Yaushe wata tawagar Afirka za ta lashe gasar cin kofin duniya?

A colourful composite graphic

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Moroko ta zama ƙasar Afrika ta farko da ta kai matakin wasan daf da na ƙarshe a gasar da aka buga a Qatar a 2022
    • Marubuci, Rob Stevens and Ian Williams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 8

"Idan akwai wani abu da nake son gani kafin Allah ya ɗauki raina, bai wuce in ga wata ƙasa daga Afirka ta lashe Kofin Duniya ba, saboda wannan gasa ce da dukkanmu ke matuƙar ƙauna a Afirka."

Sunday Oliseh yana cikin tawagar Afirka ta farko da ta lashe lambar zinare ta ƙwallon kafa a gasar Olympics, inda ya taimakawa Najeriya kafa tarihi a gasar Atlanta a 1996, amma har yanzu ɗan wasan mai shekaru 51 yana jiran ganin an yi irirn wannan nasarar a gasar cin kofin duniya.

An gudanar da gasa 22 tun shekarar 1930 aka fara shirya gasar Kofin Duniya, kuma a tsawon wannan lokaci tawagogi 49 daga ƙasashe 13 ne suka wakilci nahiyar, amma duk da haka ƙasar Afrika ɗaya ce kacal ta taɓa kai wa matakin wasan kusa da na ƙarshe.

Wannan lamari mai cike da tarihi ya faru ne shekara huɗu da suka gabata a Qatar 2022, lokacin da Maroko ta ɗaukaka matsayin nahiyar, wadda ita ce ta biyu mafi girma a duniya kuma ta biyu mafi yawan al'umma.

Hakan na nufin hasashen da tsohon ɗan wasan Brazil da ya taɓa lashe gasar cin kofin duniya sau uku, Pele, ya yi a shekarun 1970 cewa wata ƙasa ta Afirka za ta lashe kofin nan da shekara ta 2000, har yanzu bai tabbata ba.

Babbar tambayar ita ce: Har zuwa yaushe za mu ci gaba da jira?

Tsarin ƙasashen da suka taka rawar gani

Nahiyar Afirka ta samu tawaga uku da suka kai matakin daf da na kusa da na ƙarshe – Kamaru a 1990, Senegal a 2002 da Ghana a 2010 – kafin Moroko ta ɓai wa Belgium da Spain da Portugal mamaki a lokacin da kai zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a Qatar.

Abu ɗaya da ke tabbatar da nasarar ƙasar ta yankin Arewacin Afirka shi ne zuba jari na dogon zango wanda Sarki Mohammed VI na ƙasar ya goyi bayansa.

An kashe dalar Amurka miliyan 65 wurin buɗe wata makaranta da kuma cibiyar horas da ƴan wasa da duka suke ɗauke da sunansa a shekarar 2009 da 2019 kuma sun taimaka wa tawagar Atlas Lions ta kafa kanta a matsayin ta ɗaya a nahiyar Afirka.

"Maroko ta ƙirƙiro da tsarin yadda za a iya cimma nasara, wanda ya ƙunshi ɗaukar shekaru ana zuba jari a harkar ƙwallon ƙafa," in ji tsohon kyaftin ɗin Najeriya William Troost-Ekong, a hirarsa da BBC Sport Africa.

"Ya na farawa da tsari, tare da shiri na musamman. Zuba jari yana da matuƙar muhimmanci.

"Dole ne ya zama wani abu da ya samo asali daga tallafin da hukumomin ƙwallom ƙafa ke samu daga gwamnati.

"Ba kudi kaɗai Moroko ta kashe ba, har ma da lokaci da kuma yunƙurin gaske, tare da fahimtar hanyoyin da za ta bi domin samun ci gaba. Kayayyakin da ta ke da su, da daidaito da ta samu a cikin tawagogin matasanta, ina tsammanin wannan shi ne kaɗai tsarin da za a iya koyi da shi."

Ƴan wasan Kamaru sanye da koren riguna da jajayen wando da safa masu launin rawaya, tare da mai tsaron gida sanye da baƙaƙen kaya, su na murnar cin ƙwallo a gasar cin kofin duniya ta 1990.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kamaru ta zama ƙasa ta farko a Afirka da ta kai wasan daf da na kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya a shekarar 1990, kuma Indomitable Lions ta kafa tarihin buga gasa takwas- amma ta kasa samun tikitin shiga gasar ta bana.

A nata ɓangaren, hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (Caf), tana ƙoƙarin inganta asusun hukumomin ƙwallon ƙafa na ƙasashe, ta hanyar ƙara yawan kuɗaɗen da za a samu a gasar cin kofin nahiyar Afirka da kuma manyan gasannin ƙungiyoyin ƙwallon kafa na nahiyar, da kuma zuba jari a gasar zakarun makarantu.

Shugaban Caf Patrice Motsepe ya yi hasashen cewa, wata ƙasa ta Afirka za ta zama zakara a duniya.

