Wane ne ke da ƙarfin yanke hukunci a Iran?

    • Marubuci, Amir Azimi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian editor
  • Lokacin karatu: Minti 4

Tambayar da masu bibiyar al'amura ke yi tun bayan ɓarkewar yaƙin da Amurka tare da Isra'ila suka ƙaddamar kan ƙasar Iran ita ce wane ne ke da ƙarfin faɗa a ji a ƙasar?

Amsar wannan tambaya a fili - Mojtaba Khamenei ya zama jagoran addinin Iran sakamakon shahadar mahaifinsa, Ali Khamenei a ranar farko ta yaƙin wato 28 ga watan Fabrairu.

A jamhuriyar Musulunci ta Iran, muƙamin jagora na buƙatar gaggawar yanke hukunci. Jagoran ne mai faɗa a ji da yake yanke magana ta ƙrshe kan batutuwa masu muhimmanci kamar yaƙi, zaman lafiya da tsarin da ƙasar za ta bi.

To sai dai kuma al'amarin na da ƴr sarƙaƙaƙiya.

Donald Trump ya bayyana jagorancin ƙasar ta Iran da "ruguzajje" sannan ya bayar da faɗi cewa Amurka na jiran Iran ta samar da "buƙatun yarjejeniya na bai ɗaya."

Jagoran da ba a gani

Har kawo yanzu ba a Mojtaba Khamenei a bainar jama'a ba tun bayan zama jagoran addinin Musulunci na Iran. Kuma idan ban da wasu ƴan saƙonni da ya fitar ciki har da umarnin rufe mashigar Hormuz, za a iya cewa babu wata shaidar kasancewarsa mai faɗa a ji a ƙsar.

Jami'ai a Iran sun amince cewa an jikkata Mojtaba a hare-haren farko ba tare da bayar da cikakkun bayanan halin da yake ciki ba.

Mujallar New York Times ta ambato wasu majiyoyin Iran, inda ta rawaito a wannan makon cewa akwai yiwuwar ya samu raunuka masu dama da suka hada da fuskarsa wanda hakan ya sa ba zai iya magana ba.

Rashin ganin nasa ya janyo damuwa. Kasancewar mahaifinsa na fitowa ya yi jawabai da kuma daidata ɓangarori biyu da ke rashin fahimta wanda a yanzu haka za a iya cewa kamar an rasa wannan.

Da dama na ganin cewa jagorancin da Mojtaba ya samu ana tsaka da yaƙi shi ne ya hana shi nuna ikon da yake da shi. Wasu kuma na na da ra'ayin cewa raunukan da rahotanni suka ce ya samu sakamakon harin farko a yaƙin ne suka saka ba ya tafiyar da jagorancin yadda ya kamata.

Koma dai wane dalili ne ya janyo hakan, ana ganin umarni da hani ba kamar da ba kafin yaƙi a ƙasar, wanda ke zuwa bai ɗaya.

Kurarin diflomasiyya

A takarda, batun hulɗar jakadanci alhakin gwamnati ne. Ministan harkokin ƙasashen wajr, Abba Aragchi yana ci gaba da wakiltar Iran a tattaunawa da Amurka ƙarƙashin umarnin shugaban ƙasar, Masuod Pezeshkian.

To amma hakan na da wata alamar tambaya sakamakon kasancewar shugaban majalisar dokoki, Mohammed-Bagher Ghalibaf ne ke jagoranci ga tawagar tattaunawar.

Aikin Araghchi ya fi kamar da yin abin da aka umarce shi maimakon yanke hukunci. Aman da ya yi ya lashe dangane da ko mashigar Hormuz na rufe ko buɗe - inda da farko ya nuna mashigar abude take kuma jirage na wucewa amma daga baya ya janye - ya nuna irin ƙarfin da sojoji ke da shi bisa hulɗar jakadanci.

A hannu guda kuma shi Pezeshkian yana alaƙanta kansa da alƙiblar da ƙasar ta saka a gaba ba tare da yanke hukunci ba.

