Abin da muka sani kan kashe masu kallon ƙwallo a Adamawa

    • Marubuci, Harry Sekulich
  • Lokacin karatu: Minti 3

Wasu mahara sun kashe aƙalla mutum 29 a harin da suka kai kan wani ƙauye da ke jihar Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Ƙungiyar 'Islamic State' (IS) ta bayyana cewa ita ce ta kai harin, ba tare da ta bayar da dalilin da ya sa ta kai shi ba.

Mahukunta da mazauna yankin sun ce maharan sun yi wa filin da ake wasan ƙwallon ƙafa ƙawanya inda mutane suka yi dandazo, daga nan sai suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, kafin daga baya suka ƙona gidaje da wuraren ibada da kuma babura.

Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya wallafa hotunan lokacin da ya kai zaiyara a wurin da lamarin ya faru, inda ya bayyana harin a matsayin "ƙalubale ga bil'adama".

Ofishin mai bai wa gwamnan jihar shawara kan yada labarai ya ce harin, wanda aka kai a ƙauyen Guyaku da ke ƙaramar hukumar Gombi, ya ɗauki tsawon sa'o'i.

Lokacin da yake duba wurin da lamarin ya faru, mai magana da yawun gwamnan ya rubuta a shafinsa na facebook cewa "ana zaman ɗarɗar a yankin, inda mutane ke cike da tsoro da alhini."

Iyalai da dama "sun bar gidajensu saboda tsoron kada a kai musu wani sabon harin", kamar yadda mai magana da yawun gwamnan ya bayyana.

Gwamna Ahmadu Fintiri ya wallafa a shafinsa na X cewa: "muna tsananta ayyukan tabbatar da tsaro domin dawo da tsaro ba tare da ɓata lokaci ba da kuma tabbatar da kwanciyar hankalin mazauna yankin."

Yankin, wanda ke kusa da iyakar Najeriya da Kamaru ya sha fama da rikice-rikice, inda mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar IS ke yawan kai hare-hare a shekarun baya-bayan nan.

A farkon wannan shekarar, an yanke wa kusan mutum 400 hukunci bayan shari'ar da aka yi wa mayaƙa da aka kama da laifin alaƙa da ƙungiyar Boko Haram da kuma ISWAP.

A shekarar 2009 ne ƙungiyar Boko Haram ta ƙaddamar da hare-haren tayar da ƙayar baya a arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya haifar da salwantar dubun-dubatar rayuka da tarwatsa mutane sama da miliyan biyu daga muhallansu.

Rikicin ya yaɗu zuwa ƙasashe masu maƙwaftaka kamar Nijar da Chadi da kuma Kamaru.

Gwamnatin Najeriya na fuskantar matsi wajen ganin ta magance matsalar tsaro a ƙasar, wadda ita ce mafi yawan al'umma a Afirka.

Haka nan a yanzu haka ƙasar na fuskantar sanya idon ƙasashen duniya daban-daban gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara mai zuwa.

A shakarar da ta gabata, Amurka ta ƙaddamar da hari a cikin Najeriya kan wasu mayaƙa a arewacin ƙasar da ake alƙantawa da ƙungiyar IS arewa maso yammacin Najeriya.