Su wane ne jagororin yaƙin neman zaɓen Obi da Kwankwaso?

Asalin hoton, Peter Obi
A yayin da siyasar Najeriya ke fara ɗaukar sabon salo gabanin zaɓen shekarar 2027, jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta fitar da jerin sunayen mutanen da za su jagoranci yaƙin neman zaɓenta a faɗin ƙasar, tuni masu bibiyar siyasa sun fara tsokaci kan tasirin mutanen.
Kwamitin, wanda ya ƙunshi manyan ƴan siyasa da tsofaffin masu riƙe da muƙaman gwamnati, zai kasance cibiyar tsara dabaru da daidaita ayyukan yaƙin neman zaɓen Peter Obi da Kwankwaso, yayin da ake tunkarar zaɓen da ake sa ran zai yi zafi tsakanin manyan jam'iyyun siyasar ƙasar.
Jam'iyyar ta ce ta fitar da sunayen kwamitin da nufin faɗaɗa tasirin yaƙin neman zaɓenta a dukkan jihohin Najeriya.
NDC na daga cikin jam'iyyun siyasar da ake ganin za su yi tasiri a zaɓen Najeriya na 2027 da ke tafe.
To amma su waye waɗannan mutanen da aka damƙa wa ragamar yaƙin neman zaɓen Obi da Kwankwaso?
Ga wasu fitattu daga cikin ankwamitin da ake ganin shigarsu zai yi tasiri wa jam'iyyar.
Senator Henry Seriake Dickson

Asalin hoton, Peter Obi
Henry Seriake Dickson gogaggen ɗansiyasa ne kuma jagoran jam'iyyar na ƙasa.
Mista Dickso ya ksance tsohon gwamnan jihar Bayelsa har sau biyu daga shekarar 2021 zuwa 2020.
Kafin zamansa gwamna, ya kasance ɗan majalisar wakilai ta tarayya daga shekarar 2007 zuwa 2012.
Yanzu haka shi ne Satana mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Datawan Najeriya.
Ana ganin gogewarsa a fagen siyasa za ta taimaka wa jam'iyyar wajen tsara dabarun cin zaɓe.
Cleopas Moses Zuwoghe
Sanata Cleopas Moses Zuwoghe shi ne shugaban jam'iyyar NDC na ƙasa, ɗan siyasar Najeriya ne da ya taɓa zama a majalisar dattawan ƙasar.
Kamar dai jagoran jam'iyyar, shi ma Sanata Zuwoghe ɗan jihar Bayelsa ne d ake yankin kudu maso kudancin Najeriya.
Ya fara samun karɓuwa a fagen siyasa ne a matsayinsa na ɗan majalisa, kafin daga bisani ya zama jagoran sabuwar jam'iyyar da ke shirin fafatawa a zaɓen 2027.
Ibrahim Hussain Abdulkarim
Ibrahim Hussain Abdulkarim, wanda aka fi sani da Mallam Ziter, ƙwararre ne a fannin fasahar sadarwa da tsarin bayanan taswira (GIS), sannan ɗan kasuwa ne kuma ɗan siyasa.
An naɗa shi a matsayin Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Ƙasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), inda zai jagoranci ayyukan kamfen ɗin jam'iyyar gabanin zaɓen 2027.
Ikenna Morgan Enekweizu
Barrista Ikenna Morgan Enekweizu fitaccen lauya ne a Najeriya, mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, kuma ƙwararren mai gudanar da harkokin siyasa.
A halin yanzu shi ne sakataren ƙasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC).
Ya fito ne daga yankin Idemili na Jihar Anambra, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara tsarin gudanarwa da na shari'a na sabuwar jam'iyyar siyasar tun kafin babban zaɓen shekarar 2027.
A matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan jami'an jam'iyyar, ana ganin zai taimaka wajen gina tsarin gudanar da ayyukan kwamitin a shirye-shiryensa na siyasa.
Babachir David Lawan

Asalin hoton, Seriake Dickson/FB
Babachir David Lawal injiniya ne kuma ɗan siyasar Najeriya wanda ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Ya yi wannan aiki daga shekarar 2015 , kafin daga bisani a sauke shi daga muƙaminsa a 2017.
Jam'iyyar ta saka shi cikin mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen, kuma ana ganinsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ƴansiyasa daga yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Buba Galadima

Engr. Buba Galadima fitaccen ɗan gwagwarmayar siyasar Najeriya ne, kuma masanin dabarun siyasa.
Ya shafe shafe shekaru da dama yana taka rawa a siyasar ƙasar tun daga shekarar 1978.
An san shi da bayyana ra'ayoyinsa kai tsaye a kafafen yaɗa labarai da kuma sukar gwamnatoci da manufofin siyasa idan ya ga ba su dace ba.
A tsawon shekarun da ya yi a harkokin siyasa, ya sauya daga kasancewa cikin manyan masu tasiri a gwamnati zuwa zama ɗaya daga cikin fitattun jagororin adawa a Najeriya.
Ana ganin zai taka muhimmiyar rawa a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen, musamman kasancewarsa mai baki.


























