Arsenal na harin Rogers, PSG da Liverpool na gogayya kan Diomande

Asalin hoton, Getty Images
A shirye Arsenal take ta kara azama wajen nuna sha'awarta ta sayen danwasan gaba na Aston Villa da Ingila Morgan Rogers, mai shekara 23. (Talksport)
Aston Villa, da AC Milan, da kuma Besiktas na matukar son dan bayan Liverpool da Ingila Joe Gomez, mai shekara 29. (Mail)
Liverpool da Paris St-Germain na tattaunawa da danwasan gaba na gefe na RB Leipzig da Ivory Coast Yan Diomande, mai shekara 19. (Fabrizio Romano)
Kociyan Tottenham Roberto de Zerbi na harin 'yanwasa uku daga tsohuwar kungiyarsa Brighton - danwasan tsakiya na Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 22, da dan baya Jan Paul van Hecke, dan Netherlands mai shekara 25, da kuma mai tsaron ragar Ntherlands din Bart Verbruggen, mai shekara 23 - bugu da kari Tottenham din na duba yuwuwar sayen dan bayan Ingila John Stones, mai shekara 31. (Independent)
Danwasan gaba na gefe na Ingila da Newcastle Anthony Gordon, mai shekara 25, ya dauki hankalin shugabannin Barcelona, kuma a kan hakan ana ganin kila zakarun na Sifaniya su nemi sayenshi a bazara. (AS)
Enzo Maresca, wanda ake cewa zai maye gurbin Pep Guardiola a Manchester City, na son bai wa danwasan tsakiya na Ingila Jack Grealish, mai shekara 30, damar ya farfado da wasansa a City bayan zaman aro da ya yi a Everton. (Mirror)
Brentford ta gabatar da tayin yuro miliyan 45 (£39m) a kan dan wasan gaba na gefe na kungiyar Cologne ta Jamus Said El Mala, mai shekara 19. (Sky Sport)
Cologne na son sayen dan bayan Leeds Sebastiaan Bornauw, dan Belgium mai shekara 27. (Bild)
Everton na harin sayen dan bayan Jamhuriyar Dumukuradiyar Kongo Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 28, a kan fam miliyan 10, bayan da West Ham ta fadi daga gasar Firmiya. (Telegraph)
Haka kuma Tottenham, da Newcastle United, da Fulham, da Sunderland duk suna son Wan-Bissaka. (Team Talk)
Sabon kociyan da zai kama aiki a Real Madrid Jose Mourinho ya gabatar wa da kungiyar jerin wuraren da yake son ya karfafa a tawagar, yayin da yake shirin nade tabarmarsa a Benfica ya koma Bernabeu. (AS)














