Za a yi gagarumin hazo a wasu yankunan arewa - NiMet

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet, ta ce za a samu yanayin hazo a wasu yankunan arewacin Najeriya ranar Alhamis.
Wata sanarwa da NiMet ta fitar a shafin X, ta ce jihohin da za a fi samun hazo da safe sun kunshi Kano, Jigawa, Katsina, Bauchi da kuma sassan Yobe.
Sanarwar hukumar ta ƙara da cewa da yammacin yau Alhamis kuwa, hazon zai ragu zuwa na matsakaici a faɗin yankin.
NiMet ta ce wasu sassan jihohin arewa maso tsakiya ma za su fuskanci yanayi na hazo a safiyar yau, waɗanda suka haɗa da Abuja, babban birnin Najeriya, Kogi, Kwara da kuma Benue.
Saboda haka ne hukumar ta buƙaci mutane da su ɗauki matakan kariya daga hazo da za a samu, ta hanyar guje wa shiga wuraren da za a samu kura da saka takunkumin fuska yayin fita waje.
Hukumar ta kuma gargaɗi masu ababen hawa da su yi taka tsantsan, inda ta buƙaci da su rage gudu fiye da ƙima da kuma bin dokokin hanya.


