Yadda ake samun koma-baya a ilimin 'ya'ya mata a Nijar

Dalibai

Asalin hoton, OTHER

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Masu futukar kare hakki da ilimin 'ya'ya mata a Jamhuriyar Nijar sun koka da rashin cigaban karatun 'ya'ya mata a kasar.

Duk da kokarin da kungiyoyin iyaye mata ke yi wajen martaba karatun yara musamman 'yan mata, har yanzu akwai sauran rina a kaba game da ci gaban karatun 'ya'ya mata wadanda alkaluma ke cewa kalilan ne daga cikinsu da suka fara karatun ke kai labari.

Nana Hadiza, mai fafutukar kare hakki da ilimin 'ya'ya mata ce a kasar, ta shaida wa BBC cewa, ba karatun ne aiki ba, ci gabansa ne matsala.

Ta ce," Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa a cikin kashi 64 zuwa 83 cikin 100 na daliban da suke mata ne da ke karatu a matakin farko na firamare, da kyar ake samun kashi 20 cikin 100 a cikinsu da ke ci gaba da karatu."

" Kuma cikin abubuwan da muka lura muka gano cewa na kawo wa 'ya'ya matan cikas wajen ci gaba da karatunsu shi ne auren wuri."

Wata mahaifiya da ke a birnin Yamai, ta shaida wa BBC cewa, yawancin wannan matsala ta rashin ci gaban karatun 'ya'ya mata ba a birni take ba, domin mutanen birni yanzu sun waye domin sun san muhimmancin ilimin 'ya'ya mata.

Ta ce," yanzu mutanen birni sun waye domin suna sanya 'ya'ya mata makaranta su yi karatun boko mai zurfi,to amma wadanda ke zaune a kauye ne ke cikin wannan matsala."

" Muna kira ga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da ke bayar da tallafi a bangaren karatu da su taimaka wa yaranmu na kauye su samu ilimi." In ji ta.

Ita kuwa wata matashiya da ta daina karatun bayan ta kammala sakandire, ta shaida wa BBC cewa, ita kanta tana son ci gaba da karatu, to amma dalili ne ya hanata.

Ta ce," Hali na yau da kullum ne ya hana ni ci gaba da karatu, to amma ko a yanzu idan na samu dama zan ci gaba da karatuna. Kuma ya kamata mata mu sani cewa idan mace ta yi karatu za ta iya taimakon 'ya'yanta da megidanta da iyayenta da ma sauran al'umma." In ji ta.

Gwamnatin Nijar dai ta samar da kungiyoyi na iyaye mata zalla a cikin makarantu da zummar ba wa 'ya'ya mata kwarin gwiwa na ci gaba da karatu da kare martabar illiminsu da kuma kare su daga auren wuri.

Haka kuma gwamnatin, ta kuduri aniyar inganta hakkin bil-adama gaba daya musamman na mata da 'yammata a don haka inganta hakkin mata da iliminsu da kuma karfafa su, wani bangare ne na manufofin cigaban kasar.