KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Juma'a 9 ga watan Oktoban 2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Hoton Jirgi
  • Sheikh Daurawa
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Kwamishinan yansandan Kano
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Hoto
  • Yusuf Buhari
  • Mansura Isah
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. NDLEA ta gano bindigogi 40 da jabun takardun kuɗi a Kogi

    ..

    Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen Jihar Kogi ta ce ta kama sama da tan 10 na miyagun ƙwayoyi tare da ƙwato bindigogi 40 da harsasai 874 daga waɗanda ake zargi da fataucin miyagun ƙwayoyi tun daga ƙarshen shekarar 2025.

    Hukumar ta kuma ƙwato jabun takardun kuɗi na Naira, Dala da Fam, da kuma jabun magunguna, waɗanda aka miƙa wa hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike.

    Shugaban hukumar NDLEA a jihar, Mista Umar Yahuza, ne ya bayyana hakan a Lokoja yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan miƙa makaman da harsasan da aka ƙwato ga Cibiyar Kula da Ƙananan Makamai da Ƙananan Makamai (NCCSALW).

    Daily Trust ta ruwaito cewa makaman da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙanana guda biyar da wasu bindigogi 35. Ya ce an kama mutane da dama da ake zargi da hannu a fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka masu alaƙa da hakan a tsukin lokacin.

    Ya ƙara da cewa da yawa daga cikin waɗanda ake zargin suna fuskantar shari’a a Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja, inda maza suka kai sama da kashi 80 cikin 100 na masu fuskantar tuhumar.

    Yahuza ya ce miyagun ƙwayoyin da aka kama sun haɗa da tramadol, hodar Iblis, methamphetamine da tabar wiwi inda tabar wiwi ta fi yawa a cikin adadin da aka kama.

    Ya bayyana cewa an ƙwato wasu daga cikin makaman ne daga hannun mutanen da ake zargi da noman tabar wiwi, waɗanda suka mallaki makaman domin tunkarar jami’an tsaro yayin ayyukan sintiri da kama masu laifi.

    Shugaban NDLEA na jihar ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da masu fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran masu aikata laifuka. Ya kuma buƙaci jama’a su riƙa bai wa hukumomin tsaro bayanan da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka.

    Haka kuma ya gargadi mazauna jihar da su guji taimaka wa masu laifi, yana mai jaddada cewa fataucin miyagun ƙwayoyi da amfani da su ba bisa ƙa’ida ba na ƙara haddasa matsalolin tsaro, garkuwa da mutane da sauran laifuka a cikin al’umma

  2. An rufe wasu makarantun Malaysia sakamakon hayaƙi daga gobarar daji

    An rufe makarantu a wasu jihohin Malaysia a yau Juma'a, sakamakon hayaki daga gobarar daji a Indonesia, wanda ya sa gurbatar iska ta kai matakin da ke barazana ga lafiya.

    Yankunan da lamarin ya shafa sun haɗa da babban birnin ƙasar, Kuala Lumpur, da kuma cibiyar gudanarwar gwamnati ta Putrajaya.

    A Singapore ma, an samu gurbacewar iska mafi muni a kasar.

    Indonesia na fama da gobarar daji mafi muni a cikin sama da shekara goma.

  3. Za a nuna hukuncin kisa ta hanyar harbi kai tsaye a Amurka

    ..

    Sakataren harkokin Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya ce za a bai wa jama'a damar kallon yadda za a zartar da hukuncin kisa ta hanyar harbi kan Nidal Hasan, wanda aka samu da laifin kai harin bindiga a sansanin sojin Fort Hood a shekarar 2009.

    Wani jami'in ma'aikatar tsaron Amurka ya tabbatar da cewa za a watsa yadda za a zartar da hukuncin kai tsaye ta intanet.

    Hasan, wanda tsohon likitan masu fama da matsalar ƙwaƙwalwa ne a rundunar sojin Amurka, ya kashe sojoji 13 tare da raunata wasu 32 a harin da ya kai a Fort Hood da ke jihar Texas.

    Wakiliyar BBC ta ce an shirya zartar da hukuncin kisan ne a sansanin soja na Fort Hood da ke jihar Texas a ranar 3 ga watan Disamba, kuma zai zama karo na farko da sojin Amurka za su zartar da hukuncin kisa ta hanyar harbi tun bayan kawo karshen Yaƙin Duniya na Biyu

  4. Salam Alaikum!

    Masu bin mu a wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke kawo muku a kowace rana, barka da warhaka.

    Da fatan mun wayi gari lafiya. Kamar kodayaushe, a yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a duniya – musamman a Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Za ku iya garzayawa shafukanmu na sada zumunta – Fesbuk da Tuwita da kuma Instagram inda a nan ma muka wallafa ƙarin labarai da bidiyo.

    Sai ku kasance tare da mu.