Ƙasashen da aka fitar da su daga Gasar Kofin Duniya

Asalin hoton, Getty Images
Zuwa yanzu an fara fitar da tawagar wasanni ƙasashe daga Gasar Kofin Duniya ta 2026 da ke gudana a Amurka da Mexico da Kanada.
Ƙasashe 48 ne ke fafatawa a gasar, inda kowa ke neman tikitin zuwa zagayen gaba na kifa ɗaya ƙwala ta hanyar samun maki a wasannin rukuni.
Ga jerin ƙasashen da aka cire zuwa yanzu.
Tunisia

Asalin hoton, Getty Images
An cire Tunisia daga gasar ne bayan da Japan ta doke ta da ci 4-0 a wasan da suka buga a Monterrey ranar Lahadi.
Tun da farko Tunisia ta sha kashi da ci 5-1 a hannun Sweden a wasan farko na rukuni na F.
Tun a wasansu na farko ne dai aka kori kocin su Sabri Lamouchi, inda aka naɗa Hervé Renard da tunanin za su ga sauyi.
Sai dai da alama daga nan za su yi bankwana da gasar Kofin Duniya na 2026.
Sakamakon rashin samun ko maki ɗaya a wasanninta biyu na farko ya tabbatar da cewa ba za ta iya kaiwa zagayen ƴan 32 ba, duk da cewa akwai wasa guda ya rage mata a matakin rukuni.
Haiti

Asalin hoton, Getty Images
A rukuni na C kuwa, zakarun duniya sau biyar Brazil sun lallasa Haiti da ci 3-0 a birnin Philadelphia.
Wannan sakamako ya tabbatar da ficewar Haiti daga gasar bayan da ta kasa samun ko maki ɗaya a wasanni biyu.
A wasansu na farko dai Scotland ce ta ci su 1-0.
Ƙasar ce take ƙarshen teburin rukuni da bambancin ƙwallaye, lamarin da ya sa wasanta na ƙarshe da Morocco a ranar 24 ga Yuni zai zama wasan cike gurbi ne kawai.
Turkiya

Asalin hoton, Getty Images
A rukuni na D kuma, Türkiye ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Paraguay a wasan da aka buga a filin wasa na San Francisco Bay Area Stadium.
Shan kashi sau biyu a jere ba tare da samun maki ba, lamarin da ya tabbatar da ficewar ƙasar daga gasar tun kafin ta buga wasanta na ƙarshe a rukuni.
Turkiya ta sha kashi a hannun Australia da ci 2-0 a wasansu na farko.
Wasan da ya rage mata na ƙarshe shi ne wanda za ta fafata da Amurka.
Jordan

Asalin hoton, Getty Images
A Rukunin J Algeria ta doke Jordan da ci 2-1 a wasansu da aka fafata a filin wasan San Francisco Bay inda suka fitar da ita daga gasar cin kofin duniya.
A baya bayan nan ta sha kashi a hannun Austria da ci 3-1 a wasan farko na gasar, kuma wannan sakamakon ya sa sun kasance a kasan rukunin inda ba su da maki ko ɗaya bayan wasanni biyu, wanda hakan ke nufin ba za su iya tsallakewa zuwa zagaye na gaba ba.
Yanzu a wasan ta na gaba za ta kara ne da Argentina mai riƙe da kambun gasar, wanda ita ke jan ragamar rukunin kuma ta riga ta tsallaka zuwa zagaye na gaba a gasar.
Panama

Asalin hoton, Getty Images
A rukunin L an yi waje da Panama daga gasar bayan da Croatia ta ci gaba da yunƙurinta na tsallakawa zuwa zagaye na ƴan 32 inda ta doke ta da ci 1-0 a ranar Talata a filin wasan birnin Toronto.
Wannan rashin nasara shi ne karo na biyu a jere da Panama ta sha kashi a matakin rukuni na wannan gasar kuma ya tabbatar da cewa ba za ta iya tsallakewa zuwa zagayen gaba ba bayan ta sha kashi da ci ɗaya mai ban haushi a hannun Ghana a wasanta na farko a rukunin.
Panama har yanzu tana neman makin ta na farko, bayan buga wasanni biyar a tarihin gasar cin kofin duniya.
A ranar Juma'a ne za ta kara da Ingila a wasan ta na ƙarshe a gasar bana.











