Ƴan Afirka bakwai da za su taka rawar gani a Gasar Kofin Duniya 2026, Gasar kofin duniya
A karon farko a tarihi kasa 10 ce daga Afirka za ta shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 da za a buga tsakanin tawaga 48, inda ake sa ran fitattun ƴan wasa da za su fatan ɗaga kofin.
Morocco ta kafa tarihi a Qatar a 2022, shekara hudu baya da ta zama ta farko daga Afirka da ta kai zagayen daf da karshe.
Cape Verde za ta fara halartar gasar a karon farko a tarihi, yayin da Jamhuriyar Congo za ta sake buga wasannin tun bayan 1974.
BBC ta zaƙulo muku ƴan wasa bakwai daga Afirka da za a saka ido a kansu a lokacin gasar da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli.

Asalin hoton, Getty Images


