Arsenal, Manchester City da Al-Hilal sun nuna sha'awar daukar Pedro Neto

Pedro Neto

Asalin hoton, BBC Sport

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal, Manchester City da Al-Hilal sun nuna sha'awar daukar dan wasan gefe na Chelsea, Pedro Neto, sannan kungiyoyin za su iya yunkurin sayen dan wasan dan kasar Portugal mai shekara 26 a lokacin kasuwar musayar 'yan wasa a watan Janairu. (Caught Offside)

Chelsea na son kammala yarjejeniyar daukar dan wasan Bournemouth, Alex Scott, da nufin cewa ya koma taka leda a Stamford Bridge a bazarar shekara mai zuwa bayan ta gabatar da tayin fam miliyan 60 akan dan wasan abin da Bournemouth ta yi watsi da shi.. (Teamtalk)

Dan wasan gaba na Chelsea, Christopher Nkunku, mai shekara 28, ya yi watsi da tayin da Manchester United da Newcastle United suka yi masa, kafin daga bisani ya kammala komawa tsohuwar kungiyarsa ta RB Leipzig a matsayin aro. (Bild da Sky Sport Germany ta hannun Caught Offside).

Dan wasan gaban Amurka, Folarin Balogun, na iya komawa buga gasar tamaula ta Saudiyya, inda har yanzu kasuwar musayar 'yan wasa ke bude, yayin da Monaco ke fuskantar matsin tattalin arziki da ka iya sa ta sayar da dan wasan mai shekara 25, bayan da ya fasa komawa Everton a karshen wa'adin kasuwar musayar 'yan wasa ta bazara. (Football Insider).

Chelsea ta fara yunkurin daukar dan wasan Bournemouth, Alex Scott, yayin da dan wasan Chelsea Pedro Neto ke ci gaba da jan hankalin wasu kungiyoyi, irin su Manchester United da Newcastle United da suka nemi bayanai kan halin da dan wasan Chelsea, Christopher Nkunku, ke ciki.

Kwantiragin dan wasan Newcastle United, Jacob Murphy, za ta kare a bazara mai zuwa, to amma kungiyar ta Tyneside na duba yiwuwar ba wa dan wasan dan kasar Ingilan mai shekara 31 sabuwar yarjejeniya don ya ci gaba da zama a kungiyar. (Football Insider).

Tsohon dan wasan Chelsea, Hakim Ziyech, ya raba gari da kungiyar Wydad in da dan wasan dan kasar Morocco mai shekara 33 ake alakanta shi da yiwuwar komawa kungiyar Botafogo ta Brazil. (Goal).

Dan wasan tawagar Ingila, Curtis Jones, mai shekara 25, ya ce tattaunawar da ya yi da kocin Inter Milan, Cristian Chivu, ta taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawarar komawa kungiyar ta Italiya daga Liverpool a wannan bazarar. (Mirror).