Wanda ya maƙale
Fursunonin yaƙi da suka maƙale a wuri mai nisa
Lud Beverley, tsohon mai samun horon aikin soji a Congo-Brazzaville, yana riƙe da hannunsa da aka nannaɗe da bandeji da wani ɓangare na yastunsa a gaban shi.
Yana kishingiɗe a kan gado a wani sansanin fursunonin yaƙi a yammacin Ukraine.
Mutumin mai shekara 28 ya shafe wata wata uku a sansanin a lokacin da BBC ta kai ziyara a watan Maris domin bin bahasin ƙaruwar yawan mayaƙa ƴan Afirka da suka maƙale sanadiyyar yaƙin Rasha da Ukraine.
Alƙaluman da Ukraine ta fitar sun nuna cewa ɗaya daga cikin duk fusrsunonin yaƙi takwas da Ukraine ta kama a bara ɗan Afirka ne. Ukraine ta yi imanin cewa ƴan Afirka sun kai kashi 10% na mayaƙan da Rasha ta ɗauko daga waje.
"Yayin gudanar da yaƙi na samu sandarewar ƙanƙara - a lokacin da aka kama ni, ba na da safar hannu," Beverly ya faɗa a cikin harshen Rashanci.
"Muna tafiya a ƙasa, akwai sanyi sosai."
"Sai na samu sandarewar fata saboda sanyi," in ji shi.
An tura shi Rasha ne shekara bakwai da suka gabata a matsayin soja mai samun horo domin yin karatu a kwalejin sojojin ruwa, daga baya ya yi aure har ya samu ƴa mace. Daga nan sai ya faɗa cikin matsalar kuɗi, sai ya riƙa sayar da ƙwaya, a ƙarshe aka kai shi gidan yari. Daga nan sai aka ba shi damar yin yaƙi a madadin zaman gidan yari.
"Domin wanke laifin da na yi, sai na yanke shawarar hidimta wa Rasha, saboda haka suka tura ni," in ji shi.
Ana tsara ziyara zuwa sansanin ne a ranar Alhamis ɗin ƙarshen kowane wata a matsayin matakin Ukraine na nuna wa duniya cewa tana martaba fursunonin yaƙi. Hukumomin sansanin ba za su iya faɗa mana ainahin yawan waɗanda ke wurin ba, sai dai sun ce ƴan Afirkan sun fito ne daga ƙasashe 15 daban-daban.
Beverly ya ce ba ya da ƙorafi kan yadda ake kula da shi: likitocin na da sassauci kuma zaman sansanin na da gundura kamar sansanin soja
Fursunonin yaƙi ƴan Afirka a sansanin tsare su da ke Ukraine ranar 26, Nuwamba, 2026. Getty Images
Amma yana nuna nadama a lokacin tattaunawar - yana kira ga iyalinsa da ƙasarsa, wadda ya ce babu ruwanta a yaƙin, su yafe masa. Abu mai muhimmanci kuma shi ne yana so a kawo ƙarshen yaƙin.
“Duka ɓangarorin biyu sun tafka asara - na je na gani, abin babu kyau.”
Lud Beverly
Fursunan yaƙi a Ukraine
Fursunan yaƙi a Ukraine
Dukkanin fursunonin yaƙi da suka amince su tattauna da mu sun bi ta hanya daban-daban ne wajen shiga yaƙin, yawancin su sun ce suna son suna son komawa Rasha domin karɓar kuɗin da suke bi - amma babu mai son komawa fagen fama.
Lokacin farko da muka isa, mun ci karo da ƙamshin miya mai daɗi - daga nan muka bi jerin fursunoni masu sanye da kayan sojojin ruwa da ke kan layin karɓar abincin rana.
Bayan haka sai aka tambaye su ko akwai wanda ke son yin magana da baƙin ƴan jarida. Wasu da suka fito daga Afirka sun yi da'ira a can daga ƙarshen ɗakin: su kadai a baya, suna raha, suna tsokanar juna, wasu ba su son haɗa ido da mutane.
Wani daga cikin ya matso gaba lokacin da ya fahimci cewa tawagar BBC na cikin ƴan jaridar. Ya bayyana kansa a matsayin Richard Kanu daga Freetown, babban birnin Saliyo.
Lokacin da yake bayani, ya ce wannan wata dama ce ta kwantar da hankalin iyalansa da tatbbatar musu cewa yana raye.
Mutumin mai shekara 43 ya shafe shekara ɗaya a sansanin, shekara biyu kuma a Ukranie.
Kamar Beverly, ya taɓa yin aikin soji - sai dai a lokacin da ya karɓi aiki a matsayin mai gadi bai taɓa tunanin cewa za a tura shi fagen yaƙi ba.
