KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya na ranar 27/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Abdullahi Bello Diginza

  1. An ceto marayu 15 cikin yaran da ƴan bindiga suka sace a Kogi

    yan bindiga

    Asalin hoton, SOCIAL MEDIA

    Wasu ƴan bindiga sun sace yara 23 da mai ɗakin shugaban makaranta da gidan marayu na Dahallukitab da ke Zariagi, wani ƙauye da ke Kabba a kan titin Lokoja zuwa Okene da ke ƙaramar hukumar Adavi a jihar Kogi.

    A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kingsley Fanwo ya fitar a yau Litinin, ya ce an sace yaran ne a daren ranar jiya Lahadi.

    Ya kuma ce jin kaɗan bayan samun rahoton harin, ƴan sanda tare da goyon bayan wasu jam'ain tsaro suka isa yankin, inda suka yi nasarar ceto yara 15.

    Gwamnatin jihar na Allah-wadai da harin, inda ta bayar da tabbacin cewa jami'an tsaro na ci gaba da aiki wajen ceto sauran mutanen.

    Sai dai sanarwar ta bayyana cewa makarantar wadda kuma take aiki a matsayin gidan marayu ba ta da rajista, inda ya ce irin waɗannan makarantu da ke irin waɗannan yankunan kuma gwamnati ba ta san da su ba, na kasancewa cikin barazana musamman a wannan lokaci na rashin tsaro.

  2. Majalisar dokokin Kano ta amince da naɗa Garo a matsayin mataimakin gwamna

    garo

    Asalin hoton, GARO/FACEBOOK

    Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da naɗin Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar bayan ta tantance shi.

    A ranar 22 ga wannan watan ne gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya miƙa sunan Murtala Garo ga majalisar.

    Mataimakin kakakin majalisar Hon. Muhammad Bello Butubutu wanda ya tabbatar wa da BBC amincewar, ya ce sun tabbatar da cewa Garo ɗan asalin jihar Kano ne, kuma ya yi karatu har matakin HND wanda ya kai ya riƙe muƙamin, hakazalika sun tabbatar ya kai shekarun zama mataimakin gwamna.

    Ya kuma ce sun tabbatar Murtala Sule Garo na da gogewar da zai iya zama mataimakin gwamna domin a baya ya zama shugaban ƙaramar hukuma, da kwamishinan ma'aikatar kula da kananan hukumomi, hakazalika ya taɓa yin takarar neman zama mataimakin gwamna.

    Hon Muhammad Bello ya ce bayan sun tabbatar da hakan, ya gabatar da rahotonsa a zauren majalisar, inda aka bayar da damar yin tambayoyi ko kalubalantar rahoton, sai dai ba a samu wanda ya kalubalanci rahoton ba wanda ke nufin an amince da shi.

    Zaɓen sabon mataimakin gwamnan dai na zuwa ne bayan murabus ɗin da tsohon mataimakin gwamna Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi a ranar 27 ga watan Maris ɗin 2026.

    Wannan dai ya samo asali ne sakamakon sauye-sauyen sheƙa da aka samu tsakanin gwamnan da mataimakinsa da wasu 'yan majalisar jihar da sauran masu ruwa da tsaki cikin gwamnatin.

  3. Matuƙa jiragen ruwan da suka maƙale a Mashigar Hormuz na cikin 'mawuyacin hali'

    jiragen ruwa kan teku

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban ƙungiyar masu jiragen dakon mai ya ce dubban ma'aikatan jirage sun maƙale a mashigar Hormuz, lamarin da ya fara shafar lafiyar ƙwaƙwalwarsu, da sanya musu gajiya da kuma barazana ga lafiyarsu.

    Da yake bayyana halin da ma'aikatan da suka maƙale ke ciki, Tim Wilkins, shugaban ƙungiyar Intertanko, ya kuma ce samun abinci da sauran kayyayakin amfani na ci gaba da yi musu wahala, a yayin da ake ci gaba da samun tsaiko a ɗaya daga cikin mashigar ruwa mafi hada hadar jirage a duniya.

    Ya bayyana cewa gwamnatoci na ɗaukar matakai daban daban, inda wasu ƙasashe kamar Philippines ke hana sauya ma'aikata, yayin da wasu kuma ke buƙatar ƴan ƙasashen su dawo gida.

