Me ya sa wasu mutane ke daina jin sha'awar yin Jima'i?

Asalin hoton, Getty Images
Raguwa ko kuma rashin sha'awar jima'i gaba ɗaya wata matsala ce da ke damun mutane da dama a faɗin duniya, maza da mata baki ɗaya.
Ko da yake galibi ana ɗaukar wannan batu a matsayin abin kunya, kuma mutane da yawa kan ɓoye shi a matsayin sirri. Sai dai likitoci sun ce wannan abu ne na jiki da kuma na tunani da zai iya faruwa ga kowa a wani mataki na rayuwarsa.
Fahimtar musabbabin wannan matsala shi ne mataki na farko wajen samun mafita da kuma dawo da farin ciki da jituwa a cikin dangantaka.
Ga manyan dalilan da ke sa mutane daina sha'awar jima'i:
Matsalolin tunani da na damuwa
Ƙwaƙwalwa ita ce gaɓar jiki ta farko da ke haifar da sha'awar soyayya da jima'i. Idan mutum ba ya cikin kwanciyar hankali, jiki ma ba zai iya ba da haɗin kai wajen tayar da waɗannan sha'awoyi ba.
Saboda haka, mutumin da ke fama da damuwa sakamakon tsadar rayuwa ko matsalolin kuɗi ko nauyin aiki mai yawa, jikinsa kan samar da sinadarin cortisol. Idan wannan sinadari ya yi yawa a jiki, yana iya rage sha'awar jima'i.
Haka kuma mutanen da ke fama da matsananciyar damuwa (depression) ko yawan fargaba da tashin hankali (anxiety), sau da yawa su kan rasa jin daɗi da kuma sha'awar jima'i.
Ta fuskar damuwa kuwa, samun matsala da iyalinka ta hanyar faɗa ko musu na iya janyo rashin sha'awa. Misali, ɓoyayyen fushi ko rashin yafiya ko rashin kyakkyawar sadarwa da kuma rashin yarda tsakanin ma'aurata, duk waɗannan abubuwa na matuƙar kashe sha'awar soyayya da jima'i.
Sauye-sauyen sinadaran jiki

Asalin hoton, amenclinics
Lokacin da wasu sauye-sauye na sinadarai ko na yanayin jiki suka faru, suna iya yin tasiri kai tsaye kan sha'awar jima'i.
Misali, raguwar sinadarin testosterone a wajen maza. Idan wannan sinadari ya ragu, musamman sakamakon tsufa, ƙarfin jiki da kuma sha'awar jima'i kan ragu sosai.
A wajen mata kuwa, shiga shekarun daina al'ada (menopause) da kuma juna biyu na daga cikin abubuwan da kan rage sha'awar jima'i.
A lokacin juna biyu da kuma bayan haihuwa musamman lokacin shayarwa, ko kuma lokacin da mace ta kai ga daina al'ada, yawan sinadaran estrogen da progesterone a jiki kan ragu sosai. Wannan yanayi na iya haifar da bushewar farji da kuma jin zafi yayin saduwa, lamarin da kan sa mace ta kauce wa jima'i.
Matsalolin lafiya
Cututtukan da ke raunata jiki ko kuma suke shafar jijiyoyin jiki da zagayawar jini na taka muhimmiyar rawa wajen rage sha'awar jima'i.
Daga cikin irin waɗannan cututtuka akwai:
Ciwon sukari (diabetes)
Hawan jini
Cututtukan zuciya
Cutar daji (cancer)
Matsalolin glandar thyroid (thyroid gland)
Waɗannan cututtuka na iya shafar yadda jiki ke aiki, da rage kuzari, da kuma kawo cikas ga hanyoyin da ke da alaƙa da sha'awar jima'i, lamarin da kan haifar da raguwar sha'awar saduwa.
Shan magunguna da kuma irin rayuwar da mutum ke gudanarwa
A wasu lokuta, halayenmu na yau da kullum da abubuwan da muke sakawa a jikinmu na iya rage mana sha'awar jima'i ko jin daɗin saduwa.
Akwai wasu nau'ukan magunguna, musamman waɗanda ake amfani da su wajen magance matsananciyar damuwa (antidepressants), magungunan hawan jini, da kuma wasu ƙwayoyin hana samun ciki, waɗanda kan rage sha'awar jima'i.
Haka kuma, yin aiki na sa'o'i da yawa ba tare da samun isasshen hutu ba kan janyo gajiya mai tsanani, ta yadda ƙarfin da ya rage wa mutum shi ne kawai na yin barci.
Wani abin kuma shi ne, yawan shan giya da kuma shan sigari na iya lalata tsarin zagayawar jini da kuma jijiyoyin jiki, lamarin da zai iya janyo rashin sha'awar jima'i.
Shawarwari

Asalin hoton, ltclinics
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Raguwar ko daina sha'awar jima'i ba yana nufin ƙarshen duniya ba ne, kuma ba alama ce cewa soyayya ta ƙare ba. Sau da dama, saƙo ne daga jiki cewa akwai wani abu da ke buƙatar gyara ko kulawa.
Magance wannan matsala na buƙatar yin magana kan abin da ke damun ka da kuma haƙuri. Mataki na farko shi ne ma'aurata su tattauna matsalar cikin gaskiya da fahimtar juna, ba tare da zargi ko ɗora wa juna laifi ba, domin hakan zai taimaka wajen gina fahimtar juna da samun mafita tare.
Mataki na biyu shi ne yin sauye-sauye a salon rayuwa, kamar cin abinci mai gina jiki da motsa jiki da samun isasshen lokaci na hutu da barci. Waɗannan abubuwa na iya taimakawa wajen inganta lafiyar jiki da tunani, da kuma dawo da sha'awar jima'i.
A ƙarshe, idan matsalar ta ci gaba duk da waɗannan matakan, yana da muhimmanci a tuntuɓi likita ko ƙwararren masanin ilimin halayyar ɗan Adam domin a gudanar da gwaje-gwajen da suka dace, ciki har da na sinadaran hormone, ko kuma a ba da maganin da ya dace da matsalar, ko ta fuskar lafiyar jiki ko ta tunani.



























