KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 23/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 23/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Ana shirin fara Gasar Karatun Qur'ani ta duniya a Pakistan

    Makaranci

    Shahararrun mahaddatan Alƙur’ani daga sassa daban-daban na duniya sun fara isa Pakistan domin halartar gasar karatun Alƙur’ani ta duniya.

    Ma’aikatar Harkokin Addini ta Pakistan ce ke shirya gasar, wadda za a gudanar a birnin Islamabad daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Nuwamba, tare da halartar mahaddata daga ƙasashe 32 ciki har da Pakistan.

    Mahaddata daga Kamaru da Togo da Mozambik da Uzbekistan sun isa Islamabad a daren Lahadi, yayin da mahalarta daga Jamus da Jordan da Aljeriya da Iraki da Libiya da Turkiyya suka isa ƙasar a ranar Litinin.

    Haka kuma, mahaddata daga Tunisiya da Côte d’Ivoire da Masar da Tanzaniya da Gambiya da Najeriya da Qatar da Moroko da Faransa sun isa Islamabad domin shiga taron na kwanaki uku.

    Fitaccen gwanin Alƙur’ani na duniya, Qari Syed Sadaqat Ali, ne zai kasance babban alƙalin gasar karatun Alƙur’anin ta ƙasa da ƙasa karo na biyu.

    Ana sa ran sauran mahaddatan daga ƙasashen da za su halarta za su ci gaba da isa Pakistan har zuwa daren Litinin.

  2. Tinubu ya umarci Masari ya sasanta da Dikko

    Masari

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya babban mai ba shi shawara kan harkokin siyasa Ibrahim Kabir Masari ya sasanta da gwamnan Katsina Umar Dikko Radda.

    Yayin da yake jawabi a wajen taron addu’o’i na musamman da ‘yan uwansa suka shirya masa a Yoruba Tennis Club da ke Legas, shugaba Tinubu ya ce shugabannin jam’iyyar APC su ajiye saɓanin ra’ayi a tsakaninsu, su yafe wa juna tare da rungumar sulhu yayin da jam’iyyar ke shirin babban zaɓen shekarar 2027.

    Bayanai na cewa akwai saɓanin siyasa tsakanin Masara da Gwamna Radda, lamarin da ya shafi tafiyar siyasar ɓangarorin biyu a jihar.

    A wata hira da BBC a baya-bayan nan Ibrahim Kabir Masari ya tabbatar da saɓani tsakaninsa da gwamnan, sai dai ya ce bai taɓa nadamar taimaka masa ba.

    Kan haka ne Shugaba Tinubu ya umarci Masari ya koma gida domin sasanta duk wata matsala da ke tsakaninsu.

    “Ya kai abokina, sarkin aiki, Alhaji Kabiru Masari, ka koma gida ka sasanta kowa da kowa. Wannan umarnin shugaban ƙasa ne. Bayan ka kammala haka, sai ka je Jigawa da sauran wurare domin sulhunta mutane, ka roƙe su, domin dole ne mu sasanta, kuma duk wata fushi ta kau.”

    Haka kuma ya bai wa Abubakar Badaru, wanda tsohon gwamnan Jihar Jigawa ne, irin wannan aiki, yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin mambobin jam’iyyar.

    Tinubu ya ce bai kamata matsalolin ƙashin kai su yi wa muradun APC na bai ɗaya barazana ba, musamman yayin da jam’iyyar ke ƙoƙarin ci gaba da riƙe mulki a zaɓen shekarar 2027.

  3. Muna shirin daina ƙera jiragen yaƙi masu amfani da direbobi

    ;;;

    Kwamandan Rundunar Sojin Sama ta Birtaniya (RAF) ya ce jirgin yaƙi na zamani da ƙasar ke shirin ƙerawa nan gaba na iya kasancewa jirgin yaƙi na ƙarshe da matuƙi ke sarrafawa.

    Air Marshal Harvey Smith ya ce jiragen yaƙi marasa matuƙa da ke amfani da fasahar ƙirƙirar basira ta na’ura (AI) za su sauya fasalin harkokin jiragen yaƙi na soji gaba ɗaya.

    Jawaban nasa na da nasaba da shirin Global Combat Air, wani haɗin gwiwa tsakanin Birtaniya da Italiya da Japan na ƙera jirgin yaƙi, wanda ake sa ran zai fara aiki nan da shekarar 2035.

