Ƴan sanda sun rufe wasu muhimman tituna a Nairobi yayin da ake shirin fuskantar zanga-zangar Gen Z a Kenya

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Ƴan sanda a Kenya sun rufe wasu muhimman titunanan da ke shiga tsakiyar birnin Nairobi gabanin zagayowar cika shekara biyu da gudanar da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka yi a ƙasar ƙarkashin jagorancin ƙungiyar Gen-Z.
Dubban ƴan ƙasar Kenya ne suka yi zanga-zangar nuna adawa da shirin ƙara harajin da aka yi a watan Yunin 2024, wanda ya kai ga yin kutse a fadar majalisar dokokin ƙasar, daga bisani kuma aka janye ƙudirin dokar kudin da ya janyo cece-kuce.
Masu zanga-zangar sun ce suna neman a yi hukunci kan fiye da mutane 80 da aka kashe tare da jikkata wasu da dama yayin zanga-zangar ta 2024 da kuma zanga-zangar tunawa da ranar da aka yi a bara.
Mutane da dama sun maƙale a kan hanya da safiyar ranar Alhamis bayan da jami’an tsaro suka tare hanyar shiga tsakiyar birnin, yayin da aka rufe kasuwanni da makarantu da dama.
Ana sa ran za a gudanar da zanga-zangar da aka tsara a kan shafukan sada zumunta na intanet a manyan garuruwan da suka haɗa da Nairobi da Mombasa da kuma wasu sassan tsakiyar ƙasar Kenya.


