Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya na ranar 28/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Abdullahi Bello Diginza

  1. Chadi ta kori ƴan gudun hijirar Najeriya - AFP

    An kori ɗaruruwan ƴan Najeriya da ke zama a Chadi domin neman mafaka daga hare haren masu iƙirarin jihadi zuwa Najeriya a makon da ya gabata, kamar yadda wasu daga cikinsu suka shaida wa kamfanin dillanci labarai na AFP.

    Hakan na zuwa ne a yayin da masu sharhi ke gargaɗin cewa an samu ƙaruwar hare hare a arewa maso gabashin Najeriya a shekarar da ta gabata.

    Wasu ƴan Najeriya biyu da aka kama a Chadin sun shaidawa AFP cewa ƴan ƙasarsu ɗari shida aka tsare bayan an kama su, kuma aka yi watsi da su a birnin Kousseri, wanda ke kusa da iyakar babban birnin ƙasar N'Djamena.

    Ƴan sandan Chadi sun tabbatar cewa an kori mutanen, amma basu bayar da adadi ba.

    Sun ce sun ƙaddamar da wani shiri da suka saba yi kan ƴan gudun hijira da suka shigo ta ɓarauniyar hanya, ba tare da la'akari da ƙasar su ba.

    '' A ranar Juma'a jami'an tsaro suka dira a gidanjenmu, suka ce duk ƴan gudun hijira daga Najeriya ƴan Boko Haram ne, kuma su fice daga ƙasar su. Kuma suka ɗauki bayanan hannunmu'' kamar yadda Kyari Musa ya shaidawa AFP.

    A cewar sa sun kuma yi gargaɗin cewa duk wada ya dawo kuma aka kama shi zai je gidan yari na shekara 20.

    Ƴan Najeriyan sun kuma ce a ranar Asabar ne jami'an Kwastam na Chadi suka kai su garin Gamboru da ke kan iyakar ƙasar da Najeriya.

    Najeriya dai ta shafe kusan shekara 17 tana fama da mayaƙa masu iƙirarin jihadi, waɗanda suka yi ta bazuwa zuwa ƙasashen Nijar da Kamaru da Chadi.

  2. Amurka na nazari kan tayin Iran na kawo ƙarshen yaƙi

    Fadar gwamnatin Amurka ta ce tana duba wani 'rubutaccen saƙo' daga Iran, wadda Pakistan ta gabatar mata.

    Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta yi tayin buɗe Mashigar Hormuz domin kawo ƙarshen yaƙin gabaɗaya, sai dai za a jinkirta yarjejeniya kan ayyukanta na nukiliya.

    Wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka sun bayyana cewa Shugaban Trump bai ji daɗin shirin Iran ɗin ba.

    Sai dai Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce shirin da Iran ta gabatar 'ya fi yadda yake tunani' , sai dai ya jaddada cewa wajibi ne a tabbatar cewa Iran ba ta taɓa samun makamin nukiliya ba.

    Iran ɗin ta ce buƙatun Amurka na son rai waɗanda suka wuce gona da iri ne ke hana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi.

  3. Ƴansandan jihar Kaduna sun kama gomman masu garkuwa da mutane a watan Afrilu

    Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama mutum talatin da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, da masu safarar makamai 4, tare da tarwatsa gungun masu satar motoci cikin a watan Afrilun 2026.

    A cikin wata sanarwa da Kwamishinan ƴan sandan jihar Rabiu Muhammad ya fitar, ya ce sun sami waɗannan da ma wasu nasarori ne sakamakon yin aiki da bayanan sirri, da aiki bisa tsari da kuma ƙara yawan jami'ai da ke sintiri a faɗin jihar.

    Ya kuma ce sun ƙwato makamai biyar da harsasai, da kuma motoci huɗu da aka sace cikin watan.