Ya yi aiki a matsayin sojan ƙasar Saliyo na shekara 17, inda ake biyan shi dala 100 a wata. Rikici tsakaninsa da abokan aikinsa ya sa ya bar aikin soja - sannan ƙoƙarin neman kuɗi ya sanya ya tafi Turai, inda ya yi amfani da takardar biza ta mai yawon shaƙatawa.
"Ƴata tana son ta zama likita. Ina da burin na biya mata don ta yi karatu a jami'a don ta cimma manufarta," in ji shi.
Duk ƙasashen da ya nemi biza ba su ba shi ba, sai Rasha kawai. Lokacin da ya isa Rasha a 2024 sai ya fara neman aiki, abin ya ba shi mamaki lokacin da ya samu aikin da za a biya shi dala 15,000, za a riƙa biyan shi dala 2,000 duk wata duk da ba ya jin harshen Rashanci. An tura shi birnin Rostov-on-Don da ke kudanci, kimanin kilomita 200 daga fagen daga a Ukraine.
"Lokacin da na isa birnin Rostov sai na tsinci kaina a sansanin soja," in ji shi - inda wani ya shaida masa cewa ya sanya hannun yin aikin sojan Rasha na shekara ɗaya. Ya kaɗu sosai - amma wani abu da ya rage masa damuwa shi ne an ce zai samu takardar zama ɗan Rasha.
"Bayan shekara ɗaya ina aiki, za a ba ni takardun zama dan Rasha da kuɗi. Za a ba ni damar kawo iyalina Rasha. Zan yi rayuwa kamar kowa a Rasha."
Sai dai ya ce fagen yaƙin akwai hatsari sosai saboda kayan yaƙi na zamani da kowane fanni ke da shi. Da yawa daga cikin fusrsunonin na cikin kaduwa sosai saboda abin da ya faru a can.
A wani ɗakin, wani fursunan yaƙi ɗan Kenya Evans Kibet, da farko ya ƙi yin magana, amma lokacin da na yi masa magana da harshen Swahili sai ya sassauto.
Sai Kibet ya damu lokacin da ya ji yadda iyalai da dama a can Kenya ke cikin damuwa saboda rahotannin yadda ake yaudarar mutane zuwa Rasha ta hanyar hanyoyin yaudara, ana kwaɗaita musu samun aiki mai tsoka, amma daga ƙarshe sai su ga sun zama sojojin yaƙi na Rasha.
Hukumomin Ukraine sun ruwaito cewa ƴan asalin Kenya ne suka fi yawa a cikin ƴan Afirka da ake ɗauka aikin sojan Rasha, daga nan sai ƴan Masar, da ƴan Kamaru, da ƴan Ghana da kuma ƴan Uganda.
"Fagen daga ba wurin wasa ba ne. Mutanen na mutuwa ta hagu, dama da tsakiya. Kuma babu wanda ya damu," in ji mutumin mai shekara 36.
Ya bayyana yadda harin jirgi maras matuƙi ke kashe mutane birjik.
Sojoji na ci gaba da dannawa, ba su iya komawa baya su taimaka ko da suna son yin hakan.
Ya buƙaci BBC ta tuntunɓi wani ɗan Kenya da ke wani ɗakin, ya ce ƙila shi wancan ɗin zai iya yin fira da ƴan jarida.
Tabbas Willy Macharia a shirye yake ya yi bayani kafin ya tafi karɓar abincin rana: "Akwai abinci sosai a nan. Zan iya cin abinci anjima."
Na iya gane cewa shi ne wani matashi ɗan shekara 23 wanda fuskarsa ta karaɗe shafukan sada zumunta yana gargaɗin matasan Kenya kada su shiga aikin.
Lokacin da na tambaye shi game da hakan, ya yi zargin cewa sojojin Ukraine ne suka tursasa shi ya yi bidiyoyin.
Daga baya na tambayi mai magana da yawun cibiyar tsara kula da fursunonin soji na Ukraine Petro Yatsenko, game da wannan zargi, amma ya musanta.
Macharia ya ce yana a filin daga tsawon wata uku - inda aka kwaɗaita masa shiga yaƙin tare da yi masa alƙawurran albashi mai tsoka da ci gaba da karatu. Amma ya ƙi sakin jiki ya yi bayani kan yadda aka ɗauke shi aikin: "Na kasance ina yi wa Rasha aiki ne, saboda haka kasancewa ta a Ukraine yanzu na nufin ina hannun maƙiya."
Domin magance zaman banza a sansanin, yana yin wata ƴarƙaramar sana'a domin samun ƴan kuɗaɗe ƙalilan wadanda zai iya kashewa nan take a wani ɗan ƙaramin kanti wajen sayen fanke ko sabulu ko sukari.
Kuma yana koyon harshen Ukraine a ɗakin karatu na sansanin, domin yana son ya fahimci abubuwan da ke gudana a inda yake. Matashin ya ƙosa ya samu ƴancin kansa kuma yana sa ran sunansa zai fito cikin jerin fursunonin da za a yi musaya domin a mayar da shi Rasha.