  4. Kongo za ta kafa sabuwar rundunar samar da tsaro a wuraren haƙar ma'adinai

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ta sanar da ƙirƙiro wata sabuwar rundunar tsaro domin inganta tsaro a fannin haƙar ma'adinai a ƙasar.

    Rundunar, wadda za a kafa ƙarƙashin wani asusun haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Haɗaɗɗiyar ɗaular Larabawa na dala miliyan 100, na da nufin ɗaukar ma'aikata aƙalla dubu uku domin samar da tsaro a wuraren haƙar ma'adinai, da kuma sanya ido kan haƙo ma'adinai har ya zuwa yadda ake sarrafa su.

    Kongo, wadda ita ce ƙasa ta biyu wajen samar da jan ƙarfe a duniya, na fama da rikicin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a gabashin ƙasar da ke da ɗimbim ma'adinai, inda rikicin da ake yi ya kai ga mutuwar dubban mutane.

  5. Ukraine ta ce tana kashe sojojin Rasha dubu talatin duk wata

    Zelensky

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Shugaban Ukraine Zelensky

    Kwamandan rundunar jirage marasa matuƙa ta ƙasar Ukraine ya shaida wa BBC cewa dakarunsa na daƙile ci gaban sojojin Russia ta hanyar kashe sojojin da yawansu ya kai dubu talatin a duk wata.

    Robert Brovdi, wanda aka fi sani da “Magyar,” ya ce suna kashe sojojin ne daidai da waɗanda Moscow ke iya ɗauka aiki a kowane wata, inda kuma jirage marasa matukan ke ɗaukar hoton kowanne soja da suka kashe, sannan a tantance tare da rubuta bayanansa.

    Mista Brovdi ya kuma ce hare-haren jirage marasa matuƙa na dogon zango kan cibiyoyin mai na Rasha za su ci gaba, domin sun rage fitar da man fetur din kasar sosai.

    Wakiliyar BBC ta ce yana fatan irin wadannan hare hare da ake kai wa can cikin Rasha da kuma yawan dakarun da ake kashe wa ƙasar a filin daga zai tayar da hankalin ƴan kasar, kana su nuna shakku kan yaƙin da shugabansu ya fara, harma su taka masa birki.

  6. 'Sojojin Rasha da na Mali sun janye daga birnin Kidal'

    Yadda sojoji ke ficewa daga Mali

    Asalin hoton, AFP VIA GETTY

    Rundunar sojojin hayan Rasha da ke aiki a Afirka, mai alaƙa da ma'aikatar tsaro ta Rasha ta janye daga birnin Kidal da ke Mali tare da sojojin ƙasar, bayan shafe kwanaki biyu suna yaƙi da ƙungiyar FLA da ta JNIM mai alaƙa da al-Qaeda, kamar yadda rundunar ta wallafa a shafinta na Telegram a yau Litinin 27 ga watan Afrilu.

    ''Bisa matakin haɗin gwiwa da shugabannin Mali suka ɗauka, jami'an rundunar ta 'Africa Corps' da ke Kidal sun fice daga birnin tare da jami'an rundunar sojin Mali. Sojojin da suka jikkata tare da manyan motocin yaƙi ne suka fara ficewa. Sojoji za su ci gaba da ayyukansu. Har yanzu ana zaman ɗarɗar a Mali,'' in ji ƙungiyar.

    Rahotannin ficewar sojojin daga birnin sun soma fitowa ne da yammacin jiya Lahadi a wasu shafukan Telegram masu yada bayanai kan ayyukan sojojin haya na Rasha a Afirka.

    Wani sanannen shafi da ke wallafa labarai game da yaƙi a ayyukan sojin ya wallafa abin da ya ce bidiyo ne na yadda mayaƙan FLA da na JNIM ke kai-kawo a sansanin rundunar Africa Corps da ke Kidal, da kuma wasu bidiyo na abin da ya ce yadda Rudunar ke barin sansanin ne.

  7. An ayyana kwanaki biyu na makokin ministan tsaron Mali

    Rahotanni daga Mali sun ce an harbi shugaban hukumar tattara bayanan sirri na ƙasar tare da jikkata shi a hare haren da aka kai a babban birnin ƙasar Bamako, da wasu birane a ranar asabar.