"Abin da muke ƙoƙarin ganin mun cimma ke nan, shi ne abin da muke zuba jari a ciki kuma muna da yaƙinin hakan zai faru."

Claude Le Roy, wanda ya jagoranci Kamaru a gasar cin kofin duniya a shekarar 1998, kuma ya horar da wasu ƙasashe biyar na Afirka, ya ce zuba jari a kan matasa zai haifar da gagarumar riba bayan wani lokaci

"Idan ku na son samun manyan tawagogin ƙasashen Afirka masu hazaƙa, kuna buƙatar yin aiki tare da tawagogin matasa," in ji mai horaswan mai shekara 78.

"Wannan shine tushen komai."

Kokawar samun wakilci

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A baya dai Afirka ta sha fama da rashin samun wakilci a gasr cin kofin duniya , inda gwamnatin mulkin mallaka ya takaita damammakin da ƙasashen za su iya samu, kafin wasu jerin ƙasashe su ayyana ƴancin kai a shekarun 1950 da 60s.

Masar, a shekara ta 1934, ita ce ta ƙasa ɗaya tilo da ta wakilci nahiyar Afirka a gasannin takwas na farko - kuma Afirka ta ƙaurace wa ghasar shekarar 1966 bayan FIFA ta sanar da cewa ba za ta gudanar da wasannin samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya kait-tsaye da za a yi a Ingila a waccan shekarar ba.

Nahiyar ta tura tawaga ɗaya zuwa gasar a 1970, da 1974 da 1978 - saɓanin aƙalla tara daga Turai da uku daga Kudancin Amurka.

An samu gurbi biyu daga 1982, aka samu uku a 1994 sai kuma biyar daga 1998 zuwa lokacin da gasar ta faɗaɗa zuwa tagwaga 32.

Shida sun fafata ne a shekarar 2010 lokacin da Afrika ta Kudu ta karɓi baƙuncin gasar, amma gasar ta bana mai tawaga 48 a Canada da Mexico da kuma Amurka za ta kasance mafi girma inda nahiyar ke da tawaga tara da suka samu gurbi kai tsaye da kuma DR Congo wadda ta samu nasarar zuwa gasar ta hanyar lashe wasan cike gurbi.

Kyaftin din Afirka ta Kudu, Ronwen Williams, wanda zai jagoranci tawagarsa a wasan farko na gasar da za a yi a Mexico City, ya yi imanin cewa gasar cin kofin duniya ta bana za ta kasance "lokaci mai ban mamaki" ga wasan Afirka.

Ya shaida wa BBC cewa "Mun yi ta samun ci gaba - a matakin lig-lig, da matakin Caf, Gasar Zakarun Afrika (CAF Champions League), da kuma Afcon."

"Komai ya inganta sosai. Ƙasashe da yawa sun fita don yin takara a matsayi mafi girma, abin mamaki ne."

Bayan da aka samu nasara sau 37 a wasanni 162 na gasar cin kofin duniya da aka buga a baya, Williams da Troost-Ekong su na da yaƙinin cewa ƙarin yawan wakilai, da kuma sauyin tsarin inda za a samu kashi biyu cikin uku na kungiyoyin da za su tsallaka daga matakin rukuni, zai zama wani babban alfanu ga inganta tarihin Afirka a gasar.

Zauƙulowa da kuma iya riƙe masu hazaƙa

Yayin da a baya ana samun zaratan ƴan wasa da aka haifa a Afirka ko waɗanda ke da asali a Afirka su zaɓi wakiltar ƙasashen Turai, nahiyar yanzu tana cin gajiyar yawan ƴan wasan da ta ke da su a ƙasashen waje.

Wani fa'ida shi ne cewa wasu daga cikin ƴan wasan za su sami horo a makarantun manyan ƙungiyoyin Turai.

Tare da jarin da ta zuba, Maroko ta jawo hankalin ƴan wasa da dama da aka haifa a ƙasashen waje, ciki har da mai tsaron gida Yassine Bounou (Kanada) da Achraf Hakimi da Brahim Diaz (Sifaniya), waɗanda suka sanya rigar Atlas Lions.

A halin da ake ciki, ƙasashen Cape Verde da DR Congo, waɗanda suka dawo gasar a karon farko tun 1974, sun samu tikitin shiga gasar bayan sun gayyato ƴan wasa da dama daga ƙasashen waje.

Daga cikin ƴan wasa 26 na ƙasar DR Congo, an haifi 11 a Faransa, biyar a Belgium, biyu a Switzerland sai kuma biyu a Ingila. Masu tsaron baya Aaron Wan-Bissaka da Axel Tuanzebe duk sun sauya sheƙa bayan sun wakilci Ingila a matakin matasa.

"An bunƙasa gayyato ƴan wasa," tsohon kyaftin Gabriel Zakuani ya shaida wa shirin 'More Than The Score'.

Ɗan wasan mai shekara 39 a yanzu yana aiki a matsayin mai ba da shawara kan fasaha wajen gano ƴan wasan da suka cancanci shiga tawagar ƙasar kafin ya yi yunƙurin shawo kansu su wakilci Leopards.

