'Na fitar da rai a soyayya, zan ƙarasa rayuta ni kaɗai'

Asalin hoton, Julie Osgood
Bayan rasuwar abokin zamanta sanadiyyar cutar korona, Julie Osgood ta yanke shawarar fantsama neman soyayya.
To amma halin da ta tsinci kanta a ciki ya sanya bazawarar mai shekara 60, mazauniyar garin Middleton da ke Birtaniya ta yanke shawarar haƙura da soyayya, domin dukkanin maza huɗu da ta yi soyayya da ita sun kasance mayaudara.
Julie, wadda ta kasance tare da abokin zamanta Tony Donohue tun suna da shekara 17 a duniya har zuwa lokacin da ya rasu a watan Nuwamban 2020, ta ce har ma ta yi hoɓɓasa ta hanyar shiga mahnajar neman masoyi ta shafukan intanet.
Ta ce ba ta fahimci asalin yaudarar ba, duk da cewa har damfararta aka yi kuɗaɗe.
"Ba zan sake shiga manhajar neman masoyi ba," in ji ta. "Ban ma san ina zan haɗu da mutane na gaskiya ba."
'Tsari iri ɗaya'
Jo;ie ta ce ta yi yunƙurin hana wasu faɗawa cikin irin wannan yaudara da aka yi mata kuma ta yi ƙoƙarin ganin shafukan neman masoya sun ɗauki mataki kan hakan.
Alƙaluman da BBC ta tattara a shekarar da ta gabata sun nuna cewa kuɗin da mutane suka tafka asara sanadiyyar soyayyar bogi, kamar yadda ƙungiyar Action Fraud ta ruwaito ya kai fam miliyan 92 a shekarar 2024, wanda hakan ya ƙaru a kan na shekarar da ta gabata, inda masu neman soyayya suka yi asarar kuɗi fam miliyan 82.
Matar ta ce a karo uku da shafukan neman masoya ta intanet suka damfare ta, dukkaninsu sun bi hanya iri ɗaya ne.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hotunan mazan da aka nuna wa BBC (wanda shafukan suka yi amfani da su), babu ko shakka an haɗa su ne ta hanyar fasar Ƙirƙirarriyar Basira (AI), musamman idan aka yi la'akari da rubutun da ke jikinsu.
"Dukkansu na farawa ne da labari iri ɗaya,," in ji ta. "Dukkansu na iƙirarin cewa su samari ne, sai ɗaya da ya ce shi bazawari ne, amma wasunsu sun ce suna da yara mata waɗanda ke rayuwa tare da tsoffin matansu."
Bayan wahalar da Jolie ta sha a neman soyayya ta shafukan intanet, sai ta yanke ƙauna da samun masoyi a irin waɗannan shafuka.
Sai dai a lokacin da za ta bar gidan da take zama, daidai lokacin da ɗanta na ƙarshe zai bar zama da ita, sai ta yanke shawarar ta sake gwada neman masoyi.
"Ni kaɗai ce, kuma ba na son na ci gaba da zama ni kaɗai har abada," in ji ta.
"Na zata hanya ɗaya kacal da zan iya samun wani abin kirki shi ne ta shafukan soyayyaya ta intanet, na ce bari na ƙara gwadawa ko da sau ɗaya ne. Daga nan sai na sake shiga wani shafin neman masoyin domin gwadawa ko da na wata ɗaya na domin ganin yadda za ta kasance."
'Na sake dawowa'
A wannan karo Julie ta yi rajista a wani shafin neman saurayi wanda ke amincewa da mutane waɗanda suka zarce shekara 50, wanda aka yi wa laƙabi da 'Ourtime'.
Lokaci kaɗan bayan shiga shafin sai ta haɗu da wani mutum mai suna Frank.
Mutum ne ƙaƙƙarfa mai kyauwun gashi, Frnak ya shaida wa Julie cewa shi mai sana'ar zayyanar tufafi ne da ke zaune a Birtaniya, sannan shi ɗan asalin ƙasar Faransa ne.
Haka nan kuma Frank ya ce shi bazawari ne wanda yake da yarinya ƙarama, amma sai ta gane abin kamar gaskiya ne bayan da suka kwashe ƴan makonni suna tattaunawa ta manhajar WhatsApp, kuma Julie ta nemi ko za su iya haduwa su tattauna ido da ido, domin ta gane ko da gaske yake yi.
Ta ce: "Na yi tunanin cewa 'wannan ce hanyar da za ka san mutum da gaske yake yi.' Kuma sai ya ce 'ya amince, hakan zai fi', amma kwatsam bayan kimanin kwana hudu sai ce min wai tafiya ta kama shi zuwa Faransa, daga nan na gane cewa lallai an sake 'kwarfe' ni."
A wannan karo Julie ta ci gaba da biye wa Frank domin ganin iyakar gudun ruwansa.
Amma nan take sai ta gano manufarsa.
Sai mutumin ya fara ƙirƙirar wani labari, wai yana fama da wata shari'a a kotu wadda ta shafi kadarar mahaifinsa - sannan ya ce an yanke hukunci a kansa har ma an garƙame masa asusun ajiyarsa na banki.
A cikin wani saƙo da Frank ya tura wa Julie, ya ce yana cikin "wani mawuyacin hali kuma a cikin mummunan tunani."
Julie ta ce ta kai rahoton hakan ga rundunar ƴansanda ta birnin Manchester, inda suka neme ta domin amsa wasu tambayoyi.
Da aka tambaye ta me ya sa take son ƴansanda su san labarinta, sai Julie ta ce: "A fusace nake domin sau hudu kenan ana yi min irin haka.
"Tabbas za su yi wa wata irin haka, wata ƙila wadda za su yi wa haka ba za ta ankare ba har a cuce ta maƙudan kuɗaɗe."
Julie ta bayyana labarinta a sirin Ourtime.
Julie ta koka wa shafin neman samari na 'Ourtime' game da lamarinta.
A wani saƙon Email da shafin 'Ourtime' ya tura mata, wanda ta tura wa BBC, shafin ya: "Muna matuƙar fifita kare mambobinmu kuma manufarmu ita ce samar da wuri da zai zama mai aminci ga duk mai amfani da shafinmu."
Shafin ya buƙaci a ba shi ƙarin bayani kan mutumin, kuma ya sha alwashin taimakawa wajen bincike idan aka nemi hakan.
BBC ta tuntuɓi shafin Ourtime domin neman ƙarin bayani.
Julie ta ce abubuwan da suka faru da ita ya jefa ta cikin mummunan tunani.
"Na fitar da rai a soyayya, zan ƙarasa rayuta ni kaɗai," in ji ta.










