Barazana huɗu da ke fuskantar babban zaɓen Najeriya na 2027

INEC

Asalin hoton, INEC

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A daidai lokacin da ya rage sauran watanni a gudanar da babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027, ana ci gaba da tafka muhawara game da wasu abubuwan da suka faru a siyasar ƙasar da suka fara haifar da tambayoyi kan yanayin da za a gudanar da zaɓen.

Wani sabon rahoto daga SBM Intelligence, wanda ya yi amfani da bayanai da rahotanni daga Hukumar INEC da rundunar ƴansanda da Hukumar ICPC da fadar shugaban ƙasa da ƙungiyar fastocin Cocin Katolika ta Najeriya da ma kafafen yaɗa labarai, ya bayyana wasu abubuwan da ka iya ƙara matsin lamba kan dimokuraɗiyyar ƙasar gabanin zaɓen.

Rahoton bai ce za a tafka magudi a zaɓen 2027 ba, ko kuma cewa zaɓen ba zai zama sahihi ba.

Sai dai ya nuna cewa akwai wasu abubuwa huɗu da ka iya zama abin damuwa, waɗanda a cewar binciken, za su iya shafar gudanar da zaɓen, wanda kuma zai iya shafar amincewar jama'a da ma wataƙila sahihancin zaɓen.

INEC ta sanya ranar 20 ga Fabrairun 2027 domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisun tarayya, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi kuma za su gudana ne a 6 ga Maris 2027.

Ga manyan abubuwa huɗu da rahoton ya nuna:

Shari'o'i kan jam'iyyun adawa

Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka ja hankali shi ne abin da ya faru a watan Yuni, lokacin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci INEC ta soke rajistar jam'iyyun siyasa biyar.

Jam'iyyun sun haɗa da African Democratic Congress (ADC) da Accord da Action Alliance da Action Peoples Party da Zenith Labour Party.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da ta ƙalubalanci ci gaba da rajistar jam'iyyun bisa wasu tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kotun ta kuma umarci cewa jam'iyyun kada su shiga zaɓukan da za a gudanar daga baya, ciki har da na 2027.

Matakin ya haifar da damuwa matuƙa, musamman saboda ADC ta zama kusan babbar jam'iyyar hamayya a ƙasar.

Sai dai jam'iyyun sun ƙalubalanci hukuncin, sannan kotun ɗaukaka ƙara ta shiga lamarin, inda a watan Yuli, kotun ta soke hukuncin.

Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce ƙaramar kotun ta yi kuskure wajen sauraron shari'ar tun a farko, saboda a cewarta, kotun ba ta da ruhumi.

Binciken cibiyar ya nuna cewa matakan ɓangaren shari'a za su iya taka rawa wajen shafar yanayin karsashin masu kaɗa ƙuri'a.

Amfani da jami'an tsaro

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani abin da rahoton ya nuna shi ne rawar da hukumomin tsaro ke takawa a lokacin da ake gudanar da zaɓe da ma lokacin shirye-shiryen shiga zaɓen.

Ana buga misali da abin da faru a zaɓen gwamnan jihar Osun na ranar 29 ga Yuli, inda ƴansanda suka kama sakataren gwamnatin jihar Osun, Teslim Igbalaye, tare da wasu mutane biyar yayin wani samame da suka kai a wani gida da ake tunanin mallakinsa ne.

Ƴansandan sun ce sun gudanar da samamen ne bisa bayanan sirri kan wasu da ake zargi da aikata laifuka, kuma sun ce sun gano kuɗi da katunan zaɓe da wasu kayan da suka shafi zaɓen.

Amma dai duk da cewa daga baya an sake Igbalaye, lamarin ya jawo zarge-zarge daga ɓangaren hamayya, inda suka yi zargin ana amfani da hukumomin tsaro wajen tsoratar da mambobinsu.

An dai daɗe ana zargin ana amfanin da jami'an tsaro a zaɓukan Najeriya, maimaikon samar da tsaro kawai a yayin gudanar da zaɓukan, zargin da jami'an tsaron suka daɗe suna ƙarytawa.

Idan jam'iyyun siyasa suka yi imanin cewa ana amfani da ƴansanda ko wasu jami'an tsaro wajen kai wa magoya bayansu hari ko matsa musu lamba, hakan na iya haifar da tsoro da rage ƙarfin yaƙin neman zaɓe da kuma dasa shakku a zukatan mutane kan sahihancin zaɓen.

Tambayoyi kan ƴancin hukumomin gudanar da zaɓe

Abu na uku da rahoton na SBM Intelligence ya bayyana shi ne batun sahihanci da ƴancin hukumomin da ke da alhakin gudanar da zaɓe.

INEC ta fuskanci ƙalubalen shari'a kan wasu batutuwan da suka shafi jadawalin zaɓen, yayin da rikicin cire rajistar jam'iyyun ya kuma sanya hukumar a tsakiyar wata babbar taƙaddamar siyasa.

INEC ta taɓa yin gargadin cewa rashin tabbas kan jadawalin zaɓe na iya kawo cikas ga nauyin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ɗora mata da kuma gudanar da zaɓe cikin tsari.

Akwai buƙatar a ga INEC a matsayin hukuma mai ƴanci da kuma tabbatar da zaman kanta kamar yadda doka ta nuna.

Idan jam'iyyun siyasa da masu zaɓe suka rasa amincewa da hukumar zaɓe, ƙalubalantar sakamakon zaɓe na iya ƙaruwa.

Hakan na iya haifar da yanayin da ƴan takarar da suka sha kaye za su ƙi amincewa da sakamakon.

Ƙara rarrabuwar kawuna

Abu na huɗu da SBM ya kalato da yake ganin zai iya shafar yanayin siyasa da shi ne yadda ake samun ƙarin rarrabuwar kawuna a tsakanin al'umma.

A watan Yuli, shugabannin limaman Cocin Katolika ta Najeriya sun gana da Shugaba Bola Tinubu tare da bayyana damuwarsu kan tattalin arziki, rashin tsaro da kuma yanayin siyasar ƙasar.

Sai dai fadar shugaban ƙasar ta yi martani ne da wani ra'ayin daban, inda Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta samu nasarar daidaita ƙasar tare da samar da ingantaccen yanayi ga tattalin arziki da tsaro.

Wannan rashin jituwa na nuna wani babban ƙalubale da Najeriya za ta iya fuskanta gabanin 2027.

Gwamnati na nuna wasu sauye-sauyen tattalin arziki da kuma abin da ta bayyana a matsayin alamun farfaɗowa daga sumar da tattalin arziki ya yi, yayin da ɓangaren hamayya da wasu ƙungiyoyin farar hula ke ci gaba da mayar da hankali kan tsadar rayuwa da rashin tsaro da tasirin manufofin gwamnati kan talakawa.

Zaɓe na iya zama cikin haɗari idan bambancin ra'ayi na siyasa ya rikiɗe zuwa rashin amincewa mai tsanani tsakanin jama'a da ƴan adawa da hukumomin gwamnati.

Idan wani ɓangare na masu zaɓe ya yi imanin cewa hukumomi ba sa yi musu adalci, ko da zaɓen ya gudana cikin tsari, za a iya samun matsalar amincewa da sahihancin sakamakon.