    Ana sa ran jirgin, wanda aka fi sani da Tempest, zai kasance mai saurin gaske, yana da fasahar ɓuya daga na’urorin gano jirage (stealth), da na’urorin sa ido na zamani, da kuma fasahar AI da za ta taimaka wa matuƙa wajen sarrafa yanayi mai cike da bayanai ko matsanancin matsi.

    A wani sharhi da ya rubuta a jaridar Telegraph, Harvey Smith ya ce jirgin yaƙin “na iya zama jirgin yaƙi na ƙarshe da matuƙi ke tukawa da za mu taɓa ƙerawa.”

    Ya ce hakan ba yana nufin rawar ɗan Adam na raguwa ba ne, sai dai ci gaban fasaha na sauya yadda ake gudanar da yaƙe-yaƙen sama.

    Harvey Smith ya ce a nan gaba, fasahar ƙirƙirar basira ta na’ura da kuma injuna ne za su riƙa gudanar da “ayyuka mafi haɗari ga ɗan Adam”, amma ya jaddada cewa ya kamata fasaha ta taimaka wa ɗan Adam wajen yin hukunci da yanke shawara, ba maye gurbinsa wajen ɗaukar alhaki ba.

    Shugaban rundunar sojin saman ta Birtaniya ya kuma ce: “Daga shekara mai zuwa jiragen yaƙi marasa matuƙa za su fara shawagi a sararin samaniyar Birtaniya. Wannan abu ne mai ƙayatarwa kuma wajibi.”

  4. Adadin waɗanda suka mutu a hatsarin kwale-kwalen Bayelsa ya kai 29

    Douye Diri

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwalen da ya auku ranar Juma’a a ƙaramar hukumar Southern Ijaw da ke Jihar Bayelsa ya ƙaru zuwa mutum 29, yayin da sama da mutum 50 da suka tsira ke karɓar magani a asibitoci.

    Gwamnan jihar, Douye Diri, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar jaje da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai masa.

    Diri ya ce har yanzu ba za a iya tabbatar da adadin mutanen da suka rasa rayukansu gaba ɗaya ba, domin ana ci gaba da ƙoƙarin ciro kwale-kwalen da ya haddasa hatsarin.

    Sai dai ya ce akwai yiwuwar wasu fasinjoji na nan maƙale a cikin kwale-kwalen.

    Gwamnan ya yi zargin cewa kwale-kwalen bai dace da zirga-zirgar ruwa ba, sannan kuma ya tashi ne daga wata tashar fasinjoji da ba a amince da ita ba.

  5. Birtaniya za ta fara amfani da AI domin gano cutar kansar mama

    Birtaniya za ta fara gwaji mafi girma a duniya da ke amfani da fasahar AI domin taimakawa wajen gano cutar kansar mama.

    Ana gayyatar mata kusan 700,000 domin su shiga wannan gwaji.

    Za a yi amfani da fasahar AI wajen duba sakamakon hotunan sassan jiki (X-ray), domin ganin ko za ta iya inganta gano cututtuka da wuri tare da rage nauyin aiki kan ma'aikatan kiwon lafiya.

    Farfesa Fiona Gilbert na daga cikin jagororin gwajin, wadda kuma ta ce suna da yaƙinin cewa fasahar za ta taimaka wurin inganta kaifin basirar ma'aikatan lafiya kuma za a iya gano masu cutar kansa da dama.

    Kansar mama na daga cikin cutuka mafiya yawa a tsakanin matan Birtaniya.

  6. Jirgin yaƙin Rasha ya fashe a tekun Libya

    ..

    Gwamnatin yankin Libya ta bayyana cewa an samu fashewa a cikin wani jirgin ruwan yaƙi na Rasha a birnin Benghazi.

    Ana zargin harin jirgi mara matuƙi ne aka kai kan jirgin ruwan, sannan ta ƙara da cewa daga baya an kai hari kan wani jirgin ruwan kasuwanci mai ɗauke da tutar Malta.

    Mutane goma ne suka jikkata sakamakon fashewar da ta faru a jirgin na Rasha, kuma jirgin ruwan mai suna Merkury—ya kusan nutsewa.

    Ba a bayyana ko su waye ke da alhakin kai hare-haren ba.

    Sai dai ana cewa ƙwararrun 'yan Ukraine masu sarrafa jiragen sama marasa matuƙa suna aiki a yammacin ƙasar Libya.

  7. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin, Mande tushen aiki da ko da nasara na tsoronki kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.