'Yan sanda sun ce 'yan bindiga sun kashe mutane 10 a Taraba

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Taraba ta ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari ƙauye Binarri da ke karamar hukumar Karim Lamido, inda suka kashe aƙalla mutum 10, suka yi awon gaba da kayayyakin abinci daga shaguna tare da ƙona gidaje masu yawa.
Cikin hirarsa da BBC kakakin 'yan sandan jihar Victor Mshelizah ya tabbatar cewa mutum 10 da aka gano gawarsu akwai harbin bindiga a jikinsu.
"Duka da harbin bindiga jikinsu. Mun gano takwas daga cikin gawarwakin, 6 maza ne, biyu mata ne, kuma mun miƙa wasu ga 'yan uwarsu domin yi musu jana'iza,".
Jami'in ya ce sun ƙara gano gawarwakin wasu mutane 15 da suka nutse a kogi bayan kifewar kwalekwalensu.
"Har yazuwa yanzu ba mu kai ga gano su wane ne ba, sannan kuma ba mu gano musabbabin tafiyar da suka yi cikin daren ba, amma dai sun fito ne daga yankin Binnari na Karim Lamido," in ji kakakin 'yan sandan.
Mshelizah ya ce ya zuwa yanzu sun girke ƙarin jami'ai a yankin domin tabbatar da zaman lafiya da kuma ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin mutane.








