Abin da muka sani kan hare-haren ƴanbindiga 'mafiya muni' a Bamako da kewaye

    • Marubuci, Ousmane Badiane
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist BBC Afrique
    • Marubuci, Makuochi Okafor
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar sojin Mali ta ce ƴanbindiga sun ƙaddamar hare-haren haɗin gwiwa a faɗin ƙasar, ciki har da Bamako babban birnin ƙasar.

''Yanzu haka dakarun tsaronmu na fafatawa da ƴanbindigar domin daƙile hare-haren'', kamar yadda sanarwar sojojin ƙasar ta bayyana.

Shaidu sun faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun riƙa jin ƙarar abubuwan fashewa da asubahin ranar Asabar a yankin Kati, wani babban sansanin soji da ke wajen birnin Bamako.

Tuni aka girke sojoji domin toshe titunan yankin.

An kuma samu rahotonnin hare-hare a yankin Gao da ke arewa maso gabashin ƙasar da kuma yankin Sevare da ke tsakiyar ƙasar.

Sanarwar sojojin ƙasar

Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta fitar a ranar Asabar da safe, ta ce ''ƴanta'adda ɗauke da makamai'' sun ƙaddamar da hare-hare kan sansanoni da barikokin soji'' a Bamako da wasu yankunan ƙasar.

Rundunar sojin ƙasar ta ce "har yanzu dakarunta na fafatawa da maharan a ƙoƙarin da suke yi na ''daƙile hare-haren''.

Hukumomin ƙasar na kira ga mazauna yankunan da lamarin ya shafa su kwantar da hankula.

Wani matafiyi daga Ethiopia ya shaida wa BBC an soke duka jiragen da suka yi niyyar tashi zuwa Bamako a safiyar yau Asabar.

Kawo yanzu babu tabbas ko hare-haren sun shafi babban filin jirgin sama na Modibo Keïta da ke wajen birnin Bamako.

Martanin ƙasashen duniya da na makwabta

Ofishin jakadancin Amurka a Mali ya shawarci yan Amurka ''su tsaya inda suke'', bayan samun rahoton abun fashewa a kusa da garin Kati da kuma filin jirgin sama.

Amurkan ta kuma buƙaci ƴan ƙasarta su kauce wa zuwa waɗannan wurare har sai al'amura sun daidaita.

Ulf Laessing, Shugaban wata gidauniyar kula da yankin Sahel, ya shaida wa BBC cewa wannan ka iya zama ''harin haɗin gwiwa na masu iƙirarin jihadi mafi muni cikin shekaru''.

Bidiyoyin da ke yawo a shafukan sada zumunta, da ƙwararrun masana bayanan sirri suka yi nazari, sun nuna yiwuwar haɗin gwiwa takanin ƙungiyoyin JNIM da mayaƙan tawayen Azawad (FLA) wajen ƙaddamar hare-haren.

Kakakin FLA, Mohamed Elmaouloud Ramadane, ya yi iƙirarin cewa mayaƙansa sun ƙwace iko da wasu muhimman wurare a Kidal da Gao,.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ya yi kira ga ƙasashen Burkina Faso da Nijar su shiga tsakani.

Sai dai BBC ba za ta iya tabbatar da sahihancin wannan iƙirari ba.

A baya-bayan nan ne Mali da Niger da kuma Burkina Faso suka fice daga ƙungiyar ECOWAS tare da kafa ƙawancen Sahel.

Sun kafa sabuwar ƙungiyar da nufin, amfani da ma'adinan ƙasashen a cikin gida da gina abubuwan more rayuwa, da zirga-zirga tsakanin ƙasashen ba tare da shinge ba, da nufin ƙarfafa haɗin kai.

Duka ƙasashen uku a yanzu na ƙarƙashin mulkin soji, da suka ƙace mulki ta hanyar juyin mulki.

Mali ta shafe fiye da shekara 10 tana fuskantar ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

Ƙasar Mali na ƙarƙashin mulkin soji, wadda Janar Assimi Goïta ke jagoranta bayan ƙwace mulki a 2020, inda ya yi alƙawarin maido da tsaro tare da kawar da ƙungiyoyin ƴanbindiga, to amma har yanzu ƙasar na ci gaba da fuskantar hare-haren ƴanbindigar.