Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hukuncin da kotu ta yanke kan ɗaukaka ƙarar Sheikh Abduljabbar
Kotun ɗaukaka ƙara a jihar Kano ta yi watsi da ƙarar da Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya shigar, tare da bayar da umarnin ya koma kotun ƙasa domin ci gaba da sauraron ƙarar.
Wannan ne mataki na baya-bayan nan da malamin ya ɗauka a ƙoƙarinsa na kawo ƙarshen zaman jiran zartar da hukunci da yake yi a gidajen gyaran hali daban-daban na Najeriya.
Malamin ya garzaya kotun ne don ƙalubalantar hukuncin da wata babbar kotun shari'ar musulunci ta jihar Kano ta yanke masa na kisa ta hanyar rataya bayan samun shi da laifin "kalaman rashin tarbiyya ga annabi Muhammad", zargin da ya musanta.
A watan Disamban 2022 ne kotun ta yanke masa hukuncin ƙarƙashin mai shari'a Ibrahim Sarki Yola, inda ya ce an an same shi (Abduljabbar) da dukkan laifi huɗu da ake tuhumar sa da su.
Wannan ne karon farko da Sheikh Abduljabbar ya bayyana a wata kotu tun bayan da aka yanke masa hukuncin a 2022.
Sai dai bayan hukuncin da kotun ta yanke a shekarar ta 2022, malamin ya shigar da ƙorafi a babbar kotun jihar Kano, amma shari'ar ba ta gudana ba saboda ya gaza gabatar da lauyoyin da za su kare shi.
A zaman kotun ɗaukaka ƙara na wannan Alhamis ƙarƙashin alƙalai uku, kotun ta bayar da umarnin cewa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya koma babbar kotun jihar Kano don a ci gaba da sauraron ƙarar da ya ɗaukaka kan hukuncin da aka yanke masa.
Kotun ta kafa hujja da cewa ba a yanke hukunci a babbar kotun ƙasa ba, don haka babu wani abu da za ta iya yi.
Bayanai na cewa a tsarin shari'a a jihar Kano, idan babbar kotun shari'ar Musulunci ta yi wani hukunci to dole sai an je babbar kotun jihar, daga nan ne kuma, idan hukuncin bai yiwa mutum daɗi ba, za a iya garzayawa zuwa kotun ɗaukaka ƙara.
Tun da farko dai babbar kotun da ke sauraron ƙarar Sheikh Abduljabbar ta dage sauraron shari'ar har sai ya samu lauyan da zai kare shi.
To amma kassancewar bai gamsu da wannan mataki ba ne ya sanya ya ɗaukaka ƙara.
Lauyan gwamnati Barista Bashir Sale ya roƙi kotun ta kori ƙarar saboda a cewarsa akwai kura-kurai a bayanan da Shiekh Abduljabbar ya shigar.
Shiekh Nasir Abduljabbar Kabara ya isa kotun ne sanye da farar jabba da yar ciki fara, da wasu jakankuna da ake zaton suna ɗauke da hujjoji da bayanan da zai gabatar wa kotun.
To sai dai a lokacin da ya fara magana, sai kotun ta ce sai da hukunci ne ta ke da hurumin ta saurari ƙararsa, don haka ya koma kotun ƙasa, wato babbar kotun jiha.
Game da rokon da ya yi wa kotun cewa ta mayar da shi gidan yarin Kano, daga Abuja kasancewar ya yi zargin yana cikin haɗari, kotun ta ce ba ta hurumin ta saurari wannan roƙo, sai ya koma babbar kotun jihar, saboda ba ita ce ta ɗaure shi ba.
Wane ne Malam Abduljabbar?
Abduljabbar Nasiru Kabara ɗa ne ga mashahurin malamin addinin Musulunci Sheikh Nasiru Kabara, wanda ya jagoranci mabiya ɗariƙar Qadiriyya ta sufaye a Najeriya.
Sai dai salon wa'azin malamin ya janyo cece-ku-ce a shekarun 2020, inda ya riƙa shan suka kan wasu kalamai da ake ganin tamkar cin zarafi ne ga Annabi Muhammdu.
Wa'azozin nasa sun janyo zafafan martani daga malaman Musulunci da dama.
Bayan haka ne gwamnatin jihar Kano ta shirya muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da wasu malamai a Jihar a ranar Asabar, 10 ga watan Yulin 2021.
Malaman da aka gayyata domin yin muƙabala da malamin su ne:
- Malam Mas'ud Mas'ud Hotoro daga ɓangaren ɗariƙar Ƙadiriyya kuma tsohon ɗalibin Sheikh Abduljabbar
- Malam Abubakar Mai Madatai daga ɓangaren Tijjaniyya
- Mallam Kabir Bashir Kofar Wambai daga ɓangaren ƙungiyar Izala
- Dr. Muhammad Rabiu Umar Rijiyar Lemo daga ɓangaren Salafiyya