Amma Yatsenko, jami'i a cibiyar kula da fursunonin yaƙi na ganin musayar fursunonin zai yi wahala. Ya zuwa yanzu ya ce Ghana ce kadai ƙasar Afirka da ta mayar da hankali wajen kwashe ƴan ƙasarta da ke riƙe a matsayin fursunonin yaƙi - inda wakilanta suka ziyarci sansanin domin tattaunawa da hukumomi.
“A halin yanzu, babu ƙasashen Afirka cikin wannan musayar fursunoni. Suna son a mayar da su Rasha ne domin su karɓi kuɗaɗensu. Amma ba mu samu buƙatar Rasha na neman karɓar su ba.”
Petro Yatsenko
Mai magana da yawun babban ofishin tafiyar da ala'muran fursunonin yaƙi a Ukraine
Na kuma tattauna da ministan harkokin waje na Ukraine Andrii Sybiha, wanda ke kallon ƴan Afirkan da aka ɗauke su aikin sojin a matsayin "haramtaccen aikin farfaganda na Rasha".
"Wani lokaci ana gayyatr su zuwa Rasha ne domin yin karatu a ƙarshe sai su tsinci kansu a fagen daga," in ji shi.
Ministan ya ce ƴan ƙasashen waje ma za su iya yin yaƙi a ɓangaren Rasha - amma ya dage cewa tsarin Rasha na ɗaukan sojojin yana kan doka, don radin kai kuma na sa-kai. Bai da alƙaluma kan yawan ƴan ƙasar waje da ke cikin harkar.
Amma abin da muka fahimta shi ne ƴan Afirka fursunonin yaƙi da muka hadu da su na so ne su koma Rasha - kuma da wuya hakan ta faru har sai an kawo ƙarshen yaƙin.
Ga Beverly, ba don kudi kawai ba - ƴarsa tana can, sannan idan ya tafi Congo kai-tsaye, ya ce ba zai samu damar komawa Rasha ba.
Kanu ya dage kan cewa bai kamata ya ci gaba da rayuwa a Yammacin Afirka ba: "Na sanya hannu kan yarjejeniya da Rasha. Kuma ina so na koma Rasha. Rayuwa a Rasha ta fi min rayuwa a Saliyo."
Bayan barin Ukraine mun tafi birnin Freetown domin haduwa da ƴar Kanu mai shekara 19, Elsie.
Tana tsaye a ƙofar gidansu - tsohon gida wanda aka yi da tsofaffin kwanon rufi da ƙarafa a kan wani tudu da ke garin Tengneh - ta ce tana kewar mahaifinta sosai amma ta amince da ƙudirinsa na ci gaba da zama a Rasha.
“Dawowa Saliyo ba zai warware ko ɗaya daga cikin matsalolin da suka sa tun farko ya bar gida ba. Ina ganin rayuwa za ta fi masa kyau a Rasha - zai fi samu - zai fi samun dama gina wani abu, da damar sauya rayuwarmu.”
Elsie Kanu, 19
Wanda ya dawo
Ba kowa ne ke samun komawa gida ba. Amma Duncan Chege, wani ɗan Kenya, ya samu dama. Ya gudu daga asibitin da aka kwantar da shi bayan ya yi ƙaryar samun taɓin hankali a rundunar sojin Rasha.
Chege ya ce batun samun ƙarin kudin shiga abu ne da mutum zai yanke hukunci. Bayan ya kasa samun aiki a Dubai saboda matsalar samun biza, hukumar da ke nemar masa aiki ta ba shi shawarar ya gwada zuwa Rasha, inda ya samu biza cikin mako ɗaya.
Hoto daga of Duncan Chege
To finance the journey, his mother took out loans from neighbours and relatives, covering the agent’s fee and a one-way ticket.
Duncan Chege
Sai dai babu tabbas game da makomar wadannan fursunoni ƴan Afirka.
MA'AIKATA
Mai haɗawa: Sammy Awami, Rahoto daga kudancin Ukraine
Mai shiryawa da ɗaukar bidiyo: Hassan Lali
Tsarawa da zayyana: Millie Wachira
Tsara hoto: Mayowa Alabi
Zane:George Wafula
Hotuna:Ukraine (Getty Images), Sierra Leone (Sammy Awami) Saliyo da Kenya (Hassan Ali)
Tace rubutu:Lucy Fleming and Victor Oluoch
Mai shiryawa da gyara bidiyo:Kathy Harcombe
Editan shafi:Dorothy Otieno
Ƙarin tallafi: Shalom Olatunji, Brian Osweta, Njoroge Muigai, Boaz Ochieng da Damilola Ojetunde
Ranar wallafawa: 8 ga watan Yunin 2026

