Yadda al'ada ke tasiri a rayuwar matan Afrika

Lokacin karatu: Minti 6

'Duk mutumin da ya yi watsi da al'adarsa ya zama bawa'

Wataƙila kun taɓa jin waɗannan kalaman a wani wuri ko cikin dangi, in dai kuna zaune a cikin al'ummarku.

Ana yawan amfani da wannan kalmar domin nuna wa mutane su ɗauki al'adarsu da muhimmanci cike da alfahari game da tsatson su.

To amma a 2026, babbar tambayar ita ce: shin irin waɗannan al'adun suna kare mutunci da ƙimar mata kuwa?

A yawancin wurare, ba iya karkara kawai ba, har yanzu akwai wasu al'adu da suke sanya shamaki ga mata musamman abin da ya shafi jikinsu, kuma hakan yana take musu haƙƙin walwala da zaɓi, wani lokacin ma ya kan bar musu tabo a jiki.

A wannan rahoto, mun yi nazari kan yadda wasu abubuwa da ake ganin suna da muhimmanci a al'ada ke take haƙƙin mata a matsayinsu na ƴan'adam.

1. Kaciyar mata

Akwai wasu munanan al'adu guda biyar masu cutar da mata. Na farkonsu shi ne kaciyar mata.

Kaciyar mace wani abu ne da ake yi domin cire wani bangare daga al'aurar mace ba tare da bin tsarin likitoci ba.

Ana yawan yin kaciyar ne ga ƴan mata ƙanana da ba su wuce shekara 15. Wannan kaciyar, take haƙƙin ƴaƴa mata ne.

Ana kashe kimanin dala biliyan 1.4 a duk shekara domin magance matsalolin da kaciyar mata ke haifarwa, kuma kuɗin zai iya haura hakan idan ba a ɗauki matakin dakatar da hakan ba.

Sama da mata da ƙananan yara miliyan 230 ne ke fuskantar wannan cin zarafin a faɗin duniya. Lamarin ya fi ƙamari a ƙasashe irinsu Kenya, Sudan, Masar da Ehiopia.

Ana ganin yin kaciya ga ƴa mace, wani abu ne da zai kare mutuncin ta da kare mata budurci kafin aure. Wannan ya haɗa da sanya mata takunkumai kan jinsin ta da kuma nuna muhimmancin budurcin.

Sai dai, idan aka yi wa mace kaciya, hakan na matuƙar illa ga lafiyarsu. Za ta iya mutuwa, ko kuma samun matsala a lokacin haihuwa da jin zafi a lokacin saduwa ko kuma tsangwama daga al'umma.

Yin kaciyar mata babban laifi ne a Kenya. An tanadi hukuncin ɗaurin shekaru aƙalla uku ko kuma babbar tara ga wanda ya aikata hakan.

Duk da alƙaluma sun nuna cewa ana samun raguwar yin kaciyar a ƴan shekarun nan, ammahar yanzu akwai inda ake yi.

Sai dai wani babban abin damuwar shi ne yadda wasu ma'aikatan lafiya ke yin kaciyar mata a ɓoye a wasu asibitoci domin kaucewa taka doka.

Suna yin hakan ne domin nuna cewa sun bi hanyar likitoci domin a yi wa mace kaciyar, duk da yake take haƙƙi ne da ke yin tasiri na dogon lokaci ga ƴa mace.

2. Yanke nonon mace

Yanke mama ko "rage nono", wani abu ne da ake yi a al'ada, inda ake yanke nonon yarinya ƙarama ko a ƙona shi da wani ƙarfe mai zafi da aka saka a wuta, domin ɓoye girman mace da ke bayyana alamun fara balagarta, in ji Hukumar Lafiya ta Afrika (AHO).

Hukumar ta yi bayanin cewa, wuraren da ake aikata wannan al'adar na ganin yin hakan na rage jan hankalin maza kan mace a lokacin da ta fara balaga, kuma yana rage cin zarafinsu, ko fyaɗe ko yi musu auren dole ko a yi garkuwa da su da kuma tabbatar da sun ci gaba da zuwa makaranta.

Sai dai hukumomin lafiya da masu kare haƙƙin ɗan'adam sun ce wannan al'adar na jefa yara mata cikin damuwa da kuma illa ga rayuwarsu, lamarin da ke ƙara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana yanke maman mata sama da miliyan 3.8 a nahiyar Afrika, kuma yankin na daga cikin waɗanda ba ba da rahotannin cin zarafin mata.

Kashi 25 zuwa 50 na yara mata a Kamaru da wasu sassan Najeriya na fuskantar wannan cin zarafin, kamar yadda wasu bayanai da wata cibiyar bincike ta wallafa.

Yawancin mata na fuskantar ƙalubalen a wajen shayarwa bayan haihuwa da suka haɗa da matsanancin ciwo, jin zafi da kamuwa da cututtuka da tabon da ba zai goge ba.

3. Tursasa wa mata yin jima'i

A wasu sassan Ghana, Togo da Benin, har yanzu ana yin wata al'ada da ake kira da trokosi.

Ana ba da sadakar mace ga wuraren bauta a matsayin hukunci saboda wani laifi da ahalinta suka aikata.

A kan tilasta musu yin aikin ƙarfi ko kuma yin jima'i da cin zarafinsu. Wannan al'ada na tauye wa mata haƙƙinsu da damarmaki na ci gaba da karatu da kuma jefa su cikin damuwa.

