Wane ne mutumin da ya kai hari a taron da Donald Trump ke halarta?

Lokacin karatu: Minti 3

An bayyana sunan mutumin da ake zargi da yin harbi da bindiga a lokacin taron cin abinci na ƴan jarida da shugaban Amurka a fadar White, sunan shi Cole Tomas Allen, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na Amurka suka ruwaito.

An kama mutumin da ake zargi, inda ake kula da shi a asibiti bayan harin. A yau Litinin ne ake sa ran gurfanar da shi a gaban kotu.

Har yanzu babu masaniya kan manufarsa game da harin.

Rahotanni sun ce mutumin ɗan asalin garin Torrance ne a jihar California - garin da ke a kudu maso yammacin birnin Los Angeles.

A wani taron manema labarai, kalaman shugaban Amurka Donald Trump na nuna cewa mutumin ya yi gaban kansa ne wajen kai harin: 'Suna tunanin cewa shi kadai ya kitsa abinsa, ni ma na yarda da hakan'.

Ƴansanda sun ce mutumin ya sauka ne a otal ɗin Washington Hilton, inda ake gudanar da taron cin abincin, kuma yana ɗauke da makamai daban-daban, ciki har da wuƙaƙe.

Kafar yaɗa labarai ta CBS mai hadin gwiwa da BBC a Amurka, ta ruwaito cewa Allen ya yi koyarwa a garin Torrance bayan kammala karatu a daga sananniyar makarantar nan ta California Institute of Technology.

Jaridar Independent ta ruwaito cewa, ƴansanda na da yaƙinin cewa Allen ba mutum ne mai tarihin aikata laifuka ba shi ya sa ma babu idon jami'an tsaron Washington a kansa.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa wasu bayanai da aka wallafa a facebook sun nuna cewa Cole ya taɓa lashe kyautar ''malami mafi ƙwazo'' a watan Disamban 2024.

Wani shafi a dandalin LinkedIn ɗauke da sunan mutumin da ake zargin ya bayyana shi a matsayin ''bakanike mai digiri a harkar kwamfuta, mai gogewa a ɓangaren tsara wasannin gyam na kwamfuta, kuma mutumin da aka haifa da ƙwarewa ta koyarwa".

Shafin na LinkedIn ya nuna cewa Allen ya samu takardar shaidar digiri a gyaran na'ura daga kwalejin California Institute of Technology a shekarar 2017.

Sannan a shekarar 2025 ya samu digiri na biyu a ilimin kwamfuta a jami'ar jihar California.

Shafin ya nuna cewa Cole na aikin koyarwa na wucin-gadi sannan kuma yana sana'ar tsara wasannin gyam na kwamfuta.

Daga cikin laifukan da za a tuhumi Allen da su akwai amfani da bindiga domin tayar da rikici.

Taron cin abincin daren na ranar Asabar shi ne irin sa na farko da shugaba Trump ya halarta a matsayin shugaban ƙasa.

Sau biyu Trump yana tsira daga yunƙurin kashe shi a shekarar 2024, wato bayan ya bar mulkinsa na farko a 2021, sai kuma a lokacin yaƙin neman zaɓensa don komawa muƙamin shugaban ƙasa.

Hari mafi haɗari da aka kai masa shi ne wanda aka kai a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe a wani buɗaɗɗen dandali da ke garin Buttler na jihar Pennsylvania, a watan Yulin 2024.

Harbin, wanda wani matashi ɗan shekara 20 ya kai ya raunata Trump a kunne, amma jami'an tsaro sun samu nasarar halaka mutumin.

Inda aka kai harin na baya-bayan nan, wato Washington Hilton, shi ne wurin da aka taɓa yunƙurin kashe tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan a shekarar 1981.

Trump ya shaida wa manema labarai cewa Allen, wanda mazaunin jihar California ne, a yanzu jami'an tsaron na bincike a gidansa.

Hukumomi sun bayyana cewa mutumin yana ɗauke ne da bindiga da wuƙaƙe da dama.