Ƴanwasan da za su buga gasar kofin duniya ta ƙarshe a 2026

World Cup

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 11

Daf ake a fara gasar cin kofin duniya da aka sauya mata fasali da tazawa 48 za ta kece raini a Amurka da Canada da kuma Mexico.

Kawo yanzu an samnu dukkan kasashen da za su buga wasannin, har da waɗanda a karon farko za su buga babbar gasar tamaula ta duniya a tarihi.

Wannan gasar za a yi tata ɓurza ganin tawagogin suna da yawa, an kara yawan wasanni da filaye da jami'an da za su gudanar da gasar ta 2026.

Argentina ce mai rike da kofin da ta ɗauka a 2022 a Qatar, kenan Messi zai yi fatan kare kofin daga nan ya rataye takalmansa.

Wasannin bana za a samu matasan da za su nuna kansu da kuma waɗanda tsuka yi tsufan da wannan ce gasar da za su halarta ta karshe.

Ga jerin wasu ƴan wasan da za su buga gasar karshe a cin kofin duniya a 2026.

Nahiyar Turai: Cristaino Ronaldo da Luca Modric da Kevin De Bruyne da Dani Carvajal da Virgil van Dijk da Granit Xhaka da kuma Eden Dzeko.

Nahiyar Kudancin Amurka: Lionel Messi daNeymar da James Rodriguez da Luis Suarez

Africa: Mohamed Salah da Sadio Mane da Kalidou Koulibaly da Riyad Mahrez da kuma Vozinha.

Nahiyar Asia: Son Heung-Min da kuma Wataru Endo.

Nahiyar Oceania: Chris Wood

Cristiano Ronaldo (Portugal)

Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Cristiano Ronaldo shi ne mutum na farko da ya ci ƙwallo a gasar FIFA World Cup guda biyar daban-daban ya nuna irin daɗewar da wannan fitaccen ɗan wasan da irin wannan bajintar da ya yi.

Duk da kalubalen da ya fuskanta a gasar 2022 da ta kai an yi waje da su a zagayen kwata fainal, har yahna yana nuna kwazo duk da yawan shekarunsa.

Idan ya kai ga buga gasar 2026, tauraron Al-Nassr FC zai shiga gasar yana da shekara 41, wanda hakan zai zama tarihi na bayyana a kofin duniya karo na shida.

Lashe babbar kofin duniya ne ya rage masa a kundin nasarorinsa, kenan damar da yake da ita a bana kenan, daga nan zai hakura da ziyartar gasar cin kofin duniya.

Luka Modric (Croatia)

Bayan da ya ja ragamar kasarsa mai mutane miliyan huɗu zuwa wasan karshe da kuma matsayi na uku a gasar FIFA World Cup biyu a jere a shekarar 2018 da 2022, wani babban abin tarihi ne da ya saka, wanda yake da gogewa.

Luka Modric ya zama ginshikin nasarorin Croatia tun bayan da ya fara buga mata tamaula a duniya shekara 20 da suka gabata a gasar da aka gudanar a Jamus.

Zai shiga gasar 2026 yana da shekaru 40, watakila gasa ta karshe a rayuwarsa, wanda ya lashe ƙyautar Golden Ball a gasar kofin duniya ta 2018 a Rasha.

Kevin De Bruyne (Belgium)

Ga Kevin De Bruyne, rashin kaiwa wasan karshe a gasar 2018 FIFA World Cup tare da Belgium har yanzu yana daga cikin abubuwan da ke damun ɗan wasan da ya yi fice a gasar Premier League a lokacin kololuwar wasansa.

Cika shekaru 35 yayin gasar kofin duniya ta 2026 na nufin ɗan wasan Napoli zai iya kasancewa ya jagoranci kasar karo na karshe a babbar gasar tamaula ta duniya.

Dani Carvajal (Sifaniya)

Duk da cewa ɗan wasan mai shekara 34 na fama da rauni ana shakku ko zai iya buga wasannin bana kuwa? Dani Carvajal gogagge ne a jagorancin Sifaniya yayin da take neman karin wata babbar nasara a matakin duniya.

Lashe kofin Champions League da dama tare da Real Madrid bai kai ga ya samu nasara a gasar FIFA World Cup ba a rayuwarsa ta kasa da kasa.

Saboda yawan shekarunsa da kuma yawan fama da rauni — watakila wannan ce gasar kofin duniya ta karsheda mai tsaron bayan Real Madrid zai halarta.

Virgil van Dijk (Netherlands)

Ƙyaftin ɗin tawagar Netherlands ya ja ragamar kasar zuwa matakin kwata-fainal a gasar 2022 FIFA World Cup.

