Mendy ba zai buga wa Senegal wasa da Iraqi ba ranar Juma'a, Senegal
Asalin hoton, Getty Images
Raunin gwiwa da Edouard Mendy mai tsaron raga na Senegal ya ji a yayin wasan da suka sha kashi a hannun Norway a ranar Litinin, ba zai sa ya buga wasan kofin duniya da Iraq a ranar Juma’a, kamar yadda tawagar ta bayyana a ranar Laraba.
Mendy ya ji raunin ne yayin da yake kokarin hana kwallo ta shiga raga, kuma ya bar filin wasa a minti na 63 yayin da Norway ke kan gaba da cin 3-1.
Norway ta yi nasara da ci 3-2 bayan Ismaila Sarr ya zura kwallonsa ta biyu a karin lokaci.
Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce Mendy, mai shekaru 34, ya samu matsala a jijiyar gwiwa.
Senegal da Iraq za su fuskanci juna a wasa na karshe a cikin rukuni a gasar cin kofin duniya da za su kara a Toronto ranar Juma'a,
Martin Dubravka ya koma Tottenham da tsaron raga, Tottenham
Asalin hoton, Getty Images
Gogaggen mai tsaron raga, Martin Dubravka, ya sanya hannu da kungiyar Tottenham, kamar yadda mai buga gasar Premier League ta bayyana a ranar Laraba.
Dan wasan mai shekara 37 zai koma kungiyar da Roberto De Zerbi ke jan ragama daga ranar 1 ga watan Yuli, bayan karewar kwantiraginsa da Burnley, inda ya buga wasa 35 a kakar da ta gabata.
Dubravka yana da kwarewa mai yawa a gasar Premier League, bayan da ya fara komawa Ingila tare da Newcastle United a shekarar 2018.
Ya shafe kaka bakwai a St James Park, inda ya buga wasa 179 kafin ya koma Burnley a shekarar 2025.
Haka kuma ya yi gajeren zama da buga wasannin aro a Manchester United a shekarar 2022, lokacin da kungiyar ta lashe kofin League Cup. Haka ya buga wa Slovakia wasa 60 a dukkan fafatawa.
Fenerbahce ta ɗauki ɗan kasar Senegal, Amara Diouf, Fenerbahce
Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Fenerbahce ta kasar Turkiyya ta dauki dan wasan ƙwallon ƙafa na Senegal, Amara Diouf kan kwangilar shekara biyar, kamar yadda ta sanar a ranar Laraba.
Diouf, wanda kwanan nan ya cika shekara 18 kuma yana wakiltar ƙungiyar ƙasa ta Senegal, shi ne wanda ya fi zura kwallaye a gasar cin kofin Afirka ta ƴan ƙasa da shekaru 17 (AFCON U-17) a 2023, inda ya zura kwallaye biyar tare da taimakawa wajen lashe kofin kafin koci Aliou Cissé ya zaɓe shi cikin tawagar manya.
A ranar 19 ga watan Yuni, Fenerbahce ta kuma dauki dan wasa dan ƙasar Kosovo Vedat Muriqi daga ƙungiyar Mallorca ta Spain kan kwangilar shekara uku, kamar yadda ta sanar.
Dan wasan mai shekaru 32 ya taba buga wa Fenerbahce tamaula a baya.
Ronaldinho zai koma taka leda a ƙungiyar Ravenna ta Italiya, Ronaldinho
Asalin hoton, Getty Images
Tsohon fitaccen ɗan wasan Brazil, Ronaldinho, na dab da komawa filin wasa, wanda zai koma Ravenna ta Italiya, kamar yadda ƙungiyar ta sanar a wani taro da aka gudanar a Miami a Amurka ranar Talata.
Wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or a 2005, ya bayyana tare da mai ƙungiyar Ravenna FC, Ignazio Cipriani, inda aka nuna rigar da ke ɗauke da sunansa yayin da ƙungiyar ke ƙaddamar da wani sabon shiri da take cewa zai ƙara mata samun suna a fannin taka leda a duniya.
Ronaldinho ya ce tsohuwar alaƙar abota da yake da ita da iyalan Cipriani ta taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawarar shiga ƙungiyar.
“Muna da kyakkyawar alaƙa da iyalai da kuma abokai, kuma yanzu wannan dama ce ta zo, don haka ina farin ciki matuƙa,” in ji Ronaldinho. “Muna fatan komai zai tafi daidai yadda ya kamata.”
Lokacin da aka tambaye shi irin tasirin da yake fatan zai yi ga matasa, Ronaldinho ya ce yana so labarinsa ya zama abin ƙarfafawa ga wasu masu buri irin nasa.