    Gwamnatin sojin Mali ta ayyana kwanaki biyu na makokin mutuwar ministan tsaron ƙasar Sadio Camara a faɗin ƙasar, wanda aka kashe a wani harin ƙunar baƙin wake kusa da gidansa da ke babban birnin ƙasar Bamako a ranar Asabar.

    Janar Camara ya mutu ne a yayin da yake karɓar kulawa sakamakon raunukan da ya samu a lokacin da rahotanni suka ce yana gwabzawa da mayaƙan jiihadi da suka kai hari gidansa.

    Mali dai na fama wajen daƙile ayyukan ƴan bindiga duk da tsananta ayyukan tsaro da ake yi tun bayan da sojoji suka ƙwace mulki a 2020.

  8. Farashin ɗanyan mai ya ƙaru bayan tsaiko a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran

    mai sayar da mai

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyan mai ya ƙaru a kasuwannin duniya bayan da aka sake samun tsaiko a shirin zagaye na biyu na tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran.

    Farashin mai nau'in Brent ya ƙaru da kusan kashi 2 cikin 100 zuwa dala 107.26 duk ganga, yayin da ɗanyan man da ake kasuwancinsa a Amurka ya ƙaru da kashi 1 cikin 100 zuwa dala 95.40.

    Hakan na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Asabar ya ce Washington ta soke shirin aika tawaga Pakistan domin tattaunawa da wakilan Iran.

    Samar da makamashi a duniya ya soma fuskantar tsaiko tun soma yaƙi a Iran, bayan da aka rufe mashigar Hormuz.

  9. Buƙatun Amurka na son kai ne suka sa aka gaza cimma matsaya - Iran

    Abbas Aragchi

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ministan harkokin waje na Iran Abbas Aragchi

    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, ya ce an gaza cimma matsaya a tattaunawar da suka yi da Amurka a farkon wannan watan da nufin kawo karshen yaƙin ne saboda abin da ya kira '' buƙatun Washington na son kai".

    A yayin da ya isa Rasha domin tattaunawa da shugaba Putin, Mista Arachi ya ce tattaunawar zaman lafiyar zagaye na farko a Pakistan ya soma samun nasara, amma kuma daga bisani ya ruguje saboda yadda Amurka ta tunkari tattaunawar.

    Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa Iran ta gabatar da wani sabon ƙuduri ga Washington na yadda za a buɗe mashigar Hormuz da kuma kawo ƙarshen yaƙin, amma kuma ta ɗage batun tattaunawa kan nukiliya zuwa wani lokaci na gaba.

  10. Gwamnatin Nijar ta haramta sayar da shinkafar Bulmex

    shikafa a hannu da ake ɗibo daga buhu

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar kasuwanci a Jamhuriyar Nijar ta haramta sayar da wata shinkafa da ake kira Bulmex.

    Gwamnatin ta hana shigowa da sayar da wannan shinkafa a faɗin ƙasar, sakamakon wani sinadari mai cutarwa da aka ce bincike ya gano a cikinta.

    A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar mai lamba 0031, ma'aikatar ta ce bayan binciken lafiya da aka yi a kasuwanni, an gano ɓurɓushin ƙarfe a wasu buhuhunan shinkafar.

    Sanarwar ta kuma yi kira ga yan kasuwa su yi gaggawar fitar da shinkafar daga shagunansu ko su fusknaci hukunci.

    Mamman Nouri, shugaban wata kungiyar kare masu sayen kaya a Nijar, ya yabawa matakin gwamnati, sai dai ya kuma ce akwai sakaci daga bangaren gwamnati na rashin yin binciken da ya dace kan abubuwan da ake shigarwa ƙasar.

    Mamman ya kuma yi kira ga ƴan kasuwa su yi hattara tare da yin taka-tsantsan kan wasu dabaru da yake zargi ana yi don shigar da shinkafar, '' zai iya yiwuwa a chanza mata buhu, don haka in ka siya ta buɗe, in akwai mayen karfe ka saka, zai janyo duk wani karfe da ke ciki, idan an samu, daga nan sai ka gaya wa hukuma mafi kusa'' in ji shi.

  11. Rikicin ƙabilanci ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da 40 a gabashin Chadi

    Jami’an gwamnati a ƙasar Chadi, sun ce aƙalla mutane arba’in da biyu ne suka mutu a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙabilu a gabashin ƙasar.