Virgil van Dijk mai shekaru 34 yana matukar son ganin kasarsa ta yi wani abu a gasar da za a buga a Arewacin Amurka, kuma zai jagoranci matasan tawagar Netherlands zuwa lashe kofin bana da ɗan wasan Liverpool ke fatan halartar gasar kofin duniya ta karshe.

Granit Xhaka (Switzerland)

Ƙwazon da Switzerland ke nunawa a manyan gasa ta duniya ya haɗa daga jagoranci da kuma kwarewar Xhaka da kyaftin din tawagar da ya dade yana yi wa kasar.

Ya halarci gasar FIFA World Cup sau uku a baya, hakan wata alama ce da ke nuna cewa gasar karshe da zai halarta kenan, wanda ke fama da jinya.

Wannan gasar ta 2026 yana da shekara 33, yayin da mai taka leda a Sunderland ke fama jinya, watkila jikin ne ya gaji, ya kamata ya rataye takalmansa da zarar an kammala gasar kofin duniya.

Edin Dzeko (Bosnia and Herzegovina)

Bayan rawar da ya taka da ta kai sun yi waje da Italy a wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya a watan Maris, magoya bayan Bosnia and Herzegovina na kallon fitaccen mai cin kwallon a matsayin jagoran dawo da kasar zuwa babban matakin duniya fiye da shekara goma bayan bayyanarsu ta farko a 2014.

Yawan cin kwallayen da ya yi a manyan lig-lig a Turai bai rage kishin wannan gwarzon mai shekaru 40 ba, wanda aka saka shi cikin jerin ƴan wasa 26 da za su halarci gasar 2026 FIFA World Cup a ranar 11 ga watan Mayu.

Jagorantar kasarsa a matsayin kyaftin a 2026 zai zama cikakken bankwana a tarihi Edin Dzeko a fannin taka leda, ɗan wasan da ya zama alamar kwallon kafar Bosnia.

Lionel Messi Argentina

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Lashe gasar 2022 FIFA World Cup a kasar Qatar da Messi ya yi, ta tabbatar da matsayin shi a matsayin ɗaya daga cikin mafi girman ƴan wasan kwallon kafa da duniya ta taɓa gani a wannan lokacin.

Ɗaukar kofin duniya da Messi ya yi abin kamar al'amara bayan da tawagar ta fara da rashin nasara, daga baya ta kai ga lashe kofin, wanda ya fara zuwa gasar kofin duniya a 2006 tun yana matashi.

Duk da cewa ana tsammanin zai yi ritaya bayan gasar 2022, sai kawai ya ci gaba da kasancewarsa cikin tawagar Argentina yana da shekaru 38, amma ana hasashen cewar gasar 2026 za ta iya zama ta karshe da zai wakilci kasarsa a tarihi.

Jan ragamar Argentina zuwa gasar da za a buga a Arewacin Amurka zai bai wa tauraron Inter Miami CF damar yin bankwana da ƙwallon kafa a kasar da yanzu take matsayin gidansa na wasanni wato Amurka.

Neymar (Brazil)

Neymar

Asalin hoton, Getty Images

Babu tabbaci cewa Neymar zai buga gasar 2026 FIFA World Cup, amma kasancewarsa cikin jerin ƴan wasa 55 na wucin gadi da Carlo Ancelotti ya fitar ya ba da fata cewa zai sake bayyana a babban matakin gasar tamaula ta duniya karo na karshe.

Yawaitar raunuka sau da yawa ya hana ɗan wasan gaba na Santos FC nuna cikakken tasirinsa a lokutan da tawagar Selecao ta fi bukatar hakan a matakan karshe na gasar.

A baya Neymar ya taɓa bayyana cewa gasar 2022 za ta iya zama ta karshe a gare shi, amma burin lashe kofin duniya na shida da Brazil ke fata, mai shekaru 34 ya sake yin yunkuri na karshe, domin a kafa wannan tarihin tare da shi.

Kenan zai so ya gyara kurakuren da ya tafka da samun lashe kofin duniya, domin a ci gaba da tunawa da shi a fannin taka leda a duniya.

James Rodriguez (Colombia)

Yayin da ƴan wasa da dama suke nuna kansu a gasar kofin duniya, James Rodriguez mai shekara 34 ya kafa tarihin da har yanzu ana hangen abin da ya yi a 2014.

A lokacin yana da shekaru 24, dan wasan na Colombia ya jagoranci kasarsa zuwa matakin kwata-fainal, inda ya ci kwallaye shida da lashe kyautar Golden Boot.

Ɗaya daga cikin kwallayen da ya ci na ban mamaki har da wata da ya yi vole da ya ci Uruguay a zagayen ƴan 16, wanda har yanzu ake ɗauka a matsayin ɗaya daga cikin mafi ƙyawun kwallaye da aka zura a raga na ban mamaki a tarihin kofin duniya.