    A cewar sa, sun gundanar da wani aiki a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda jami'an tsaron suka yi bata kashi da wasu da ake zargi ƴan bindiga ne, waɗanda suka tsere tare da raunuka kuma suka bar makamansu na AK47 da harsasai.

    Rundunar ta kuma tarwatsa gungun masu satar motoci, inda ta kama wasu da take zargi da satar a Kaduna da Kano da Katsina.

    Haka zalika ya ce ƴan sandan sun ceto wani yaro ɗan shekara bakwai wanda aka sace a ƙaramar hukumar Kubau kuma aka nemi biyan Naira miliyan 40 kuɗin fansa.

    Kwamishinan ƴan sandan ya kuma bayar da tabbacin cewa rundunarsa za ta ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka a jihar Kaduna, inda ya ce a yanzu haka ana ƙoƙari wajen kamo ƴan bindigar da suka tsere da kuma tarwatsa gungun masu aikata laifuka a faɗin ƙasar.

  4. Wani babban jirgin ruwa mai alaƙa da Rasha ya bi ta Mashigar Hormuz

    Wani babban jirgin ruwa da ke da alaƙa da ɗaya daga cikin makusantan shugaban Rasha Vladimir Putin ya wuce ta Mashigar Hormuz, duk da rufe muhimmiyar mashigar da aka yi.

    Jirgin Nord Luxury mai tsawon mita 142, da ke da alaƙa da hamshaƙin mai kuɗin nan da aka sanya wa takunkumai Alexey Mordashov, ya yi tafiya ne zuwa Muscat da ke Oman daga Dubai a ƙarshen mako, kuma ya kasance ɗaya daga cikin jiragen ruwa waɗanda ba na gwamnati ba ko kasuwanci da ya bi ta mashigar a cikin ƴan watannin nan.

    Iran ta yi wata ganawa mai muhimmanci da Rasha a cikin makon nan, a yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana tsakaninta da Amurka kan sake buɗe Mashigar Hormuz.

    A ƙiyashi kashi ɗaya cikin biyar da ɗanyan mai da iskar gas da ake amfani da shi a duniya ne ke wucewa ta Mashigar.

  5. Ukraine na zargin Isra'ila da sayen ''hatsin sata'' daga yankunanta da Rasha ta mamaye

    Ukraine ta gayyaci jakadan Isra'ila a ƙasar, bayan da Kyiv ta zargi Isra'ilar da sayen abin da ta kira hatsin sata daga yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye.

    Ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Sybiha ya ce irin wannan sayayya na kawo cikas ga alaƙa mai kyau da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    Ya ce jirgin ruwan dakon kaya na biyu ya isa Haifa, bayan na farkon ya kai hatsi yakin.

    Ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Sa'ar ya ce za a gudanar da bincike kan lamarin.

    Sai dai kuma ya yi gargaɗin cewa zargi ba shaida bane, inda ya ja hankalinsu kan gudanar da hulɗar diflomasiyya ta intanet ko kafafen yaɗa labarai.

  6. Dukkan jagororin Iran masu tsattsauran ra'ayi ne - Rubio

    A wata hira da ya yi da kafar talibijin ta Fox News, Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi ƙarin bayani game da halin da ake ciki a Iran, da kuma tsaikon da Amurka ke samu wajen cimma yarjejeniya da gwamnatin ƙasar.

    A tattauwnawar ta sa, Rubio ya bayyana jagororin Iran da cewa ‘’ Dukkaninsu masu tsatsauran ra’ayi ne, Amma akwai masu tsatsauran ra’ayin da sun san cewa dole za su tafiyar da alamuran kasa kuma dole su tabbatar tattalin arzikin kasar na tafiya yadda ya kamata. Sai dai addini ne abin da suka fi mayar da hankali kai''.

    Sai dai a cewarsa ‘abin takaici, ana iya cewa masu tsatsauran ra’ayi waɗanda ba sa ma duniya fatan alkhairi ne ke rike da wuyar kasar’’.

