Labarai da dumi-dumi, 'Ƴanbindiga sun ƙaddamar da hare-haren haɗin gwiwa a faɗin Mali'
Rundunar sojin Mali ta ce ƴanbindiga sun ƙaddamar hare-haren haɗin gwiwa a faɗin ƙasar, ciki har da Bamako babban birnin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta fitar a ranar Asabar da safe, ta ce har yanzu ana ci gaba da faɗa tsakanin sojoji da ƴanbindigar.
''Yanzu haka dakarun tsaronmu na fafatawa da ƴanbindigar domin daƙile hare-haren'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Shaidu sun faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun riƙa jin ƙarar abubuwan fashewa da asubahin ranar Asabar a yankin Kati, wani babban sansanin soji da ke wajen birnin Bamako.
Tuni aka girke sojoji domin toshe titunan yankin.
An kuma samu rahotonnin hare-hare a yankin Gao da ke arewa maso gabashin ƙasar da kuma yankin Sevare da ke tsakiyar ƙasar.
Ƙasar Mali na ƙarƙashin mulkin soji, wadda Janar Assimi Goïta ke jagoranta bayan ƙwace mulki a 2020, inda ya yi alƙawarin maido da tsaro tare da kawar da ƙungiyoyin ƴanbindiga, to amma har yanzu ƙasar na ci gaba da fuskantar hare-haren ƴanbindigar.