Wannan gasa za ta kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka kasance a rayuwar James da kuma tarihin kwallon kafar Colombia baki ɗaya.

Luis Suarez (Uruguay)

Bayan da ya jawo cece-kuce a watan Satumba da ikirarin cewa Marcelo Bielsa ya raba kan ƴan wasan kasar, daga nan makomar Luis Suarez tare da tawagar Uruguay ta fara zama cikin shakku.

Duk da cewa yiwuwar sake buga wata gasar FIFA World Cup na iya zama mai wahala, ɗan wasan mai shekara 39 ya sake komawa kan ganiya da hakan kan iya ba shi damar buga gasar karo na biyar bayan 2010 da 2014 da 2018 da kuma 2022.

Waasanninsa biyu a gasar sun yi kaurin suna saboda hannu da ya sa a lokacin da Ghana za ta ci su a karin lokaci a kwata-fainal na 2010, yayin da a 2014 kuma ya shiga cikin rikicin bayan da ya cizi ɗan kasar Italy, Giorgio Chiellini.

Duk da cewa ba wanda ya goyi bayan abnida ya yi, har yanzu ana jiran ganin ko Bielsa zai sake gayyatar tsohon ɗan wasan tawagar, domin yiwuwar bankwana ta karshe a gasar duniya.

Mohamed Salah (Egypt)

Kwallon kafar ƙasar Masar ta samu ci gaba mai yawa saboda wani fitaccen ɗan gaba da ke ɗauke da burin kai kasar a kan ƙololuwar tamaul a Afirka da duniya gabaki ɗaya.

Mohamed Salah ya halarci gasar FIFA World Cup ta 2018 duk da yana fama da rauni, abin da ya hana duniya ganin cikakken bajintarsa a wasannin.

Komawarsa gasar 2026 — wacce za ta kasance karo na huɗu a tarihi — za ta yi fatan taka rawar gani a karon farko fiye da wasannin da ta halarta a baya.

Shigarsa cikin shekara 30s na nufin wannan ka iya zama dama ta ƙarshe ga Salah, domin ya bar tarihi a gasar FIFA World Cup.

Sadio Mane (Senegal)

Sadio Mane

Asalin hoton, Getty Images

A yanzu dai baya kan ganiya kamar da, kasancewar Sadio Mané a gasar FIFA World Cup ta 2026 a Arewacin Amurka ana ganin ita ce ta karshe da zai halarta.

Yanzu yana da shekaru 34, ɗan wasan tawagar Senegal yana cikin tawagar "Lions of Teranga" da ta fice daga gasar 2018 a matakin rukuni bisa ƙididdigar fair play points, sannan a 2022 suka kai zagaye ƴan 16 kafin Ingila ta doke su da ci 3-0.

Wannan tarihin yana nuna irin ci gaban da Senegal ta samu a gasar kofin duniya, tare da yiwuwar gasar 2026 ta zama bankwana ga ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasanta na zamani.

Kalidou Koulibaly (Senegal)

Kalidou Koulibaly ya tabbatar da matsayinsa na gwarzo a ƙasar Senegal bayan da ya jagoranci "Teranga Lions" a matsayin ƙyaftin wajen lashe kofin Africa Cup of Nations da kuma kaiwa matakin fitar da gwani a gasar FIFA World Cup ta 2022.

Fuskantar manyan ƴan gaba na duniya a gasar 2026 ya ba shi damar ƙarshe — yana da shekaru 34 — don nuna irin kwarewa da ƙarfinsa a matakin tamaula a duniya.

Wannan na iya zama babi na karshe ga ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan tsaron bayan Senegal a zamaninsa.

Riyad Mahrez (Algeria)

Riyad Mahrez zai halarci gasar kofin duniya karo na biyu — kuma mai yiwuwa ta ƙarshe — a gasar FIFA World Cup, bayan shekara 12 da ya fara shiga gasar a 2014.

A wancan lokacin, tsohon kocin Algeria Vahid Halilhodžić an ruwaito cewa ya fuskanci zargin rashin gaskiya ta yadda ya shigar da Mahrez cikin tawagar a 2014, kodayake irin waɗannan batutuwa babu su a cikin tawagar da Vladimir Petković zai jagoranta a gasar da za a buga a Arewacin Amurka.

Yanzu yana da shekaru 35, Mahrez na iya shiga gasar ne a matsayin ɗaya daga cikin gogaggun ƴan wasa a abin da zai iya zama bankwana da babbar gasar ƙwallon ƙafa ta duniya.

