Su wane ne masu ɗaukar nauyin ta'adanci a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Mahukunta a Najeriya sun fitar da sunayen mutum 48 da kamfanoni 12 da suke zargi da ɗaukar mnauyin ta'addanci a ƙasar.
Jerin sunayen da aka fitar a ranar Juma'a bai bayar da cikakken bayani kan mutanen da ake zargin ba. Babu cikakken bayanin ƙasashen su ko girman laifin da aka same su da shi, ko kuma sunan ƙungiyoyin da ake zargin suna ɗaukar nauyi. Haka nan kuma mahukuntan ba su bayar da cikakken bayani kamar jinsi ko hotunan mutanen da ake zargi ba.
A baya dai Najeriya ta sanar da matakin ladabtarwa kan wasu mutanen da kamfanoni, kamar yadda kwamitin tsaro na majalisar Dinkin Duniya ya gindaya, kuma cikin matakin da aka ɗauka harda na rufe asusun ajiyar su da kuma taƙaita tafiye-tafiye gare su.
Ƙasar ta kafa wani kwamiti mai alhakin zartar da matakin ladabtarwa wanda zai taimaka wajen aiwatar da tanadin dokokin Majalisa Dinkin Duniya a kan ayyukan ta'addanci. Kwamitin na zartar da takunkumi da sauran matakan ladabtarwa da nufin daƙile hanyoyin samun kudi ga mutane ko ƙungiyoyi da ke da alaƙa da ayyukan ta'addanci da safara makamai. Matakin kwamitin na aiki a kan duk wani mutum ko hukuma ko kuma ƙungiya da ke ayyukanta a cikin Najeriya.
Sanarwar masu ɗaukar nauyin ta'addancin na zuwa ne bayan da a makon nan mahukunta a Najeriya suka gurfanar da mutane fiye da 500 da ake zargi da laifin ta'addanci, alƙalumma mafi yawa a tarihin ƙasar. Kawo yanzu an yankewa 386 a cikin su hukunci kan laifukan ta'addanci.
Waɗanda aka gurfanar na fuskatar zarge-zarge nasu alaƙa da tallafawa ta'addanci da ɗaukar nauyin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai musamman a yankin arewa maso gabas, inda ƙungiyoyi masu tayar da ƙayar baya irin su Boko Haram ke gudanar da ayyukan su fiye da shekaru goma da suka gabata.
Tun bayan ɓullar Boko Haram a yankin, tashin hankali ya watsu a sassan ƙasar, inda ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ke kai hare-hare da garkuwa da mutanen don neman kudin fansa a sassan Najeriya.
Kwannan nan gwamnatin ƙasar ta ayyana ƙungiyoyin ƴanbindiga a matsayin ƙungiyoyin ƴan ta'ada, wani lamari da ya faɗaɗa aikin yaƙi da ta'addanci a ƙasar.
Duk da munin hare-haren da suke kai wa, ba a cika ganin an gurfanar da waɗanda ake zargib a gana ƙuliya ba. Mafi yawa ana tsare su ne na tsawon lokaci ba tare da shari'a ba, lamarin da ke janyo damuwa game da rashin bin ƙa'idar doka wajen hukunta masu laifi.
Ƙungiyoyi irin su Boko Haram da Islamic State West Africa Province (Iswap) da kuma Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) na gudanar da ayyukan su a sassan Arewacin Najeriya, wani abu da ke ƙara ruruta wutar rashin kwanciyar hankali a ynlin.
Haka nan kuma a ƴan watannin nan matsalar rashin tsaro ta yaɗu ha zuwa wuraren da a baya basu da wannan masalar, yayin da mahukunta ke cewa suna ƙoƙarin daƙile ta.
A makon nan ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta gargaɗi ƴan ƙasarta game da shiga Najeriya, tana mai kafa hujja da ƙaruwar ayyukan ta'adanci da gankuwa da mutane da kuma sauran rikce-rikice.
Mutum 2,360 aka kashe a Najeriya a wata ukun farkon 2026 - Rahoto

Asalin hoton, ADABKA
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kamfanin Beacon Security mai nazarin matsalolin tsaro a yankin Sahel ya ce an ƙara samun taɓarɓarewar al'amuran tsaro a Najeriya cikin watanni uku farkon 2026.
Cikin rahoton wata-wata da kamfanin ke fitarwa ya ce duk da matakan da jami'an tsaron ƙasar ke ɗauka har yanzu matsalar ba ta sauya ba.
Rahoton na Beacon Security ya ce mutum 2,360 aka kashe a Najeriya cikin watanni ukun farkon shekarar 2026 da muke ciki.
Najeriya dai ta jima tana fama da matsalolin tsaro, inda ƴanbindiga a sassan ƙasaer da dama ke kai hare-hare da kashe mutane tare da kama wasu domin neman kuɗin fansa.
Ƙungiyoyin ƴanbindiga irin su Boko Haram da ISWAP da ƴan fashin daji ne ke yawaitar kai hare-hare.
Rahoton ya nuna cewa yankin arewa maso gabashin Najeriya ne kan gaba a samun kashe -kashen cikin wata ukun farkon wannan shekara.
Beacon Security ya ce mutum 801 aka kashe a yankin cikin watannin uku.
Yankin na arewa maso gabashin Najeriya ya yi ƙaurin suna a ayyukan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadim Boko Haram da ISWAP.
A cikin wannan shekara kaɗai an samu manyan hare-haren da waɗannan ƙungiyoyi suka ƙaddamar kan sojoji da fararen hula, ciki har da wanda suka kai garin Ngoshe a cikin watan Maris.
Baya da Yankin arewa maso gabas, yankin da ya biyo baya a samun kashe-kashen shi ne Arewa ta Tsakiyar ƙasar mai fama da rikicin ƙabilanci da na manoma da makiyaya, inda rahoton ya ce an kashe mutum 762.
Yankin arewa maso yammcin ƙasar - mai fama da matsalar hare-haren ƴan fashin daje masu garkuwa da mutane - ne ya zo na uku a samun kashe-kashen, wanda aka kashe mutum 508,
Sai kuma kudu maso gabashi, inda aka kashe mutum 157, da kudu maso kudu mai mutum 64, sai kuma kudu maso gabas da aka kashe mutum 58 cikin watanni ukun farkon 2026.