    Rubio ya kuma ce masu tsautsauran ra’ayin addinin ba wai kawai dakarun juyin juya halin Iran bane, har ma da shugaban Iran ɗin da majalisar sa.

    Ya kuma kara da cewa mutane kamar Fira ministan kasar da Shugaban ƙasar da Shugaban majalisa duk masu tsatsauran ra’ayi ne, amma kuma sun san cewa dole ne ƙasar ta samu tattalin arziki mai inganci, kuma dole ne yan ƙasar su ci abinci.

  7. Ƙungiyar ISIS ta ɗauki alhakin harin da ya hallaka mutum aƙalla 30 a jihar Adamawa

    Wasu ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutane ashirin da tara a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun shiga wani filin wasan ƙwallon ƙafa ne inda jama’a ke taruwa, kana suka buɗe wuta kan mai uwa-da-wabi.

    Ofishin gwamnan jihar ya ce maharan sun shafe sa’o’i da dama suna harbin jama'a da ƙona gidaje, da babura da wuraren ibada.

    A shekarun baya-bayan nan, yankin ya sha fama da hare-hare daga kungiyoyin ‘yan daba na cikin gida da kuma masu alaka da ISIS.

    Wata sanarwa da kungiyar ta ISIS ta wallafa a shafinta, ta dauki alhakin kai harin.

    Rahotanni na cewa an tura jami’an soji da ƴan sanda zuwa yankin domin daƙile yiwuwar sake kai wani harin.

  8. Ana tuhumar mutumin da ya yi harbi a taron cin abinci da yunƙurin kashe Trump

    Mutumin nan da ake tuhuma da yunƙurin kashe shugaban Amurka Donald Trump a wajen wata liyafar cin abincin dare ta masu aiko da rahotanni daga fadar White House ya gurfana a gaban kotu.

    Ana zargin Cole Thomas mai shekara 31 a duniya da kutsawa cikin taron a ranar Asabar, ɗauke da bindigogi da wukake.

    Taron, wanda aka gudanar a otal din Washington Hilton, ya samu halartar shugaban ƙasar da manyan jami’an gwamnatinsa.

    Wakilin BBC ya ce bayanan kotu sun nuna cewa mutumin ya kama ɗaki ne a Otal ɗin bayan ya taso tun daga birnin Los Angeles a jirgin ƙasa a makon da ya gabata.

    Ana sa ran wanda ake zargin zai sake gurfana a gaban kotu ranar Alhamis domin sauraron batun tsare shi.

    Yana iya fuskantar daurin rai da rai idan aka same shi da laifi.

  9. Ana ci gaba da aikin ceto bayan jiragen ƙasa biyu sun yi taho mu gama a Indonesia

    Masu aikin ceto a Indonesia na can na ta ƙokarin ceto waɗanda ke da sauran numfashi, bayan wani mummunan hatsarin jiragen kasa a kusa da babban birnin kasar, Jakarta.

    Adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa goma sha hudu, yayin da aƙalla mutane tamanin suka jikkata lokacin da jiragen suka yi taho mu gama a kusa da tashar Bekasi Timur.

    Hatsarin ya auku ne lokacin da wani jirgin ƙasa da ya yo tafiya mai nisa ya sauka daga layinsa, kana ya yi karo da wani jirgin kasa na fasinja da ke tsaye, bayan wata mota kirar tasi ta toshe masa hanya.

    Tsarin sufurin jiragen kasa da na motocin bas dai na cike da cikas a Indonesia, abun da ke yawan haifar da haɗurra.

  10. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu a shafinmu na BBC hausa kai tsaye barkanmu da safiyar yau Talata.

    Kamar dai yadda aka saba wannan shafi ne da zai kawo muku labarai na abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, da Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance tare da mu, kuma za ku bibiye mu a shafukan mu na sada zumunta kamar Facebook, X, Instagram da kuma YouTube domin kallon bidiyo da tafka muhawara.