"Dole ne ku sa ƴan wasa su yarda da hangen nesan ku. Mai yiwuwa ba za su iya buga wa Ingila, ko Belgium ko Faransa ba, amma duki da haka za su iya zuwa gasar cin kofin duniya," in ji shi.

"Babban misali shi ne Axel Tuanzebe, ya taso ne a tsarin Ingila sannan kuma ya zura ƙwallon da ya kai mu gasar cin kofin duniya.

"Wannan shi ne ƙarshen labari mai faranta zuciya, kuma wataƙila zan yi amfani da wannan labarin wurin shawo kan ɗan wasa na gaba."

Bunƙasa samun ƙwarin gwiwa

Ƴan wasan Moroko sun yi murna a filin wasa bayan da suka doke Portugal a gasar cin kofin duniya na 2022 a Qatar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Moroko ta doke Belgium da Spain da Portugal kan hanyarta ta kai wa matakin wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya ta 2022, inda suka ta yi rashin nasara a hannun Faransa.

A halin da ake ciki kuma, nasara da Maroko ta yi a Qatar ta zaburar da ƴan wasan ƙwallon ƙafa daga sassan nahiyar cewa, ana iya cimma burin kai wa aƙalla zagayen kusa da na ƙarshe.

"Abin da Maroko ta yi, shi ne mataki na farko a gare mu ƴan Afirka, inda mu ka yi imanin cewa za mu iya yin nisa," in ji golan Bafana Bafana Williams.

"Yana farawa da wannan kyakkyawan zato, sannan kuna buƙatar fita ku yi aiki tuƙuru."

Samun tunani mai kyau shima yana da matuƙar muhimmanci, a cewar ɗan wasan gaban Senegal, Iliman Ndiaye.

"Ba zan ma damu da tattara akwati na da tafiya gasar cin kofin duniya ba idan ba don lashe gasar ba," kamar yadda ya shaida wa shirin Newsday na BBC.

"Ba na buga waɗannan gasa don zama dan yawon buɗe ido kawai.

"Abin da Moroko ta yi a gasar cin kofin duniya na ƙarshe ya kamata ya bai wa dukkan tawagogin Afirka ƙwarin gwiwa."

Abin da aka rasa

Golan Senegal Tony Sylva, wanda ake iya gani sanye da rigar ƙasar Senegal mai dogon hannu da launin shuɗin, ya rufe idonsa tare da ɗora hannunsa biyu a kan sa da alamun takaici a fuskarsa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Senegal were knocked out of the 2002 World Cup on golden goal when Turkey scored early in extra time in their quarter-final tie An fitar da Senegal daga gasar cin kofin duniya a shekara ta 2002 da 'golden goal' lokacin da Turkiyya ta zura ƙwallo a farkon ƙarin lokaci a wasan daf da na kusa da na ƙarshe.

Don duk da sanya hannun jari, da haɓaka wakilci da haɓaka ƙwarin gwiwa, duk wata ƙasar da ke fafutukar lashe gasr kofin duniya sai ta haa da samun sa'a a kan hanya.

An doke Senegal a shekarar 2022 bisa dokar 'golden goal' wanda yanzu aka yi watsi da ita , yayin da sauran ƙirin Afirka ta samu tawagarta ta farko da za ta kai matakin kusa da na ƙarshe a shekarar 2010 da ɗan wasan Ghana Asamoah Gyan bai ɓarar da bugun fanareti ba a ƙarshen ƙarin lokaci a wasan daf da na kusa da na ƙarshe, inda aka fitar da ƙasar ta yankin Afirka ta Yamma da bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Yayin da a yanzu aka samu ƙarin zagayen kifa-ɗaya-ƙwala, guje wa rauni da dakatarwa zai zama mai matuƙar mahimmanci.

"An samu ci gaba sosai," tsohon aɗn wasan Black Stars Michael Essien ya shaidawa BBC Sport Africa.

"Abin da aka rasa shi ne sa'a, kawai mu ci gaba da imani da fatan wata rana hakan zai faru."

Moroko da Senegal, da ke matsayi na takwas da na 14 a duniya bi da bi, suna bai wa Afirka ƙwarin gwiwar cewar za su iya tayar da hankulan manyan ƙasashen Turai da Kudancin Amurka, amma dukkansu suna da cikin rukunnai masu ciken da sarƙaƙiya.

Idan tawagar nahiyar ta sake gazawa, to Moroko za ta samu damar kasancewa a gida a shekara ta 2030, lokacin da Masarautar za ta karɓi baƙuncin gasar tare da haɗin gwiwar Portugal da Spain kuma tana fatan shirya wasan karshe.

Babu shakka an tage tazarar da ke tsakanin manyan ƙasashe a fagen ƙwallon ƙafa da kuma ƙanana, kuma lokacin da ƴan wasan kwallon kafa daga nahiyar za su ɗaga kofin duniya - yana ƙara kusantowa.