Shi kuwa Cipriani, wanda ya taso a Ravenna, ya ce Ronaldinho yana daga cikin waɗanda suka yi tasiri sosai ga zamaninsu.
Ronaldinho ya lashe kofin duniya a 2002 tare da Brazil, kuma ya yi fice a matakin ƙungiyoyi inda ya taka leda a Barcelona da AC Milan, wanda ya yi suna a matsayin ɗaya daga cikin ƴan wasan da suka fi kayatarwa da fasaha a tarihin ƙwallon ƙafa a duniya.
An sanar da wannan labari ne a Cipriani Miami, inda Ronaldinho ya sanya hannu, sannan aka ɗauki hotuna, kuma ya tattauna da manema labarai yayin da ake murnar sabon babban ɗan wasan da ƙungiyar ta ɗauka.
Wasu karin tarihin Ronaldo a gasar cin kofin duniya, Portugal 5-0 Uzbekistan
Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa na farko da ya ci kwallaye a gasar cin kofin duniya shida, bayan da ya zura biyu a ragar Uzbekistan a karawa ta biyu ta cikin rukuni, amma wannan ba shi ne kawai tarihin da ya kafa ba a daren jiya.
Ronaldo ya ci kwallaye 10 a gasar cin kofin duniya jimilla, wanda shi ne kan gaba tsakanin yan wasan tawagar Portugal, ya shiga gaban, Eusébio mai tara a raga.
Asalin hoton, Getty Images
'Yan wasan Crystal Palace suna haskakawa a gasar cin kofin duniya 2026, Colombia 1-0 Congo DR
Kwallon da Daniel Munoz ya ci a wasan da Colombia ta Congo DR, ita ce ta shida da dan wasan da ke taka leda a Crystal Palace ya ci a gasar cin kofin duniya ta 2026.
Munoz da Daichi Kamada na Japan da Ismaila Sarr na Senegal sun ci kwallaye biyu kowannensu a gasar.
Real Madrid ita ce kadai ƙungiyar da ƴan wasanta suka ci kwallaye fiye da na Crystal Palace, mai bakwai a raga.
Asalin hoton, Getty Images
Wasu wasa na karshe a cikin rukuni a gasar kofin duniya, Gasar kofin duniya
Group B
Bosnia-Herzegovina v Qatar da karfe 8:00 agogon Najeriya
Switzerland v Canada da karfe 8:000 agogon Najeriya
Group C
Morocco v Haiti da karfe 11:000 agogon Najeriya
Scotland v Brazil da karfe 11:000 agogon Najeriya
Group A
Czech Republic v Mexico da karfe 2:00 tsakaddare a Najeriya
South Africa v South Korea da karfe 2:00 tsakaddare a Najeriya
Yadda rukuni na 12 yake, Ingila 0-0 Ghana
Za a buga wasan karshe na uku a cikin rukuni na 12:
Asabar 27 ga watan Yuni da karfe 10:00 agogon Najeriya da Niger
Panama v Ingila
Croatia v Ghana
Asalin hoton, BBC Sport
Magoya bayan Ghana sun yi murna bayan tashi wasa ba ci da Ingila, Ingila 0-0 Ghana
Lokacin da aka busa tashi a filin wasa na Boston, tawagar Ghana da ta magoya baya, sun yi murna ganin cewa tashi wasa ba ci da Ingila tamkar nasara ce.
Asalin hoton, Getty Images
, England 0-0 Ghana
Asalin hoton, Getty Images
Mafi mallakar wasa ko taka rawa ba tare da zura kwallo ba a raga a tarihin gasar cin kofin duniya ba, England 0-0 Ghana
Ingila ta buga wasa sosai da kai matsi zuwa gidan Ghana a karawar da ta mamaye tun daga zangon farko da kuma zargo na biyu.
Ingila ta mallaki kashi 78.8 cikin 100 a taka leda a wasan - mafi girma a karawa ba tare da cin kwallo ba a tarihin gasar cin kofin duniya.
Asalin hoton, Opta BBC
England ba ta ji dadi da ta tashi ba ci da Ghana ba, England 0-0 Ghana
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Sakamakon wasannin gasar cin kofin duniya da aka buga, England vs Ghana
Ga sakamako wasannin da aka buga a gasar cin kofin duniya:
Rukunin K
Portugal 5-0 Uzbekistan
Colombia 1-0 Congo DR
Rukunin L
Ingila 0-0 Ghana
Panama 0-1 Croatia
Me ya sa ba a kori Bellingham kan rufe baki a wasan Ghana?, England 0-0 Ghana
Asalin hoton, Getty Images
Hoton da aka ga ɗan wasan Ingila, Jude Bellingham yana rufe bakinsa yayin da yake magana da Jordan Ayew na Ghana ya jawo cece-kuce.
