Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya kamata ku sani kan babban zaɓen Najeriya na 2027
Yayin da shirye-shiryen zaɓukan 2027 ke ci gaba da kankama, tuni ƴan siyasa suka fara tashi haiƙan domin ƙoƙarin cika burinsa na siyasa a kakar zaɓen da ke tafe.
Zaɓen zai kasance na takwas da ƙasar ta yi tun bayan komawarta turbar dimokraɗiyya a jamhuriya ta huɗu.
Tuni dai hukumar zaɓen ƙasar ta saka watannin Janairu da Fabrairun sabuwar shekarar domin gudanar da zaɓukan.
Cikin wannan muƙala, mun tattaro wasu muhimman bayanan da ya kamata ku sani game da zaɓen mai zuwa.
Mun gina labarin namu ne ta hanyar bibiyar sahihan bayanai daga shafin hukumar zaɓen ƙasar, INEC.
Zaɓen shugaban ƙasa
Hukumar zaɓen ƙasar, INEC ta saka ranar Asabar, 16 ga watan Janairun 2027 a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.
Tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokraɗiyya a 1999, an zaɓi shugabannin ƙasa guda biyar da suka ja ragamar ƙasar.
Biyu daga cikin shugabannin (Obasanjo da Buhari) sun yi shekara takwas kowanne, yayin da Yar' Adua ya yi shekara uku, Jonathan ya yi shekara biyar, sai kuma Tinubu da ke shekarar mulkinsa ta uku zuwa yanzu, kuma yake hanƙoron samun wa'adi na biyu.
Kamar yadda aka saba za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar ne tare da na ƴan majalisar dattawa da na wakilan ƙasar.
Najeriya dai na da sanatoci 109 - uku daga kowace jiha - sai ɗaya daga birnin Abuja, yayin da take da ƴanmajalisar wakilai 360, waɗanda ake zaɓa gwargwadon yawan al'ummar yankunan da suka fito.
Zaɓen gwamnoni
Kamar yadda jadawalin hukumar zaɓen ya nuna za a gudanar da zaɓen gwamnoni bayan na shugaban ƙasa da mako biyu.
INEC ta ce za a gudanar da zaɓen gwamnonin ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairun 2027.
Za a gudanar da zaɓukan gwamnonin a jihohi 28 na ƙasar, yayin da sauran jihohin takwas na ƙasar za a yi zaɓukan gwamanan daga baya.
Haka kuma za a gudanar da zaɓukan gwamnonin tare da na ƴanmajalisar dokoki na jihohi.
Jihohi 8 da ba za a yi zaɓen gwamna a 2027 ba
Akwai jihohin ƙasar takwas da ba za a yi zaɓukan gwamna a watan Fabrairun 2027 ba, sakamakon wasu matsaloli da suka janyo tsaiko a zaɓukan jihohin.
Jihohin takwas sun haɗa da: Kogi da Bayelsa da Imo da Anambra da Edo da Ekiti da Osun da kuma Ondo.
Ana gudanar da zaɓukan waɗannan jihohi ne daga baya.
Zaɓukan fitar da gwani da yaƙin neman zaɓe?
Jadawalin zaɓukan 2027 da INEC ta fitar ya nuna cewa za a gudanar da zaɓen fitar da gwani, da kuma warware duk wata taƙaddama da za ta taso a lokacin zaɓukan, daga ranar 22 ga watan Afrilun 2026 zuwa 30 ga watan Mayun 2026.
Za a fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya daga ranar 19 ga watan Agusta 2026.
Sai kuma yaƙin neman zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi, da za a fara daga ranar 9 ga watan Satumban 2026.
Sabon shugaban INEC
Zaɓen na 2027 zai kasance ƙarƙashin jagorancin sabon shugaban hukumar zaɓen ƙasar, Farfesa Joash Amupitan.
A ranar 9 ga watan Oktoban 2025 ne Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya naɗa Amupitan matsayin shugaban INEC, bayan ƙarewar wa'adin tsohon shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu.
Farfesa Amupitan ne mutum na shida da ya jagorancin INEC tun bayan komawar ƙasar mulkin dimokraɗiyya a 1999.
Sai dai yana fuskantar suka da zarge-zargen ɗaukar ɓangarancin a aiki, kama daga na addini zuwa na siyasa.
Majalisar Ƙoli kan Harkokin Shari'ar Musulunci a Najeriya (SCSN) na zarginsa da iƙirarin kisan Kiristoci a ƙasar.
Yayin da wasu mambobin jam'iyyar ADC ke zarginsa da alaƙa da jam'iyyar APC mai mulki.
Sai dai sabon shugaban na INEC ya sha musanta zarge-zargen.
Guguwar shiga APC
Wani abu da masana da masu bibiyar siyasa ke ganin zai ɗauki hankali a zaɓen na 2027 shi ne yadda ƴan siyasa musamman masu riƙe da muƙamai ke tururuwar shiga jam'iyyar APC mai mulki.
Bayan zaɓen 2023, jam'iyyar APC na da gwamnoni 16, banda jihohi takwas da ba a yi zaɓukansu a lokacin ba.
Amma zuwa yanzu jam'iyyar na da gwamnoni 31, bayan da gwamnonin adawa masu yawa suka koma jam'iyyar.
Haka ma jam'iyyar ta samu gagarumin rinjaye a majalisar wakilai da ta dattawa inda take da kashi 2 cikin 3 na mambobi a majalisun ƙasar biyu.
Haɗakar ADC
Wani abu da zai ƙara ɗaukar hankali a zaɓen na 2027 shi ne yadda manyan jiga-jigan hamayyar ƙasar suka dunƙule ƙarƙashin jam'iyyar ADC da nufin ƙalubalantar APC a zaɓen da ke tafe.
Atiku Abubakar da ya zo na biyu a zaɓen 2023 da Peter Obi da ya zo na uku da kuma Sanata Rabi'u Kwankwaso da ya zo na huɗu, duk sun dunƙule a jam'iyyar ta ADC.
Idan aka haɗa adadin ƙuri'un da suka samu a 2023, sun zarta na Tinubu nesa ba kusa ba, wani abu da ya sa ake ganin zaɓen an 2027 zai bayar da mamaki.
Ko a zaɓen 2015 ma, jam'iyyar APC ta haɗakar ƴan hamayya ta samu nasarar kawar da PDP da ta shafe shekara 16 a kan mulki.
Sauye-sauyen dokar zaɓe
Hukumar INEC ta kuma ɓullo da wasu manyan sauye-sauye a dokokin zaɓen ƙasar.
INEC ta ce ta ɓullo da sauye-sauyen ne domin inganta ayyukanta da ƙarfafa zaɓukan ƙasar.