    An yi imanin cewa tashin hankalin da ya faru a lardin Wadi Fira, ya samo asali ne daga taƙaddama kan wata rijiyar ruwa, lamarin da daga bisani ya haifar da jerin hare haren ramuwar gayya a faɗin yankin.

    Mataimakin firaministan ƙasar, Limane Mahamat, ya shaida wa gidan talabijin ɗin ƙasar cewa yanzu an shawo kan lamarin.

    Gabashin Chadi dai ya daɗe yana fama da rikice-rikicen kabilanci tsakanin manoma da larabawa makiyaya tsawon shekaru.

    Sai dai kuma rikicin ya ƙara tsananta sakamakon ƙarancin albarkatu da matsalolin tsaro, musamman bayan kwararar ‘yan gudun hijira sakamaon yaƙin basasar Sudan.

  12. Yau za a gurfanar da mutumin da ake zargi da kai wa Trump hari

    wani mutum a kwance da hannunsa a baya

    Asalin hoton, @REALDONALD TRUMP / TRUTHSOCIAL

    Nan gaba a yau Litinin ne za a gurfanar da mutumin da ake zargi da kutsawa wajen wata liyafar cin abinci domin kai hari ga Shugaban Amurka, Donald Trump.

    Za a tuhumi Cole Tomas, mai shekara 31 a duniya, daga Los Angeles, da laifin kai hari ga jami’in gwamnatin tarayya da kuma amfani da bindiga yayin aikata laifin.

    Ana zargin ya buɗe wuta ne a kusa da wurin binciken jami'an tsaro, lamarin da ya tilasta fitar da Shugaba Trump daga wurin cikin gaggawa.

    Jami’an tsaro sun ce an samu wani sakon email da maharin ya aikawawa 'yan uwansa mintuna kaɗan kafin ƙaddamar da harin, inda a ciki yake bayani a kan ajandarsa ta kai hari kan jami'an gwamnatin Mista Trump din.

  13. Ƴan bindiga sun kashe Ministan tsaron Mali Sadio Camara

    Sadio Camara

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan tsaron Mali, Sadio Camara, ya rasu sakamakon wani harin ƙunar baƙin wake da aka kai gidansa da ke kusa da babban birnin ƙasar, Bamako, a ranar Asabar.

    Harin na ɗaya daga cikin jerin hare-hare da masu ɗauke da makamai da kuma ‘yan awaren Tuareg suka kai a wasu birane daban-daban a lokaci guda.

    Wakilin BBC ya ce tsawon gwamman shekaru kenan ƴan awaren na Tuareg da a aka fi sani da FLA ke ta ƙokarin ɓallewa don kafa na su shugabancin, a wannan yanki, lamarin da ya sa suka haɗa kai da ƙungiyar JNIM mai akala da Alqa'eda wadda ita kuma manufarta ita ce yana manufarta a yankin wajen kai waɗannan hare hare.

    A yanzu dai ƴan tawayen na Tuareg sun ce suna riƙe da garin Kidan, mai muhimmanci na yankin hamada, inda wata rundunar tsaron Rasha ke da sansani.

    Haka kuma an kai hari gidan shugaban mulkin sojin kasar Assimi Goïta, amma bai samu wani rauni ba.

  14. Wakilin Iran ya isa Rasha domin ganawa da Putin

    Araqchi na gaisawa da jami'an Rasha

    Asalin hoton, TELEGRAM/REUTERS

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya isa birnin St Petersburg domin tattaunawa da shugaban Rasha, Vladimir Putin.

    Rahotannin kafafen watsa labaran Amurka sun ce Iran ta gabatar da wani sabon shiri ga Washington, wanda ya mayar da hankali kan buɗe mashigin Hormuz, da kuma kawo ƙarshen yaƙin, wanda kuma ya buƙaci ɗage tattaunawar nukiliya zuwa wani lokaci na gaba.

    Tun da farko, Mista Araghchi ya ce tattaunawarsa a ƙasar Oman a ranar Lahadi ta mayar da hankali kan hanyoyin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin.

    Sai dai Shugaba Donald Trump ya ce dole ne duk wata yarjejeniya ta ƙunshi buƙatar Iran ta yi watsi da duk wani yunƙuri na ƙera makamin nukiliya.

  15. Buɗewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da shiga sabon mako.

    A yau Litinin ma mun shirya tsaf domin kawo muku labarai kan halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa, har ma ku kalli bidiyon da muka wallafa.