Vozinha (Cape Verde)

Vozinha, mai tsaron raga na Cape Verde, zai yi murnar cika shekaru 40 a lokacin gasar FIFA World Cup, abin da ke nuna irin tsufansa a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƴan wasa mafi shekaru a tarihin gasar.

Kasancewarsa muhimmi kuma ginshiƙi ga wata ƙasa da za ta shiga gasar a karon farko a tarihi ya ƙara bayyana muhimmancinsa ga tawagar Cape Verde.

Wannan hali na gogaggen mai tsaron raga na nuna yadda ƙwarewa duk da yawan shekarunsa, wanda ke kan ganiya a taka rawa a matakin duniya, musamman ga ƙananan ƙasashe masu tasowa a ƙwallon kafa.

Guillermo Ochoa (Mexico)

Magoya bayan Mexico sun saba ganin fitaccen mai tsaron ragarsu, yana zama tamkar katanga a kowace gasar FIFA World Cup da ake yi duk bayan shekara huɗu.

Wannan gogaggen mai tsaron gida ya yi suna ta hanyar tare ƙwallaye su shiga raga masu ban mamaki da manyan ƴan gaba ke nuna fasaharsu a duniya, ya buga gasar 2014 da 2018 da kuma ta 2022, tare da kasancewa cikin tawagar a 2006 da 2010 ba tare da buga wasa ko ɗaya ba.

Ƙoƙarin samun shiga tawagar gasar kofin duniya karo na shida zai sanya Guillermo Ochoa cikin rukunin ƴan wasa na musamman a tarihin gasar.

Kenan a wannan gasar da Mexico ma ke karbar bakunci, zai samu yin ban kwana da tawagar Mexico, wacce ake kira "El Tri".

Johnny Placide (Haiti)

Johnny Placide na daga cikin ƴan wasa mafi gogewa da ake sa ran za su halarci gasar FIFA World Cup, inda mai tsaron ragar ƙasar Haiti ya taka muhimmiyar rawa a dukkanin matakan neman tikitin shiga gasar bana.

Ɗan shekaru 38 ya nuna kwarewa da jagoranci, wanda ya taimaka wajen tabbatar da tsaron baya da kuma dorewar ƙwazon tawagar Haiti a lokacin wasannin share fagen shiga gasar.

Kwarewarsa da hangen nesa a filin wasa sun sa ya zama ginshiƙi ga tawagar, musamman a lokutan da aka fi bukatar kwanciyar hankali da gogewa a manyan wasanni.

Son Heung-Min (South Korea)

....

Asalin hoton, Getty Images

Son Heung-min ya nuna tasiri mai girma a tawagar Koriya ta Kudu bayan da ya taka rawar gani wajen doke Portugal a gasar FIFA World Cup ta 2022.

Yin wasa duk da raunin da ya ji a fuska a lokacin gasar ya nuna irin jajircewarsa da sadaukarwa, abin da ya sa ya zama gwarzon kasar.

Idan ya kai ga shiga gasar 2026 yana da shekaru 33, hakan na iya zama dama ta karshe ga dan wasan Los Angeles FC ta Amurka, domin jagorantar Koriya ta Kudu zuwa matakan karshe a gasar cin kofin duniya.

Wataru Endo (Japan)

Wataru Endo ya kasance ɗaya daga cikin muhimman ƴan wasa a tawagar Japan da ta yi nasara mai tarihi a kan Jamus da Sifaniya a gasar FIFA World Cup ta 2022.

A wannan gasar a Qatar, Japan ta nuna kishin kasa da jajircewa ta yadda ta sanarwa duniya, kowa ya iya taka ledaa duniya ba kamar a baya ba, kafin a taka an san gwani.

Shigarsa gasar 2026 yana da shekaru 33 na nuna cewa wannan ka iya zama babi na ƙarshe a rayuwarsa ta tamaula ta ƙasa da ƙasa, wacce ta ginu bisa aiki tukuru da ladabi.

Chris Wood (New Zealand)

New Zealand za ta koma buga gasar FIFA World Cup bayan shafe shekara 16 ba ta halarta ba, inda hakan ya ba wani fitaccen ɗan gaba mai shekaru 34 damar samun damar da ya dade yana jira.

Chris Wood, wanda shi ne mai rike da tarihin yawan cin ƙwallaye a tarihin ƙasar, zai jagoranci tawagar a babbar gasar tamaula ta duniya da za a buga a Amurka da Canada da kuma Mexico

Kwarewar da yake da ita a gasar Premier League ta Ingila ta zama muhimmiyar ginshiƙi ga tawaga da za ta sake buga gasar kofin duniya a karo na farko tun bayan 2010.

Idan ya samu damar zura ƙwallo a wannan mataki, hakan zai zama cikar mafarki ga ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan da New Zealand ta taɓa samarwa.