Manoman Najeriya sun yi barazanar daina noman kayan abinci sai na sayarwa

Shuka

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Yayin da ruwan daminar bana ya fara sauka, wasu manoman Najeriya sun yi barazanar daina noma kayan abinci irin su masara da gero da sauransu, inda suka ce za su mayar da hankali ne kan noman kayan amfanin gona na sayarwa kamar waken soya da gyada da dai sauran kayan amfanin gonar da ke bukatar taki.

Manoman sun yi barazanar ne bisa la'akari da irin asarar da suke tafkawa idan sun noma kayan abinci.

Wannan dai na da nasaba da karyewar farashin kayan a kasuwanni, yayin da kayan da ake noman da su kamar taki da maganin kwari kuma farashinsu ke hawa.

Matakin manoman dai ya sa kungiyar manoman Najeriyar, wato AFAN, ta ce ta farga da wannan batu, kuma ta fara bin matakin shawo kan matsala.

Muhammadu Magaji Gettado, shi ne shugaban kungiyar na kasa, ya shaida wa BBC cewa illa ce babba manoman su ce ba za su noma kayan abinci ba.

Ya ce," Lallai muna sane da wannan mataki na manoman kuma tuni muka yi nisa wajen fadakar da manoman namu akan su koma su ce za su noma kayan abinci."

" Ya kamata mutane su sani cewa babbar illa ce a wayi gari a ce ba a noma kayan abinci ba sai kayan sayarwa kawai, domin ai na ce mu noma abincin da za mu ci, to idan aka wayi gari a ce mun dogara da masarar da za a shigo mana da ita daga waje wadda kuma yawancin irin wannan kayan abinci ana ajiye su ne a cikin rumbu su shafe shekaru da dama a ajiye sannan daga baya a kawo shi cikin kasashenmu, to wannan babbar illa ce."

Muhammadu Magaji Gettado, ya ce " Idan manoman kuma suka ce sun daina noma kayan abinci to ai ba su da aikin yi kenan, sannan abinci zai yi tsada."

" Mun riga mun sani manomanmu na cikin damuwa saboda har farashin kayan abici bai yi daraja kamar yadda manoma ke so, ma'ana ta inda za su iya sayar da buhunsu na abinci daya su sayi takin zamani da kudin." In ji shi.

Tun bayan da farashin kayan abinci ya karye sannan kuma gwamnatin Najeriya take ƙara karya farashin domin sauƙaƙa wa 'yan ƙasa, manoma da masana ke ta nuna damuwa dangane da yadda farashin abincin ke faɗuwa amma kuma a gefe guda farashin takin zamani ke ƙara hauhawa.