Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Newcastle na son Jackson,watakil Conte ya koma Chelsea
Newcastle ta bayyana a matsayin kungiyar da ke kan gaba wajan daukar dan wasan Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 24, wanda zai koma Chelsea a bazara bayan da Bayern Munich ta tabbatar da cewa ba za ta mayar da aronsa zuwa matsayin dindindin ba. (Talksport), external
Watakila Nottingham Forest ta dauko dan wasan Middlesbrough da Ingila Hayden Hackney, mai shekara 23, idan dan wasan Ingila Elliot Anderson, mai shekara 23, ya bar kungiyar a bazara. (Sun), external
Kocin Napoli, Antonio Conte na cikin wadanda Chelsea ke son ta dauka a matsayin wadanda za su maye gurbin Liam Rosenior a kakar badi . (Express), external
Kocin Porto Francesco Farioli shi ma na cikin jerin sunnayen mutanen da ta ke sha'awar dauka sai dais ai a shekarar 2028 ne kwantaraginsa zai kare kuma akwai sharadin biyan yuro miliyan 20(Nicolo Schira), external
Arsenal da Chelsea na cikin kungiyoyin firimiya da suka Kali wasan dan kasar Belguim Mika Godts mai shekara 20 wanda ya zura kwallo mai kyau ga Ajax a ranar Asabar. (Teamtalk), external
Manchester United na bibiyar halin da Xavi Simons ya ke ciki a 'Tottenham yayin da suke tunanin daukar dan wasan kasar Netherlands mai shekara 23 a bazara. (Fichajes - in Spanish), external
Everton na sha'awar dan wasan Aston Villa da Scotland, John McGinn mai shekara 31 . (Football Insider), external
Liverpool ta kara kaimi wajan ganin ta ci gaba da rike Alison Becker mai shekara 33 saboda golan na Brazil na son ya koma Juventus(Teamtalk), external
Dan wasan Manchester City da Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31, na jan hankalin Juventus da Barcelona da Paris St-Germain da kuma Al-Hilal. (Caught Offside), external
Dan wasan Ingila John Stones, mai shekara 31, ya na son ya koma Barcelona ya yin da ya kusan barin Manchester City idan kwantaraginsa ya zo karshe a watan Yuni. (Fichajes - in Spanish), external
Liverpool ta tuntubi wakilan RB Leipzig da dan wasan Ivory Coast Yan Diomande, mai shekara 19 (Football Insider), external
Arsenal na bibiyar dan wasan Brazil, Endrick, wanda a halin yanzu yake zaman aro a Lyon daga Real Madrid, kuma za ta iya kai tayin dan wasan mai shekaru 19 idan ya kasance ba shi da wani kwantaragi.(Mundo Deportivo - in Spanish)