Waɗanne ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ne suka samu shiga gasar Firimiyar Najeriya a bana?

Lokacin karatu: Minti 4

A gasar Firimiyar Najeriya, daga cikin abubuwan da suka daɗe suna ci wa masu sha'awar ƙwallon ƙafa tuwo a ƙwarya, akwai kwan-gaba-kwan-baya da ƙungiyoyin ke yi wajen samun nasara.

Daga cikin abubuwan da suke jawo tsaikon, akwai irin tallafin da gwamnonin jihohi suke ba ƙungiyar.

A lokuta da dama, idan an samu gwamna mai sha'awar ƙwallo, ƙungiyar ƙwallon ƙafar jihar na nuna ƙwarewa, amma da zarar ya sauka, an samu wanda ba ya sha'awar ƙwallo sai a koma gidan jiya.

Wannan ya sa aka riƙa hanƙoron ganin ɗaiɗaikun mutane masu zaman kansu sun fara shiga harkar suna zuba kuɗi a ciki, inda ake tunanin idan an samu ƙarin masu zuba jari, harkar za ta samu ƙarin tagomashi.

Kakar gasar 2025-2026

Bayan kusan shekara 18, ƙungiyar Ranchers Bees da ke jihar Kaduna ta samu nasarar komawa babbar gasar ƙwallon ƙafa ta ƙungiyoyin Najeriya, wato Firimiya.

Ƙungiyoyin da suka samu nasarar tsallakawa zuwa gasar su ne:

  • Doma United a jihar Gombe
  • Ranchers Bees a jihar Kaduna
  • Sporting Lagos a jihar Lagos
  • Inter Lagos a jihar Lagos

Wani abu da ya ɗauki hankali shi ne dukkan ƙungiyoyin guda huɗu masu zaman kansu.

A kakar bara ce ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai da ɗan wasan ƙungiyar Valencia ta Spain da tawagar Super Eagles ta Najeriya, Sadiq Umar suka sanar da mallakar ƙungiyar Ranchers Bees ta Kaduna.

Ƙungiyar Rancher Bees, daɗaɗɗiyar ƙungiya ce mai tarihi a jihar Kaduna, da ta yi tashe a arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya a shekarun baya, amma sai ta samu koma-baya, har aka daina maganar ta.

A wata sanarwa da ƙungiyar Ranchers Bees ta fitar, ta bayyana cewa dama a gasar Firimiya ta fi cancantar bugawa.

A nasa ɓangaren, Sadiq Umar ya wallafa a shafinsa na Facebook, cewa ya yi, "duk abin da aka yi da zuciya ɗaya to Allah zai shiga lamarin. Allah mun gode maka, ba iyawarmu ba ce, kai ka ba mu nasara."

Ya kuma yi godiya ga magoya bayan ƙungiyar da ya ce suna bayar da gudunmuwa sosai.

Cigaba ne?

Wani abu da aka daɗe ana tattaunawa a Najeriya shi ne yadda ƙungiyoyi masu zaman kansu ɗin ke fara tashe, amma kuma bayan lokaci sai a daina jin ɗuriyarsu, su ɓace ɓat.

Wannan ya sa wasu suke ganin komai lalacewar ƙungiyoyin da gwamnati ke ɗaukar nauyi, inda wasu ke cewa ko ba komai, suna samun albashi duk wata.

Sai dai nasarar da ƙungiyar Remo Stars ta jihar Ogun ke samu, da irin rawar da take takawa a gasar Firimiya, ta sa an fara ganin akwai haske mai kyau a samun ƙungiyoyi masu zaman kansu a ƙasar.

Ƙungiyoyi masu zaman kansu da yanzu haka suke fafatawa a gasar Firimiyar Najeriya su ne:

  • Remo Stars ta jihar Ogun
  • Barau FC ta jihar Kano
  • Kun Khalifat a jihar Imo

Idan har duka guda ukun suka tsira daga faɗawa gasar baya, za a samu ƙungiyoyi guda bakwai da za su fafata a gasar ta baɗi.

A game da hakan na nuna cigaba a harkar tamaula a Najeriya, ɗan wasan ƙwallon ƙafa a ƙungiyar IFK Värnamo ta Sweden Abdulrazaq Ishaq ya bayyana cewa nasara ce babba samun ƙungiyoyi masu zaman kanu su riƙa zuba kuɗi a harkar.

Abdulrazaq, wanda ɗan Najeriya ne, ya ce tunda a baya dai an saba cewa ƙungiyoyin na ƙarƙashin gwamnati ne, amma sai ya kasance ba sa zuba kuɗi sosai, yana tunanin samun mutane masu zuba jari zai taimaka.

"Ni dai a ra'ayina, cigaba ne a samu masu zuba jari a harkar. Idan aka samu ɗaiɗaikun mutane suna zuba jari, za su taimaka. Ka ga an fara samun manyan mutane suna mallakar ƙungiyoyi suna zuba kuɗaɗe. Hakan na da kyau sosai," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa hakan zai inganta ƙwallon ƙafa a Najeriya.

A nasa ɓangaren, mai sharhi kan wasanni, Salisu Musa Jegus ya ce idan aka auna a ma'aunin da ake auna cigaban ƙwallo a duniya, to lallai za a ce cigaba ne a harkar ƙwallon ƙafa.

A cewarsa, "duk manyan ƙungiyoyin da suka samu nasarori da cigaba a duniya, ba na gwamnati ba ne, ƙungiyoyi ne na ɗaiɗaikun mutane ko haɗaka."

Sai dai ya ce ba haka abun yake a Najeriya ba, domin a cewarsa yana ma fargabar za su iya yin da-na-sanin shiga harkar.

"Ina tabbatar maka a Najeriya, ba haka yake, waɗannan ƙungiyoyin ma za su iya yin da-na-sani saboda ɗabi'u da irin yadda ake gudanar da harkar ba da gaskiya. Ba a iya harkar ba, kuma an ƙi neman waɗanda suka iya su kawo gyara."

Ya ce daga cikin manyan matsalolin ƙwallon ƙafa a ƙasar akwai neman nasara ta dole kum ta kowace hanya.

Ya ce da a ce akwai tsari mai kyau ne, da sai a yi murna da samun ɗaiɗaikun mutane suna zuba kuɗaɗensu, inda ya ƙara da cewa a irin tsarin da ake ciki, akwai sauran rina a kaba.