Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da muka sani kan sake ɓullar korona a Najeriya
Tun bayan fitar wani rahoto da ke cewa an samu wani ɗan ƙasar China da ke ɗauke da cutar korona a birnin Calabar da ke jihar Cross River a kudu maso kudancin Najeriya, hankalin ƴan Najeriya ya tashi.
Ƴan Najeriya dai ba za su taɓa mantawa da irin halin da suka shiga ba a lokacin kullen korona a 2020 watanni bayan ɓarkewar cutar a 2019, baya ga irin mutanen da suka rasu.
Mutum fiye da miliyan bakwai ne dai cutar ta kashe a faɗin duniya, inda kuma fiye da 3000 ƴan Najeriya suka rasu sakamakon cutar.
Ana ganin rahoton ɓullar cutar zai zama mai matuƙar tayar da hankali ga ƴan Najeriyar saboda irin abubuwan da suka fuskanta sakamkon ɓarkewar cutar.
BBC ta yi nazari dangane da haƙiƙanin abin da ya faru.
Abin da ya faru
Ma'aikatar lafiya ta jihar Cross River da ke kudu maso kudancin Najeriya ta tabbatar da samun mai ɗauke da cutar Corona a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Henry Ayuk, wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce an tabbatar da hakan ne a ranar 17 ga watan Afrilun 2026, kuma wani ɗan China da ya shiga ƙasar ranar 17 ga watan Maris ne ke ɗauke da cutar.
Ya ce jikin mara lafiyar ya yi tsanani ne a lokacin da ya ke wani asibiti da ke ƙarƙashin ofishin da yake aiki, kafin daga bisani aka garzaya da shi asibitin koyarwa na jami'ar Calabar.
A cewarsa bayan yi masa gwaje-gwaje a asibitin ne aka tabbatar da cewa yana ɗauke da cutar, kuma a yanzu haka an killace shi.
Ya kuma buƙaci yan jihar da kar su tayar da hankalinsu, a cewarsa suna duk mai yiwuwa na hana cutar yaɗuwa, da ma duk wata cuta a jihar.
Gaske ne an ƙara samun masu cutar 10?
Rahotanni na cewa an ƙara samun masu ɗauke da cutar ta korona mutum 10 a jihar ta Cross River sakamakon mu'amila da ɗan ƙasar China
To sai dai kuma hukumomin lafiya a jihar sun musanta inda suka ce har yanzu mutum daya ne kawai ya kamu da cutar wato ɗan China wanda kuma a yanzu haka yake samun kulawa.
Sai dai ya ce an gano mutum 10 da suka yi hulɗa da wanda aka tabbatar yana ɗauke da cutar, kuma tuni aka killace su kuma ana gudanar da gwaje gwaje kan su.
Kwamishinan lafiya na jihar ta RIvers, Henry Ayuk ya shaida wa taron manema labarai a ranar Alhamis.
"Ina son yin amfanin da wannan damar na sanar wa da ƴan Najeriya cewa labaran da ke yawo an samu ƙarin masu kamuwa da cutar guda 10 a Cross River ba gaskiya ba ne. Mutum ɗaya ne ya kamu," in ji Ayuk.
Me NCDC ta ce?
Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta tabbatar da an samu wani ɗan ƙasar China da ya kamu da cutar korona a birnin Calabar na jihar ta Cross River, kuma ta ce tana aiki da gwamnatin jihar domin shawo kan lamarin.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Talata, NCDC ta ce "mutumin da ke ɗauke da cutar na cikin halin killacewa kuma yana samun sauƙi kamar yadda tsarin yake a Najeriya."