Mutum 6 da gwamnatin Najeriya ta zarga da tallafa wa ta'addanci

Mayaƙan ISWAP

Asalin hoton, AFP

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Gwamnatin Najeriya ta bayana sunayen wasu mutum shida da kamfanonin canji uku da take zargi da tallafa wa ayyukan ta'adanci a ƙasar.

Matakin na zuwa ne kwanaki bayan da Amurka ta bayyana sunan wani mutum mazaunin Legas, mai sana'ar musayar kuɗaɗen waje a matsayin wanda take zargi da tallafa wa ayyukan ta'addanci a ƙasar.

Najeriya ta jima tana fama da ƙungiyoyin ta'addanci masu alaƙa da ƙasashen waje, lamarin da ya sa ake zargin wasu daga ciki da wajen ƙasar da tallafa wa ayyukan ƴanbindigar ta hanyar taimaka musu da hada-haɗar kuɗi da safarar makamai.

Wannan ya sa gwamnatin ƙasar ta duƙufa domin gano mutanen da ke taimaka wa waɗannan ƙungiyoyin ta hanyar taimaka musu da kuɗaɗe ko wasu kayan aiki.

Kan haka ne gwamnatin ƙasar ta fitar da sunayen mutum shida da tace tana zargi da ɗaukar nauyin ta'addanci a ƙasar bayan ɗaukar lokaci tana bincike a kansu.

Su wane ne mutanen?

Kwamitin sanya takunkumai na ƙasar, ƙarƙashin jagorancin shugabar kwamitin, Beatrice Jedy-Agba, ya fitar da sunayen ne bayan tantancewa ta hanyar hukumomin tattara bayanan sirri.

"Mun fitar da sunayen ne bayan tattara bayanan sirri, da binciken hada-hadar kuɗi da tantance bayanai tsakanin hukumomi, waɗanda suka tabbatar da hujjojin zarge-zargen da muke da su a kansu'', kamar yadda ta bayyana.

Mutanen da ake zargi sun haɗa da:

  • Mukhtar Muhammad Adamu
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mazauni birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, da ake zargi da taimaka wa ayyukan ƙungiyar ISWAP reshen Okene, ta hanyar yi wa ƙungiyar hada-hadar kuɗi da kamfaninsa na canji.

An zarge shi da tura wasu kuɗin da suka kai kimanin naira miliyan uku zuwa wani asusu da ake zargi na wani mutum ne ɗan ISWAP a 2023.

A ranar Laraba ne Amurka ta bayyana sunansa a matsayin wanda ke taimaka wa ta'addanci a Najeriya.

  • Ibrahim Yakubu Ogirima

Gwamnati ta zargi mutumin da bayar da kayan aiki da tallafin kuɗi da mayaƙan ISWAP na yankin Kogi.

An zarge shi da aiki da umarnin shugabancin ISWAP, wajen karɓa tare da rarraba kuɗi da iyalan mambobin ISWAP da suka mutu, wanda hakan ke taimakawa wajen ci gaba da wanzuwar ayyukan ƙungiyar.

  • Adamu Chiroma

Yana fuskantar zargin hannu a tallafa wa ta'addanci ta hanyar amfani da kamfanonin musayar kuɗaɗensa na waje zuwa wasu mutane masu alaƙa da ISWAP.

Gwamnatin ta ce bincikenta ya zargi Chiroma da amfani da kamfanonin canji wajen tura kuɗaɗe zuwa asusun wasu mutane masu alaƙa da ƙungiyar ISWAP ta yankin Okene.

  • Ibrahim Abubakar

An zarge shi da hannu a ɗaukar nauyin ta'addanci da kuma kasancewa mamba a ƙungiyar ta ISWAP.

Gwamnatin ta ce bincikenta ya gano cewa Ibrahim ya taɓa zama sansanin ISWAP na yankin Tafkin Chadi tsakanin 2015 zuwa 2017.

Binciken ya kuma gano cewa yan taimakawa wajen tura kuɗi ga manyan mambobin ISWAP da mutanen da suka yi fice wajen ɗaukar nauyin ƙungiyar.

Motar ISWAP

Asalin hoton, Getty Images

  • Abdullahi Umar Usman

Ana zarginsa da samar wa ISWAP rashen Okene tallafin kuɗi. Binciken gwamnati ya gano cewa yana amfani da kamfanin musayar kuɗinsa da aka yi wa rajista a Kano wajen tura kuɗaɗe ga mambobin ISWAP.

Bayanan hada-hadar kuɗi sun nuna yadda ya tura kuɗi har naira miliyan 3.5 zuwa asusun bankin Abdulkareem Abdulsamad Ohida, ɗaya daga cikin manyan mambobin ƙungiyar ISWAP reshen Okene.

  • Babangida Muhammed Adamu Hammajam

Mutum na ƙarshe cikin jerin sunayen da gwamnatin Najeriya ta fitar a baya-bayan nan, ana zarginsa da hannu wajen hada-hadar kuɗaɗen da ƙungiyar ke gudanar da ayyukanta.

Ana kuma zarginsa samar da kuɗi da amfani da su wajen saya wa ISWAP abubuwan da take buƙata ciki har da sayen na'urar intanet ta Starlink domin bunƙasa sadarwa da ayyukan ƙungiyar.

An kuma zarge shi da alaƙa da Abdulhamid Muazu, tsohon kakakin Boko-Haram da ya koma ISWAP daga baya.

  • Sauran kamfanonin canji uku da aka zarga
  • Abbal Bako & Sons Bureau De Change Limited.
  • Nine to Nine BDC.
  • Generation BDC Limited.

Me ya sa ake yawan zargin ƴan canji da taimaka wa ta'addanci?

Ba wannan ne karon farko da aka kama ƴan canji da wasu kamfanonin canji bisa zargin tallafa wa ta'addanci a Najeriya ba.

Lamarin da ya sa wasu ƴanƙasar ke mamakin yadda ake zargin ƴan canjin da hannu a ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a ƙasar.

To sai dai Dr. Kabiru Adamu masanin harkokin tsaro a yankin Sahel ya ce wannan ba abin mamaki ba ne, la'akari da cewa kowace sana'a a kwai bara-gurbi.

''Akwai wasu bara-gurbi a cikinsu waɗanda ke ganin kamar ba a sanya idanu a ayyukansu, kasada ce wadda kusan a iya cewa gwamnati ta fahimce ta, tana kuma ƙoƙarin maganceta'', in ji masanin tsaro.

Martanin ƴan canjin

Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar masu canjin kuɗaɗen waje ta Najeriya, ABCON ta yi Allah wadai da dukkan ayyukan ta'addanci da na masu tallafa musu.

Cikin wata sanar da ƙungiyar ta fitar, ta jaddada cewa takunkuman da gwamnati ta sanya wa waɗancan kamfanoni ya shafi ɗaiɗaikun mutane da kamfanonin da aka ambata ne, ba duka mambobi da kamfanonin ƙungiyar ba.

ABCON ta kuma ce za ta ɗauki matakan daƙile amfani da harkar canjin kuɗin waje domin tallafa wa ta'addanci.

Ƙungiyar ta ce za ta riƙa amfani da wasu dabaru da suka haɗa da sanin abokin ciniki kafin tura masa ko canja masa kuɗi.

Da kuma kai rahoton musayar kuɗin da ba a yarda da shi ba, da shirya tarukan ƙara wa juna sani da kuma bai wa hukumomin gwamnati haɗin kai.