Fitattun matasa 8 da ke takara a zaɓen Najeriya na 2027

Asalin hoton, Social Media Handles
- Marubuci, Abdulrazzaq Kumo
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Shigar matasa cikin harkokin mulki da siyasa na ci gaba da kasancewa batu mai jan hankali a Najeriya inda har yanzu ake ce-ce-ku-ce kan irin tasirin da suke da shi wajen jagoranci. Yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, wasu fitattun matasa daga fannoni daban-daban na rayuwa na takarar kujerun siyasa.
Wasu daga cikinsu sun yi fice a harkokin gwamnati da kasuwanci, wasu kuma ƴaƴa ne ga wasu fitattun ƴan siyasar ƙasar.
To amma su waye waɗannan matasan da ake kallo a matsayin masu iya taka rawa a zaɓen 2027? BBC ta yi nazari kan fitattun matasa 10 da takararsu ke jan hankali a babban zaɓen da ke tafe.
Mustapha Sule Lamido

Asalin hoton, Mustapha Sule Lamido
Mustapha Sule Lamido na neman kujerar gwamnan Jigawa a jam'iyyar PDP. A watan Mayun 2026 jam'iyyar ta amince da shi a matsayin ɗan takararta na gwamna, ba tare da hamayya ba.
Ya shiga siyasa a shekarar 2019 inda ya yi takarar kujerar Majalisar Dattawa mai wakiltar Jigawa ta Tsakiya a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.
A shekarar 2023, Mustapha ya sake fitowa takarar gwamnan Jigawa a ƙarƙashin PDP, inda ya fafata da Umar Namadi na APC, wanda ya lashe zaɓen.
Mustapha ɗa ne ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Sule Lamido.
Yusuf Buhari

Asalin hoton, Yusuf Buhari/fb
Yusuf Buhari na takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar Daura, Sandamu da Mai'adua a jihar Katsina.
Yusuf ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne. Mahaifinsa ya shugabanci Najeriya daga 2015 zuwa 2023, a ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Zai yi takara ne a ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Abba Mangal

Asalin hoton, Abba Mangal/fb
Abba Mangal yana takarar kujerar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Katsina ta tsakiya a jam'iyyar APC inda ya maye gurbin Sani Aliyu Danlami wanda yake kan kujerar a yanzu kuma a APC.
Abba lauya ne kuma ɗa ga fitaccen ɗan kasuwa a jihar Katsina wato Dahiru Bara'u Mangal.
Yana daga cikin mafi ƙarancin shekaru da suka samu takara a faɗin Najeriya.
Aliyu Mohammad (Sarkin Mota)

Asalin hoton, Sarkin Mota/X
Aliyu Mohammed wanda aka fi sani da Sarkin Mota fitaccen ɗan kasuwa ne wanda ya shahara wajen sayar da motoci. Ya yi suna ne musamman saboda salonsa na tallata motocin a shafukan sada zumunta.
Matashin yana takarar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da Girei a ƙarƙashin jam'iyyar NDC.
Mustapha Rabiu Kwankwaso

Asalin hoton, Mustapha Kwankwaso/fb
Mustapha Rabiu Kwankwaso ɗa ne ga tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.
Yana takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a jam'iyyar NDC amma a baya ya riƙe muƙamin kwamishinan matasa da wasanni a gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Sai dai har yanzu kotu ba ta gama tantance takararsa ba tare da Aminu Abdussalam Gwarzo.
Adamu Atiku

Asalin hoton, Adamu Atiku/fb
Ɗa ne ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo, Atiku Abubakar
Mahaifinsa ya daɗe yana cikin manyan ƴan siyasar da ake damwa da su aaƙasar, kuma ya taɓa neman shugabancin Najeriya sau da dama a jam'iyyu daban-daban.
Yanzu haka mahaifinsa ne ke takarar shugaban ƙasa a babbar jam'iyyar adawa ta ADC a zaɓen 2027 da ke tafe.
Adamu Atiku yana takarar Sanata a mazaɓar Adamawa ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar ADC.
Mohammed Turad Sha'aban

Asalin hoton, Mohammed Turad Sha'aban/fb
Mohammed Turad Sha'aban yana takarar sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa a ƙarƙashin jam'iyyar NDC.
Turad ɗa ne ga tsohon ɗan majalisa Sani Mohammed Sha'aban kuma ya auri ɗiyar tsohon shugaban Najeriya, Hanan Buhari.
Ya yi takarar zaɓen fitar da gwani na sanata a jam'iyyar APC a 2022, amma bai yi nasara ba.


























