Ko Bola Tinubu ya taɓa faɗuwa zaɓe?

Tinubu

Asalin hoton, Bola Tinubu/FACEBOOK

Bayanan hoto, Shugaba Bola Tinubu na Najeriya
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Bola Ahmed Tinubu, shugaba mai ci da ke riƙe da tutar jam'iyyarsa ta APC a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, wanda zai kasance babban zakaran gwaji ga burinsa na jagorantar Najeriya a wa'adi na biyu.

Nasarar da ya samu a zaɓen 2023 ta sanya shi a sahu ɗaya da gaggan shugabannin siyasa kamar Shehu Shagari da Olusegun Obasanjo da kuma marigayi Umaru Musa 'Yar'aduwa, waɗanda suka yi 'da gamo da kasawa'. A karon farko na takara suka ci zaɓen shugaban ƙasa.

Masharhanta da abokan hamayyarsa na bayyana ɗan siyasar a matsayin mutum mai kaifin lissafi, gwanin iya shirin zaune, mai hangen nesa da gogewar dabarun siyasa, kuma goshin jirgi da ke awon gaba da abokan karawa.

"Magoya bayansa da waɗansu al'umma suna gwada shi da cewa ya laƙanci ƙauli da ba'adin siyasa, tun fitowarsa fagen siyasa, inda cikin ƙanƙanin lokaci ya yi fice kuma ya yi kane-kane a siyasar Lagos, jiha mafi muhimmanci a Najeriya, da kuma sashen da ya fito na Kudu maso Yamma." A cewar Farfesa Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa.

Ga alama a yanzu yana fuskantar ƙalubalen siyasar da bai taɓa gani ba a rayuwarsa.

Jim kaɗan bayan hawansa mulki a 2023, Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur kuma ya sanya kuɗin ƙasar naira a kan tsarin da za ta tsaya da ƙafarta a kasuwar canji. Manufofin tattalin arziƙi ne masu zafi da suka haddasa tsananin hauhawar farashi da jefa talakawan ƙasar cikin ƙarin wahalhalu da matsin rayuwa.

'Yan adawan Najeriya ga alama suna cike da ƙwarin gwiwa tsohon gwamnan nan na jihar Lagos, ba zai ji da daɗi a hannunsu ba, idan an je rumfar kaɗa ƙuri'a a zaɓen baɗi.

Hakan dai ya sa ana tambayar ko Tinubu ya taɓa faɗuwa zaɓe?

Tarihin zaɓukan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya faro ne tun zamanin rusasshiyar jamhuriya ta uku a Najeriya, lokacin shirin miƙa mulki hannun farar hula na shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida.

Ya shiga siyasa ne a matsayin mamba cikin ƙungiyar siyasa ta PF (Peoples Front) ta marigayi Shehu 'Yar'aduwa, amma sai hukumomi suka ƙi yi wa ƙungiyar rijista, don haka shi da abokan tafiyarsa sai suka koma jam'iyyar SDP, ɗaya daga cikin jam'iyyu biyu da aka yi wa rijista a zamanin.

Zaɓukan da Tinubu ya yi takara

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Zaɓen shugaban ƙasa na 2027, shi ne zai kasance na biyar a rayuwar siyasar Bola Tinubu ta tsawon shekara 34.

Karon da ya fara tsayawa takara shi ne a zaɓen 1992, ƙarƙashin rusasshiyar jam'iyyar SDP, inda ya ci zaɓen ɗan majalisar dattijai mai wakiltar Lagos ta Yamma. Sai dai tafiyar ba ta yi nisa ba, inda sojoji suka hamɓaras da gwamnati a 1993 kuma suka rusa harkokin dimokraɗiyya.

A 1999, Bola Tinubu ya ci zaɓen gwamnan jihar Lagos a ƙarƙashin jam'iyyar AD bayan Najeriya ta koma tafarkin dimokraɗiyya.

Shi ne gwamna ɗaya tilo da ya koma kan kujerarsa a cikin gwamnonin jam'iyyarsa su shida dukkansu a yankin kudu maso yamma, lokacin da PDP ta ƙwace mafi rinjayen jihohin yankin a shekara ta 2003.

Tinubu bai sake tsayawa wata takara ba sai a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ya kayar da abokan karawa 17, da yawan ƙuri'a 8,794,726. Kuma bayan rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, ya zama shugaban Najeriya na biyar a Jamhuriya ta Huɗu.

Farfesa Kari ya ce idan an duba ta wani gefe, ana iya cewa Tinubu, gwarzon ɗan siyasa ne.

"In dai shi kansa ne ya yi takarar, ba a kayar da shi (a zaɓe) ba."

Tinubu

Asalin hoton, Nigeria Presidency/FACEBOOK

Bayanan hoto, Bola Tinubu na ɗaga tutar tsayawa takara da jam'iyyar APC ta ba shi

Zaɓukan da aka kayar da jam'iyyar Tinubu

Bola Tinubu "ya sha tallafa wa 'yan siyasa ko kuma waɗanda suke tafiya tare amma ana kayar da su a manyan zaɓuka da ƙanana," in ji Farfesa Kari.

  • Zaɓen 2007

Jam'iyyar Action Congress ta Bola Tinubu ta faɗi zaɓen shugaban ƙasa a 2007, lokacin da ta tsayar da Atiku Abubakar takara.

  • Zaɓen 2011

Jam'iyyar Tinubu ta ACN ta sake faɗuwa zaɓen shugaban ƙasa a hannun Goodluck Jonathan bayan ta rikiɗe ta canza suna daga Action Congress (AC).

Ɗan takararta Mallam Nuhu Ribaɗu ya zo na uku ne a zaɓen.

Farfesa Abubakar Kari ya ce hatta a sashensa na kudu maso yamma, an kayar da 'yan jam'iyyarsa ta ACN.

Haka zalika, "Obasanjo ya ma kusan kashe jam'iyyar (Tinubu) ta farko mai suna Alliance for Democracy a zaɓen 2003".

Salon siyasar Tinubu

Shafin intanet na fadar shugaban Najeriya ya bayyana Tinubu "a wani lokaci jigon da ke jagorantar adawa ne a Najeriya kuma jagoran ƙasa ne ga jam'iyyar APC. Yana cikin haziƙan da suka tsara fitowar manyan jam'iyyun siyasa biyu a Najeriya.

Ɗan fafutukar tabbatar da tsarin tarayya na ainihi, kaifin basirar siyasa na Shugaba Tinubu da labarin nasararsa shi ne mafi fice a cikin shekara ashirin a fagen siyasar Najeriya, in ji shafin.

"A zamanin yau, mutane da dama na mutunta shi a matsayin jagoran siyasa kuma mai tsara dabarun tattalin arziƙi, mai ɗaukar kasada kuma mai farautar baiwa da hikimomi."

Sai dai a cewar Farfesa Abubakar Kari "waɗansu kuma suna ga cewa ma ai irin siyasar tasa kwata-kwata, inkari yake ma ga dimokraɗiyya ta haƙiƙa".

Sannan kuma zai iya tattaunawa ya kuma samu abin da yake nema da kowa da kowa, in ji Kari. "Yana amfani da abin da yake da shi ya samu abin da yake so."