Ta ya ya jiragen Iran marasa matuƙa suka sauya iko a rikicin duniya?

    • Marubuci, احمد روابه
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بی‌بی‌سی
  • Lokacin karatu: Minti 7

Yayin da ake tsaka da yaƙin haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Isra'ila da kuma Iran, kwararren nan kan harkokin soji Akram Kharif ya wallafa wani littafi da aka yi wa suna "In the Shadow of Witness."

A cikin littafin, ya bayyana tsari da kuma ci gaban da aka samu a fanni ƙera jirage mara matuƙa a masana'antar ƙere-ƙere da Iran, da kuma bayani kan hanyoyin da Iran ta bi ta zama ɗaya daga cikn manyan masu ƙarfin soji a duniya dun da takunkumin da Amurka ta sa mata.

An sanya bayanan jirage marasa matuƙi na Iran a rahoton yaƙin da ake yi na kan iyaka tsakanin Hezbollah da ke Lebanon da Isra'ila. Bayan an sami wasu ɓaraguzan jiragen an yi nazari mai karfi a kansu, an gano akwai alaƙa tsakanin waɗanda Houthi suke amfani da su a Yemen da wanda ake samarwa a Iran.

A watan Satumbar 2022, duniya ta kaɗu da jin labarin cewa Iran ce ke baiwa Rasha jiragen soji maras matuƙa. Wannan ya biyo hoton jirage biyu da aka gani ƙirar (Shahed 136) suna shawagi a shararin samaniyar Keiv babban birnin Ukraine.

Ta yaya ƙasar da aka sa mata takunkumi na sama da shekara 40 ta iya sauya fasalin girmanta a idanun duniya? mene ne ya ta samar kaiwa ga wannan nasarar.

Takunkumin da aka sawa Iran a 1979 ya tilasta shugabannin Iran su nemo hanyoyin da za su iya magance matsalolinsu da kansu domin karya alƙadarinsu. Wannan yanayi ya sanya su dogaro kan harkokin ƙere-ƙere, maimakon dogaro da masu kai musu ɗauki. Sakamakon takunkumin, Iran ta ƙirkiri wani kawance da ƙasashen waje domin biyan buƙatarta. Ta dogara ne kan abubuwan fasahar da take da shi na cikin gida ta yi hakuri da rashin wasu kayayyakin aikin zannan ta nuna juriya da jajurcewa.

Yayin da Mohammad Reza Pahlavi Shah na Iran ya bar ƙasar a Janairun 1979, ya barta a matsayin mafi ƙarfin soji a yankin. Itama rundunar sojin saman Iran na da jirage ƙirare F-14 Tomcats, F-4 Phantoms, and F-5 Tigers.

A wannan lokacin sojin Iran na matsayi na biyar a duniya ta ɓangaren kayan aiki, bayan sojojin Amurka da Tarayyar Sobiyat da Burtaniya da kuma Faransa. A wannan lokaci ana ganin sojin Iran sun fi ƙarfin na Jamus da China da abokiyar hamayyarta Isra'ila, tun da tana da jirgin F-14 Tomcat na yaƙi, wanda shi ne mafi maƙurar jirgin yaƙi a duniya a lokacin.

Amma kula da jiragen ya ta'allaƙa ne da yawan injiniyoyin Amurka da masana fasaha da ke Iran, sa'annan kayan gyaransa a Amurka ake samunsu a kamfanin Grumman. Saboda waɗannan dalilai jiragen sun dogara ne kacokan kan Amurka domin tafiyar da su.

Bayan faɗuwan garkuwa Shah, mafi yawan kwamandojin iran ko dai sun gudu sun bar ƙasar ko kuma an kashe su ko kuma an ɗaure su a gidajen yari. Sai injiniyoyin Amurka da masana fasaharsu suka bar Iran, kuma kamfanonin Amurkan suka warware alƙarsu da sabuwar gwamnatin Iran.

Dole ƙanwar naƙi.

A Satumbar 1980, dakarun Iraƙi suka afkawa Iran, fara yaƙi tsakanin ƙasashen biyu sai da ya kai shekara takwas ana yi. An yi amfani da munanan makamai wajen lalata abubuwa da kisa ciki har da amfani da makamai masu munanan sinadarai, kuma an kashe kimanin mutum miliyan ɗaya a lokacin.

A farkon wannan yaƙi, dakarun Iraƙi sun fi dama a hannunsu saboda ɗaukakarsu. Sojjin Iraƙi sun sayi wasu jirage daga Tarayyar Sobiyet kuma sun riƙa amfani da tauraron ɗan adam ɗin Tarayyar wajen sanin inda makiyansu suke da kuma motsinsu.

Amma a ɓangaren Iran sojojinta na yaƙi ne cikin yanayi mara daɗi kuma an hana su damar kaiwa da kawowa da samun rahotannin leƙen asiri.

Dan haka Iran na buƙatar ci gaban fasaha domin rayuwa a tsakanin ƙasashen da suke yi mata barazana a kullum. Kuma takunkumin tattalin arziki da aka sa mata ya hana ta damar gyara kanta. Dan haka suka yi wa kansu alƙawarin fara samar da abubuwan ƙirƙire-ƙirƙire a cikin gida, mai makon sayowa daga wasu wurare.

Tunanin cikin sauƙi: Idan ya zama ba za a iya tuƙa jiragen sama da za su iya nuna wuraren maƙiya ba da motsinsu, wataƙila wata ƙaramar fasahar da za a iya iko da ita daga gida ta yi wannan aikin. Wannan fasahar na da sauƙi, tana da wuyar ganewa, sannan tana samar da bayanai masu amfani sosai.