An kafa wata sabuwar doka a gasar kofin duniya ta 2026, wadda ta ce za a iya bai wa ɗan wasa jan kati idan ya rufe bakinsa yayin da yake magana da abokin hamayya.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ne ya nemi a kafa wannan doka bayan da aka hukunta ɗan wasan Benfica Gianluca Prestianni na dakatar da shi wasa shida daga hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA saboda amfani da kalaman nuna wariya ga dan wasan Real Madrid Vinicius Jr a wani wasan Champions League a watan Fabrairu.
Dan wasan Paraguay Miguel Almiron ya zama na farko da aka bai wa jan kati a gasar kofin duniya a bana, saboda aikata laifin rufa baki a wannan laifi a wasan da suka buga da Turkiyya, inda VAR ta ba da shawarar a kore shi.
To me ya sa ba a bai wa Bellingham jan kati ba, kuma ba a duba VAR ba a wasan da suka tashi 0-0 a Boston?
Dalili ana duba yanayin da aka rufe bakin shi ne muhimmi. Rufe baki gaba ɗaya ba a haramta ba, amma yin hakan yayin rigimar ko cece-kuce ko mayar da kalamai da wani ɗan wasa ne aka haramta.
Kafin gasar, shugaban alkalan FIFA Pierluigi Collina ya bayyana a sarari cewa:
“‘Yan wasa za su iya ci gaba da rufe bakinsu da hannu ko rigarsu idan suna tattaunawa da juna.
Amma idan maganar an yi don bakanta ran abokin hamayya, rufe baki yana nuna akwai wani laifi, kuma hukuncinsa jan kati ne.”
Me yasa jan katin Almiron ya bambanta?
A kusan kowane wasa a wannan gasar, za ka ga ƴan wasa suna magana suna rufe bakinsu — har ma alkalai ma suna yin hakan.
Abu mafi muhimmanci shi ne, babu fadin kalaman wariya ko rikici tsakanin Bellingham da Ayew — kawai suna tattaunawa ne a tsakaninsu, wannan ba laifi bane.
To me ya bambanta da na Almiron?
Yanayin wasan ne ya bambanta:
Dan wasan Paraguay Isidro Pitta ya fadi kasa, yana zargin Ismail Yuksek na Turkiyya ya yi masa keta
Wannan ya jawo hayaniya tsakanin ƴan wasa daga bangarorin biyu. A nan ne Almiron ya rufe bakinsa yayin da yake magana da Mert Muldur.
Ko da yake ba su yi rikicin kai tsaye ba, amma wasan ya shiga yanayi mai zafi da fuskantar kalubale.
Ronaldo ya zama wanda ya ci ƙwallo a kowacce gasa shida a kofin duniya, Cristiano Ronaldo
Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo ya samun zura ƙwallo a karon farko a gasar cin kofin duniya a 2026, inda ya ci kwallo mintuna shida da fara wasan Portugal da Uzbekistan a ranar Talata a Houston, wanda hakan ya sa ya zama ɗan wasa na farko a tarihi da ya zura ƙwallo a gasar kofin duniya har sau shida daban-daban.
João Cancelo ya kutsa ta gefen dama ya aika da ƙwallo cikin gidan Uzbetistan, wadda ta je ƙafar Ronaldo daidai a layin yadi na shida, inda ya buga ta kai tsaye ta wuce mai tsaron ragar, Abduvohid Nematov.
Ronaldo, wanda ya fara zura kwallo a gasar kofin duniya tun a shekarar 2006, ya kuma zama na biyu mafi tsufa da ya zura kwallo a tarihin gasar yana da shekaru 41. Wanda ya fi shi tsufa shi ne Roger Milla na Kamaru wanda ya yi hakan yana da shekaru 42 a shekarar 1994.
Ronaldo ya ƙara kwallo ta biyu a minti na 39, wanda ya bai wa Portugal jagoranci da ci 3-0. Bruno Fernandes ne ya ba shi wata ƙwallo a gefen dama a gidan Uzbekistan, inda Ronaldo ya zura ta cikin kusurwar hagun ragar.
Wannan bajintar ta Ronaldo ta jawo farin ciki da kwanciyar hankali ga Portugal, musamman bayan sukar da tawagar ta fuskanta bayan kunnen doki 1-1 da DR Congo a wasan farko, tare da tambayoyi kan ko Ronaldo ya kamata ya kasance muhimmin ɗan gaba a wasanninta.
