Ɗan wasan fim Pete Edochie ya rasu

Asalin hoton, Pete Edochie
An tabbatar da mutuwar ɗan wasan fim na Najeriya Pete Edochie.
Iyalan shahararren ɗan fim ɗin ne suka fitar da sanarwar rasuwarsa yana da shekara 79 a duniya bayan ya yi fama da cutas kansar bakin mafitsara.
Edochie ya rasu ne da kimanin ƙarfe 12:30 na daren ranar Laraba.
Edochie tsohon ɗan jarida ne kuma ɗan fim wanda ya yi suna a kan rawar da ya taka a fina-finan Najeriya, kamar labarin 'Things Fall Apart' da aka yi fim a kan shi, wanda Chinua Achebe ya rubuta.
Wane ne Pete Edochie?
An haifi Pete Edochie ne a ranar 7 ga watan Maris 1974 a garin Zaria da ke jihar Kaduna, duk da cewa iyayensa sun fito ne daga Akamnato, Ifite Nteje da ke jihar Anambra a kudancin ƙasar.
Ya yi makarantar Firamare ta St Patrick and St James da ke Zaria, kafin tafiya kwalejin St James College da ke Kaduna.
Ya karanta aikin jarida a kwalejin karatun aikin jarida da talabijin da ke Ingila.
Kafin shiga harkar wasan kwaikwayo, Edochie ya kasance shahararre a ɓangaren aikin jarida.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya fara aiki da kafar yaɗa labarai ta gabashin Najeriya a shekarar 1967 inda ya kai har matsayin darakta mai kula da shirye-shirye a hukumar yada labarai ta Anambra, daga baya ya zama mai taimaka wa shugaban hukumar kafin daga baya ya zama mai riƙon shugabancinta.
Tauraruwar Pete Edochie ta haska ne a wani wasan kwaikwayo na kafar yaɗa labarai ta Najeriya – NTA – da aka shirya daga littafin 'Things Fall Apart' wanda Chinua Achebe ya rubuta.
Rawar da ya taka a matsayin jarumi kuma mayaƙi ɗan ƙabilar Ibo ta sanya ya zamo ɗaya daga cikin manyan jarumai a masana'antar fim ta Najeriya.
Sauran fina-finan da ya haska sosai a cikin su sun haɗa da 'Rituals' da 'Billionaire's Club' da fim ɗin 'Lionheart' na Genevieve Nnaji da aka yi a 2018.
A shekarar 1980 ya samu horo daga kafar yada labarai ta Birtaniya, wato BBC, sannan ya ci gaba da samun nasarori a harkar wasan fim da yaɗa labarai, inda a 1987 ya zama darakta na farko na kafar yada labarai ta Anambra.
Sai dai ya yi ritaya daga muƙamin a cikin shekarar lokacin da ya yi zargin gwamnati da tsoma baki cika al'amura gidan yada labaran.



