Tsayawar da zango na biyu na tattaunawa da Amurka ta yi a Islamabad ya yi nuni ga hakan. Duk da cewa ƙofofin tattaunawa a buɗe suke, amma da alama ƙasar ba ta da niyyar shiga tattaunawar.

Rawar da sojoji ke takawa

Iko da mashigar Hormuz shi ne wani abun tunƙaho da Iran ke da shi a baya-bayan nan.Sai dai ikon rufe mashigar na tattare da rundunar juyin juya halin Iran da Ahmed Vahidi ke jagoranta, maimakon hulɗar jakadanci.

Kuma hakan na nufin iko na hannun wasu mutane da ba a ganin su. Ba kamar yaƙin da aka yi a baya ba, babu wani shugaba guda wanda ke faɗin abin da za a yi, A maimakon hakan an samu wani sabon salon ƙaddamar da al'amari kafin daga bisani saƙonni masu karo da juna su biyo baya.

Abin da ya fito fili shi ne rundunar juyin juya hali ta IRGC ce ke da iko kan rufe Hormuz ko kuma kai hare-hare a yankin Gulf, sannan kuma daga baya sai kalaman siyasa da na hulɗar jakadanci sai su biyo baya.

Hakan ba yana nufin cewa an samu rauni a sassan gwamnati ba ne amma na nufin ƙarfin iko na IRGC ya ƙaru wataƙila na ɗan wani lokaci, a daidai lokacin da aka rasa hukunci a siyasance.

Bayyanar Ghalibaf

Ana cikin irin wannan tanayi sai Mohammed-Bagher Galibaf ya kunno kai wanda tsohon kwamandan dakarun juyin juya hali ne yanzu kuma ya zama shugaban majalisar dokokin ƙasar ya fito a matsayin mutanen da aka fi jin amonsu a baya-bayan nan.

Ya cusa kansa cikin jerin yarjejeniyoyi sannan ya yi ƴan ƙasa jawabai sannan a wasu lokutan yana nuna yaƙin a matsayin haryar sama wa ƙasa makoma maimakon na wata aƙida.

A tsakanin majalisar dokoki nuna kin amincewa da tattaunawa wani abu ne mai ƙarfi.

Saƙonni daga masu tsaurin fahimta sun ƙaru tare kuma da kafafen watsa labaran gwamnati da masu kamfe da ke nuna cewa amince wa da tattaunawa tamkar wani abu ne na rauni a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar maƙiya.

Matsayar Ghalibaf tana da ruɗarwa domin yana ɗaukar matsaya amma kuma wadda ba ta samu sahhalewa ba duk da yana cewa matsayarsa tana da goyon bayan Mojtaba Khamenei amma kuma akwai ƙaranci shaidar da ke nuna hakan.

Rashin magan da baki guda

Bisa abubuwan da ke faruwa da sauye-sauyen da aka samu a Iran, za a iya fahimtar cewa tsarin na aiki amma kuma za a iya cewa ba irin na da ba wanda umarni ke zuwa daga wuri guda ba.

Ikon jagoran addini na nan amma kuma ba a ganin ana aikata shi. Fadar shugaban ƙasa na da alaƙa da jagoranci amma kuma ba ita ce ke jan ragama ba. Akwai diflomasiyya da ke aiki amma kukam ba ita ce aka fifita ba. Sojoji ne ke riƙe da madafun iko amma kuma ba tare da cikakken goyon bayan al'umma. Masu riƙe da madafun siyasa na ƙoƙarin nuna kansu amma kuma ba tare da an amince da su.

Hakan ba ya nufin ƙasa ta durƙushe ba. Jamhuriyar Musulunci ta Iran na nan yadda take. Sai dai kawai a ce ɓangarorin daban-daban na jamhuriyar na ƙaddamar da al'amura a warwatse wanda wasu ke yi wa kallo tamkar zaman ƴan marina ake yi.