Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko jam'iyyun hamayyar Najeriya za su iya tsayar da ɗan takara ɗaya?
A daidai lokacin da jam'iyyun hamayya a Najeriya suke ƙoƙarin ɗinkewa domin fitar da ɗantakara ɗaya da zai fafata da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a babban zaɓen ƙasar da ke tafe, hankali ne ya fara komawa kan wanda zai yi takara ya samu amincewar sauran.
A makon jiya ne a Najeriya jam'iyyun hamayyar ƙasar suka gudanar da wani taron gangami a birnin Badun na jihar Oyo domin samar da matsaya kan yadda za su fuskanci zaɓen.
A taron ne PDP da ADC, da Labour da NNPP suka bayyana cewa zai yi wahalar gaske a iya kayar da shugaba Tinubu idan ba sun haɗa ƙarfi da ƙarfe ba domin yi masa taron dangi su fuskance shi.
Kusan duk wani jigon hamayya a ƙasar ya halarci taron, kamar tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi da Aminu Waziri Tambuwal.
Sai kuma mai masaukin baƙi, Gwamna Seyi Makinde da shugaban wani tsagi na PDP, Tanimu Kabiru Turaki da wasu jiga-jigan jam'iyyu daban-daban da sauran masu ruwa da tsaki.
Babban abin da ya fito daga taron shi ne amincewar da ƴan hamayyar suka yi ta tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya, sai su haɗu su mara masa baya ya gwabza da Tinubu.
Jam'iyyun da suka shiga haɗakar
Daga cikin manyan jam'iyyun da suka halarci taron sun haɗa da;
- ADC
- PDP
- Labour
- NNPP
- PRP
- Accord
- APM
- YP
- ADP
Haɗakar za ta yiwu?
A game da ko haɗakar jam'iyyun hamayyar za ta yiwu domin fuskantar Tinubu, Dr Kabiru Sufi, mai sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya, ya ce akwai sauran aiki ja a gaban jagororin.
"Sun dai yi alƙawari, amma tabbatar da lamarin ne ake jinjinawa. Bayan haka kuma bayan an tabbatar da ɗantakara, akwai fargabar ko duk za su iya haƙura su mara masa baya," in ji shi.
Sufi ya ce ƙalubale ne babba domin a cewarsa, wani ɗantakarar ba shi ba ne matsalar, inda ya ƙara da cewa wasu magoya bayansu ne za su iya yin tasiri wajen samun cikakkiyar haɗaka.
Sai dai masanin siyasa ya ƙara da cewa matuƙar ƴan hamayya suna da burin kayar da Tinubu, lallai suna buƙatar haɗin kai.
"Alƙalumam zaɓen da ya gabata ya nuna cewa idan ba haɗa kai aka yi ba, nasara za ta yi wahala, musamman ganin yadda APC ke ƙara janyewa tare da gwamnoni," in ji shi.
A ƙarshe ya shawarci jam'iyyun hamayyar su jajirce, sannan su yi haƙuri da duk abin da ya biyo bayan fitar da ɗantakararsu.
2027 kamar 2015?
A zaɓen shekarar 2015, an yi shigen haka, inda manyan ƴan hamayya suka haɗu a inuwar jam'iyyar APC domin tunkarar jam'iyyar PDP mai mulki a lokacin.
A zaɓen ƴan hamayya, ciki har da shugaban na yanzu Bola Tinubu da Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso suka haɗu, suka fuskanci PDP, har Marigayi Muhammadu Buhari ya samu nasarar kayar da Goodluck Jonathan.
Sai dai wani abu da ya bambanta wancan haɗakar da ta yanzu shi ne yadda a wannan karon, jam'iyya mai mulki ta samu ƙarin gwamnoni da dama da sanatoci da ƙarin jiga-jigai a daidai lokacin da maganar zaɓen ta ƙara kankama.
A wancan lokacin kuwa, a daidai lokacin da shirye-shiryen zaɓen ke kankama, wasu gwamnoni biyar ne daga jam'iyya mai mulki suka bayyana cewa ba sa tare da shugaban, ciki har da Kwankwaso da Amaechi kuma jihohin su na Kano da Rivers na da ɗimbin ƙuri'u.
Sai dai a zantawarsa da BBC, Atiku Abubakar ya ce ba gwamnonin ba ne suka zaɓe, domin a cewarsa mutane ne za su yi zaɓe.
Haka kuma a game da haɗakar, masanin harkokin siyasa a Najeriya, Dr Kabiru Sufi ya ce duk da cewa haɗakar ta 2027 na kamanceceniya da haɗakar 2015, amma akwai bambanci.
"A zaɓen 2015, jam'iyyun sun haɗu ne suka sadaukar da rajistarsu, suka narke a APC. Amma yanzu kuwa jam'iyyun suna nan, kawai sun amince su yi aiki ne a tare a babban zaɓen," in ji shi.
Masu neman takara a jam'iyyun haɗaka
Daga cikin lissafin takarar da ake yi a jam'iyyar ADC ko kuma jam'iyyar da ƴan hamayyar za su fitar da ɗantakara guda ɗaya akwai waɗanda suka fi ƙarfi kamar haka:
- Atiku da Obi
- Obi da Kwankwaso
- Atiku da Makinde
- Atiku da Amaechi
Ƙalubalen da ke gaban ƴan hamayya
A watan Afrilun 2025 ne wasu jiga-jigan ƴansiyasa a Najeriya suka amince da African Democratic Congress (ADC) a matsayin jama'iyyar da za su ƙulla ƙawancen haɗaka a cikinta.
Ƴansiyasar sun ce sun amince da ADC ne da nufin haɗa ƙarfi da ƙarfe a cikinta da nufin kawar da jam'iyyar APC daga mulkin Najeriya a zaɓen 2027.
An cimma ƙawancen ne a taron haɗakar da aka gudanar ranar Laraba 2 ga watan Yulin bara a babban ɗakin taro na Ƴar'adua Centre da ke birnin Abuja.
Sabuwar haɗakar ta ADC ta zaɓi Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar, wadda suka amince da ita a matsayin jam'iyyar haɗaka.
Sai dai yanzu haka jam'iyyar na fama da rikicin cikin gida, lamarin da yanzu haka ake jiran Kotun Ƙolin ƙasar ta warware.
Tuni dai Nafiu Bala Gombe, wanda tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ne ya bayyana cewa shi ne halastaccen shugabanta bayan tsohon shugaban ya yi murabus, a yayin da a gefe guda kuma David Mark ke cewa shi ne shugaba.
Ita kuma PDP yanzu haka INEC ta fi mu'amala da tsagin Wike, inda tsagin Tanimu Kabiru Turaki ya bayyana aniyarsa ta samun maslaha da ADC wajen tsayar da ɗantakara.
Sai dai kuma masanan na ganin akwai sauran rina a kaba idan har jiga-jigan yan hamayyar na Najeriya suka kasa haɗa kansu domin mara wa ɗayansu baya kan manufar zaɓen 2027 da ta haɗa su.