An tashi wasan, inda Portugal ta sharara 5-0 a ragar Uzbekistan.
Ga jerin ƴan wasan tawagar Ingila da suka buga gasar kofin duniya sau uku, wadda ta ɗauki kofin sau ɗaya a tarihi.
Tom Finney (1950, 1954, 1958)
Billy Wright (1950, 1954, 1958)
Bobby Moore (1962, 1966, 1970)
Bobby Charlton (1962, 1966, 1970)
Peter Shilton (1982, 1986, 1990)
Terry Butcher (1982, 1986, 1990)
Bryan Robson (1982, 1986, 1990)
Sol Campbell (1998, 2002, 2006)
David Beckham (1998, 2002, 2006)
Michael Owen (1998, 2002, 2006)
Ashley Cole (2002, 2006, 2010)
Joe Cole (2002, 2006, 2010)
Steven Gerrard (2006, 2010, 2014)
Frank Lampard (2006, 2010, 2014)
Wayne Rooney (2006, 2010, 2014)
Raheem Sterling (2014, 2018, 2022)
Harry Kane (2018, 2022, 2026)
Jordan Pickford (2018, 2022, 2026)
John Stones (2018, 2022, 2026)
Marcus Rashford (2018, 2022, 2026)
Asalin hoton, Getty Images
Su wanene suka halarci gasar kofin duniya da yawa?, Gasar kofin duniya
Gasar cin kofin duniya 6:
Lionel Messi da Cristiano Ronaldo (2006, 2010, 2014, 2018, 2022, 2026)
5 gasar cin kofin duniya:
Manuel Neuer (2010, 2014, 2018, 2022, 2026)
Luka Modric (2006, 2014, 2018, 2022, 2026)
Lothar Matthaus (1982, 1986, 1990, 1994, 1998)
4 Gasar cin kofin duniya:
Miroslav Klose (2002, 2006, 2010, 2014)
Paolo Maldini (1990, 1994, 1998, 2002)
Diego Maradona (1982, 1986, 1990, 1994)
Asalin hoton, Getty Images
Yadda rukuni na 10 yake, saura wasa ɗaiɗai ya rage, Rukuni na 10
Lahadi 28 ga watan Yuni
Algeria v Austria
Jordan v Argentina
Asalin hoton, BBC Sport
Mbappe ya zama na biyu a yawan cin ƙwallaye a gasar kofin duniya, Faransa
Kylian Mbappe ya zura kwallaye biyu, wanda ya kai shi matsayi na biyu a tarihin masu yawan cin kwallaye a gasar kofin duniya, yayin da Faransa ta doke Iraq a wasan da aka jinkirta saboda rashin ƙyawun yanayi a Philadelphia.
Mbappe ya zura kwallo a zangon farko da kuma na biyu, wanda ya kai jimillar yana da 16 a raga, kenan yana da tazarar biyu tsakani da Lionel Messi, wanda ke kan gaba da 18 a raga, wanda ya haura tarihin da Miroslav Klose ke rike da shi.
Wasan Faransa da Iraq shi ne na farko a wannan gasar kofin duniya da aka dakatar saboda rashin ƙyawun yanayi, inda aka fara zango na biyu fiye da sa’o’i biyu, sakamakon tsawa da walƙiya da suka faru a yankin.
Ruwan sama mai yawa da aka yi tun da fari a ranar ya kuma jinkirta shigar magoya baya zuwa filin wasan Philadelphia, duk da cewa an fara wasan akan lokaci.
Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta ɗauki Abdelkarim daga Al Ahly, Barcelona
Barcelona ta ɗauki ɗan wasan tawagar Masar, Hamza Abdelkarim bisa kwantiragin kaka uku, kamar yadda ƙungiyar da ke buga LaLiga ta sanar ranar Talata.
Matashin ɗan wasan mai shekaru 18 ya koma Barcelona ne a kan aro daga Al Ahly a lokacin kasuwar saye da sayar da ƴan wasa ta hunturu, tare da zaɓin sayensa idan ya taka rawar gani a karshen kaka.
Abdelkarim ya zura kwallo shida a wasanni 11 da ya buga wa ƙungiyar Barcelona ta ƴan ƙasa da shekaru 19.
Ɗan wasan Masar zai koma ƙungiyar domin sanya hannu kan yarjejeniyar kaka uku da za ta kare har zuwa 30 ga watan Yuni 2029.
A halin yanzu Abdelkarim yana cikin tawagar Masar da ke buga gasar kofin duniya ta 2026 da ake yi a Amurka da Mexico da kuma Kanada, inda ya taka rawa a wasa na biyu da Masar ta buga da Belgium da kuma New Zealand.