'Sojojin Rasha da na Mali sun janye daga birnin Kidal'
Rundunar sojojin hayan Rasha da ke aiki a Afirka, mai alaƙa da ma'aikatar tsaro ta Rasha ta janye daga birnin Kidal da ke Mali tare da sojojin ƙasar, bayan shafe kwanaki biyu suna yaƙi da ƙungiyar FLA da ta JNIM mai alaƙa da al-Qaeda, kamar yadda rundunar ta wallafa a shafinta na Telegram a yau Litinin 27 ga watan Afrilu.
''Bisa matakin haɗin gwiwa da shugabannin Mali suka ɗauka, jami'an rundunar ta 'Africa Corps' da ke Kidal sun fice daga birnin tare da jami'an rundunar sojin Mali. Sojojin da suka jikkata tare da manyan motocin yaƙi ne suka fara ficewa. Sojoji za su ci gaba da ayyukansu. Har yanzu ana zaman ɗarɗar a Mali,'' in ji ƙungiyar.
Rahotannin ficewar sojojin daga birnin sun soma fitowa ne da yammacin jiya Lahadi a wasu shafukan Telegram masu yada bayanai kan ayyukan sojojin haya na Rasha a Afirka.
Wani sanannen shafi da ke wallafa labarai game da yaƙi a ayyukan sojin ya wallafa abin da ya ce bidiyo ne na yadda mayaƙan FLA da na JNIM ke kai-kawo a sansanin rundunar Africa Corps da ke Kidal, da kuma wasu bidiyo na abin da ya ce yadda Rudunar ke barin sansanin ne.