannan yarjejeniya tsakanin ƙasashen biyu.
John Erath ya ce muryoyin da ke goyon bayan yaɗuwar makaman nukiliya na ƙara ƙarfi, yana mai jaddada cewa akwai manyan dalilai uku da ke tura duniya zuwa wannan hanya

Asalin hoton, VCG via Getty Images
Dalilin farko shi ne ƙoƙarin China. Erath ya ce, "Sun ninka yawan makaman nukiliyansu kusan sau biyu cikin shekaru goma da suka wuce, kuma babu alamar za su tsaya."
Dalili na biyu shi ne yaƙin Rasha da Ukraniya. Ya ce, "Idan Rasha ta yi nasara a wannan yaƙin ta hanyar mamaya, wannan nasara za ta kasance ta yiwu ne saboda barazanar makaman nukiliya. Wannan ya ƙirƙiri sabon kayan amfani a siyasar ƙasa da ƙasa, wanda sauran ƙasashe za su yi sha'awar mallaka."
Dalili na uku kuwa, a cewarsa, shi ne rashin tabbas game da matakin da Amurka za ta ɗauka a nan gaba. Wannan rashin tabbas yana haifar da shakku ga abokan hulɗa da kuma abokan hamayya.
Ya ce, "Idan akwai rashin tabbas da rashin tsaro, koyaushe za a samu waɗanda za su ga makaman nukiliya a matsayin wata hanya ta ƙarin kariya."
Ukraine da Libya da Koriya ta Arewa
Ɗaya daga cikin hujjojin da ake amfani da su wajen kafa hujjar cewa ƙasashe su mallaki makaman nukiliya shi ne cewa, idan Iran ta riga ta mallaki makamin nukiliya, mai yiwuwa ba za a kai mata hari ba.
Kafin rikicin Iran, mutane da dama sun riga sun kawo misalin Ukraine, wadda a shekarun 1990 ta mika manyan makaman nukiliyarta, waɗanda suka kasance na uku mafi girma a duniya a wancan lokaci. A madadin haka, ta samu alƙawarin tabbacin tsaro daga Rasha da Amurka da Birtaniya.
Sai dai bayan kusan shekaru talatin, ba tare da makamin nukiliya a matsayin kariya ba, Rasha ta mamaye Ukraine ta hanyar kai mata hare-hare, wadda ita kanta ke da makaman nukiliya.
A gefe guda kuma, ana yawan kawo misalin Libya, wadda ta yi watsi da shirinta na nukiliya, amma daga baya aka kifar da gwamnatinta.
A sabanin haka, ana kuma duba misalin Koriya ta Arewa, wadda ta fara da kasancewa cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta fice a hukumance a shekarar 2003. A yau, tana daga cikin ƙasashe tara da ke da makaman nukiliya kuma ba ta fuskantar barazanar soji daga wata ƙasa.
Sai dai duk da waɗannan misalai da fargaba na yanzu, masana na ganin cewa ba lallai ba ne a samu yaɗuwar makaman na nukiliya.
Reid Pauly ya ce, "Makaman nukiliya suna da tasiri wajen hana hari, amma hanyar mallakar su tana cike da haɗari."
Ya ƙara da cewa, "Saboda haka, ƙasa na iya ganin cewa ya fi dacewa ta dogara da makaman da ba na nukiliya ba kawai domin tsaronta. "

Asalin hoton, AFP PHOTO / KCNA VIA KNS / STR / Coreia do Sul
Baya ga matsalolin fasaha, akwai kuma babban nauyin kuɗi da ke tattare da ƙera makaman nukiliya, ciki har da takunkumi da keɓancewa daga ƙasashen duniya.
John Erath ya ce, "Makaman nukiliya suna da tsada sosai, suna da wahalar ƙerawa da kulawa, kuma suna da haɗari ƙwarai."
Ya ƙara da cewa, "Babu wata ƙasa da ke kera su cikin sauƙi ko daga ra'ayi na lokaci ɗaya..
Ya ce kuma, "rige-rien mallakar makaman nukiliya ba ya da amfani ga kowa wanda hakan ya sa ya kamata a yi aiki wajen ganin an kawar da yaduwar makaman nukiliya."