Duk da yake wasu ƙasashe sun haramta wannan al'ada, amma ba a cika tabbatar da ita ba.

4. Gwajin budurci

Gwajin budurci ana yin shi ne domin dubawa da tabbatar da cewa mace tana nan da budurcinta ko kuma ba ta taɓa saduwa da namiji ba. Babu wasu bayanan kimiyyya da suke tabbatar da sahihancin wannan gwajin.

Ana sanya yatsu biyu a al'aurar mace domin tabbatar da cewa budurcin ta na nan, inda wasu suka yi amanna cewa da zarar an duba ba a ji wani abu da ya yi turke ba, to tabbas mace ta taɓa saduwa da namiji. Sai dai akwai matan da ake haifarsu babu wannan fatar da take rufe al'aurar ko kuma ta yage a lokacin da mace ta yi wasu wasanni.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yin hakan cin fuska ne ƴaƴa mata, kuma hakan ba shi da amfani a kimiyyance.

Yawancin mata na fuskantar cin zarafi saboda wannan abin.

Wannan sun haɗa da shiga damuwa, ko zaƙuwa inda wasu kan shiga wani hali na ƙunci na tsawon rayuwarsu bayan an musu gwajin budurci.

"Wasu yara matan su kan yi yunƙurin kashe kai idan aka musu gwajin, kuma hakan ba daidai ba ne saboda waɗannan al'ummomin suna ganin cewa sai mace ta yi aure ya kamata ta sadu da namiji, kuma hakan na tauye mata haƙƙinta na ƴar'adam," in ji Dr. Simelela a hirarta da jaridar the Nation a Kenya.

Har yanzu ana yin wannan al'adar a wasu sassan Kenya, musamman Mombasa, da Afrika ta Kudu da Masar.

5. Cin zarafin zawarawa

A wasu wuraren a ƙasashe irinsu Kenya, Najeriya, Uganda, Zambia, Ghana da Tanzania, ana tilastawa mace bin wasu ƙa'idoji bayan mutuwar mijinta.

Wasu matan na fuskantar ƙalubale bayan mutuwar mijinsu, tare da tunanin yadda za su ci gaba da rayuwa ba tare da mijin ba. Amma kuma ana ƙara musu wannan raɗaɗin da wasu sharuɗɗa na al'adu da mai takaba za ta yi domin nuna girmamawa ga mijinta.

A yankin Ukerewe na ƙasar Tanzania, ana ganin takaba a matsayin wata al'ada da idan mace ba ta yi ba, ko kuma ta ƙi bin wasu ƙa'idojin, kurwar mijinta za ta ci gaba da bin wannan ahalin da kuma shafa musu rashin nasara ko ƙashe su.

Domin hana aukuwar hakan, al'adar ta buƙaci mai takabar ta yi jima'i da wani bazawari daga dangin mijinta, sannan kuma za ta kwana da wani mutum daga wani gari daban, wanda ba shi da alaƙa da ita ko danginta.

Ba a Tanzania kaɗai ba, har Kenya ma bazawara tana fuskantar matsi kan wasu al'adun.

Alal misali, a Nyamira County da ke Kenya, an yi wata mata dukan tsiya da cin zarafinta, saboda ba ta zuba ƙasa a ƙabarin mijinta da ya rasu ba domin girmama shi, kamar yadda al'adar ta sharɗanta.

Hakazalika a ƙasar Kenya, al'ummar Luo na tilasta matar da mijinta ya mutu ta aske gashinta sannan kuma ta auri dan'uwan mijinta.

Ba Kenya kaɗai ake irin wannan ba. India ta haramta duk wasu, al'adu da ke cin zarafin matan da mazajensu suka mutu, kuma ta samar da tsarin fansho a jihohi da taimakon samar da matsuguni ga matan.

Rwanda ta sake gyara dokokinta na gado da na filaye domin kare haƙƙin zawarawa kan dukiya da gado bayan kisan kare dangin da ya faru. Togo ta kafa dokoki da ke haramta al'adun tsarkakewa da ake yi tare da samar da dokar kariya ga zawarawa.

Waɗannan ƙasashen sun gane cewa akwai cutarwa a irin waɗannan al'adu da suka ken matan da mazajensu suka mutu, kuma bai kamata a ƙyale su haka, dole a ɗauki mataki don ƴancin ɗan'adam.

The big picture

Ɗaya daga cikin kowace mace uku a duniya, za ta fuskanci cin zarafi a rayuwarta.

Wasu ƙasashe da dama kuma suna bari ana auren wuri ga yara mata, wanda ke hana su damar samun ilimi da damarmaki ko rayuwa mai kyau. Ga mata miliyan 676 da suke zaune a wuraren da ake fama da rikici ba a cika bin tsarin doka ba, kuma masu aikata hakan na ci gaba da cin karensu ba babbaka.

Akwai buƙatar samun haɗin kan ƙasashen duniya idan ana son yin adalci da ɗaukar matakin da ya dace. Dole a tabbatar da amfani da dokokin da za su kare ƴancin mata da ƙanan yara daga rikici, cin zarafi da tauye haƙƙi, yayin da su ma kotuna ya kamata su ba kowace mace ƙwarin gwiwa da kariya.

Al'ada na da muhimmanci, amma kuma idan ta zama hanyar jefa damuwa, akwai buƙatar canji.

Akwai buƙatar tabbatar da cewa an daina irin waɗannan al'adu.