Tun daga 1981, Iraniyawasuka fara tunani kan wannan na'urar da yadda za a sa masu kyamara mai ɗaukar bayanai.An fara samar da wannan tunanin ne a jami'ar Isfahan kuma wasu ɗaliban da ke karantar injiniya ne suka fara zuwa da ita suka aiwatar da ita a raɗin kansu. Sun fara samar da ainihin sangalalon abin kafin daga baya su bunƙasa ta, sannan suka gabatar da ita ga shugabannin ƙasar.

Bayan shekarun gwaji, ana tsaka da gazawa, sai wasu matasa uku na jami'ar Isfahan suka haɗa na'urar suka gwada ta a jirgin ƙasar Khuzestan: a matuƙin jirgin farar hula da ake kira Farshid, da ɗaliban fiziks da suka haɗa da Saeed da Masoud sune suka yi aikin.

Da aka kawo bayanan gwajin na'urar ga sojoji wasu ma izgili suka riƙa yi mata. Tafi kama da 'yar tsanar wasan yara ko saboda an haɗa ta daga wani sinadari da ba a saba gani ba. Fankar da aka haɗa ta da ita, wadda aka haɗa da hannu ce, sannan tankin man an haɗa shi ne da irin ledar jakar asibiti da ake sa magunguna.

Jirgin soji maras matuƙi na farko

A shekarar 1983, jirgin da aka raina ya yi tafiyar kilomita 40 zuwa sansanin sojin Iraƙi inda ya ɗuko hotunan da suka fita kal na wuraren da soji da kuma kaiwa da kawowarsu. An riƙa bashi umarni ne daga Thunder Battalion daga nan kuma aka aura zimmar fara samar da jirage marasa matuki a hukumance.

An auke wannan shiri daga hannun waɗannan ɗalibai zuwa hannun gwamnati. Domin samun abubuwan da ake buƙata na dole wajen haɗa jirage maras matuƙi, dole suka kaucewa wasu takunkumai suka shiga mu'amala da wasu ƙasashe domin samun waɗannan abubuwa.

IRGC sun ƙirƙiri wani kamfani a Dubai amma ta hannun wani kamfani daga Singapore ya riƙa saya musu kayan aiki daga gwammnan ƙasashe. Haka aka riƙa kawo kayan zuwa jami'ar Isfahan ana haɗa su a nan. Wannan ya isa misali kan wata na'ura da aka cire a jikin Shahed 136 wanda aka harbo a Ukraine.

Jirage marasa matuƙan an riƙa amfanin da su a yakin da Iran ta yi da Iraƙi a 1983. Injiniyoyi a Bataliyar Raad suka fara tunanin samar da jirgin soji marar matuƙi a 1987. Jirgin da ya tashi ya ɗauki hotonan maƙiya da motsinsu, amma hakan na buƙatar wasu ci gaban fasaha daga baya kuma Raad suka samar da wannan fasahar da aka yi wa suna "Mohajir".

A shekarar 1988, Iran na cikin ƙasashen da suka fara amfani da "jirgin soji maras matuƙi" (UCAV), abin da ake kira Drone a yau. Amurka da Turkiyya da Isra'ila sun yi fice wajen samar da irin waɗannan jirage, amma dai Iran ita ce kan gaba wajen samar da su.

Jiragen sojin Iran na da muhimmanci sosai kuma an ƙirƙire su ne a 1988, kuma ba sa wuce tazarar kilomita 50. Amma a 2026, Jiragen Iran da aka inganta sukan haura saman ƙasashe da dama sukai hari cikin Isra'ila inda nan aka nufa, kuma tun daga cikin Iran ɗin.

A taƙaice Isra'ila ce ta fara amfani da jiragen da ake kira Drones da zummar hare-haren soja, tun kan Amurka ta fara. Ta fara amfani da su a 1973 lokacin yaƙinta da Masar.

A shakarar 1982 lokacin da suka mamaye Lebanon, Isra'ila ta yi amfani da nau'in Scott da Mustif domin kai hari kan inda makaman masu linzamin Syria suke a Bekka Valley. Wannan ne karon farko da aka yi amfani da jirage marasa matuki a rikicin soji.

Sauya akala

Samar da jirgi maras matuƙi ɗaya yana cin dalar Amurka 20,000, amma hakan Iran ta riƙa harba jiragen sama da 100 afarkon rikicin.

Ba a yi jirage marasa matuki ba da ƙarfi, amma an tsara shi da sauri rashin nauyi da zafin kai hari. Dan haka harin jiragen suna tsayi sosai, kuma makamai masu linzafi suna fin jiragen tsada wajen haɗawa da kashi 10 zuwa 20.

Harin da aka kai wa kamfanin mai na Saudiyya Aramco a 2019, ya nuna fitinar da ke tattare da sabon jirgi maras matuki da irin su Iran ke da shi, tun da tsarin kariyar samaniya na Amurka ma baya iya hana jiragen da aka haɗa a Iran. Duk da cewa dai HOuthi ne suka yi iƙirarin kai harin, amma dai abin dubawa shi ne jiragen an harba su ne daga Iran ko Iraƙi.

Ɓarnar da harin ya janyo ta laƙumi biliyoyin dala, yayin da kuɗin da aka kashe aka kai harin bai fi miliyoyin dala ba. Wannan kuma ya isa ya gwada wanda ya yi nasara da wanda ya faɗi a yaƙin da ake yi na jirage marasa matuƙa a duniya a yanzu.