Me ya sa Birtaniya ke yawan sauya Firaminista?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Rob Watson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, UK political correspondent, BBC World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Yanzu dai Sir Keir Starmer shi ne firaminista na shida da ya yi murabus ko kuma masu jefa ƙuri'a suka tilasta mi shi yin murabus cikin shekara 10.
Idan ana kokwanto, wannan ba al'ada ba ce a siyasar Burtaniya ba. Idan ba ku gamsu ba, ku yi la'akari da wannan: tun lokacin da aka ƙirƙiri muƙamin firaminista a ƙarni na 18, kowanne yana kai wa kimanin shekara biyar a kan karagar mulki,
A cikin shekaru goma da suka gabata, hakan ya ragu zuwa watanni 18!
Ko me ya haddasa wannan baban sauyi mai ban mamaki? Tabbas, akwai dalilai na musamman a kowanne daga cikin shugabannin guda shida.
David Cameron ya yi murabus ne bayan ya kira ya kuma ya sha kaye a zaɓen raba gardama na ko ƙasar za ta fice daga ƙungiyar tarayyar Turai a shekarar 2016.
Ita ma Theresa May rikicin Brexit ne sanadiyar murabus ɗin ta, inda ƴan majalisar suka sha yin watsi da shirinta na ƙulla sabuwar alaƙa tsakanin Burtaniya da Tarayyar Turai har sai da ta kasa ci gaba da riƙe muƙaminta.
Sbi kuma Boris Johnson an tilasta masa tafiya ne saboda halayensa da mutuncinsa da kuma yanayin yadda ya yanke hukunci kan wasu baututuwa, inda ƴan majalisar daga jam'iyyarsa ke ganin cewa zai iya kawo ma jam'iyyar cikas a manyan zaɓukan ƙasar, akasin taimaka mata da ya yi a baya.
Liz Truss ta samu matsala ne sakamakon martanin da kasuwannin hada-hadar kuɗi suka yi game da shirinta na rage haraji ba tare rage kashe kuɗaɗe don cike gurbin da yin hakan zai bari.
Ɗan jam'iyyar Conservatives na ƙarshe a jerin sunayen, Rishi Sunak, shi ne kaɗai aka cire a zaɓen da masu kaɗa ƙuri'a suka kore shi bayan sun gaji da shekara 14 a ƙarƙashin gwamnatocin Conservative.
Shi kuma baya-bayan nan, Sir Keir, zai tafi ne saboda ya rasa goyon bayan ƴan majalisar wakilai daga jam'iyyar Labour, wadanda suka yi imanin cewa rashin farin jininsa na kawo babbar barazana ga jam'iyyarsu.
Amma baya ga wadannan dalilan da suka yi sanadiyar tafiyar waɗannan shugabannin , da alama akwai waɗansu abubuwan da ke gudana a cikin Burtaniya wanda ke sa siyasarta ta ƙara zafi kuma masu jefa ƙuri'a sun zama marasa hakuri.
To me kuma ke faruwa?
Rashin gamsuwar al'umma
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙuri'un jin ra'ayoyin jama'a, da sauran bayanan da ake tattarawa sun nuna cewa masu jefa ƙuri'a na gani kamar ƴan siyasa ba sa la'akari da wasu muhimman abubuwan da ke haifar da rashin jin daɗi da rashin gamsuwa a tsakanin al'umma.
Na farko shi ne munin yanayin rayuwa. Wannan lamari mai raɗaɗi ya samo asali ne tun lokacin da duniya ta fuskanci barazanar tattalin arziki a 2008.
Don haka yayin da muke duban dalilan da su ka sa Birtaniya ta sami Firaminista shida tun daga 2016, za mu iya fara duba wa daga wannan lokacin.
Kuma domin fahimtar tsanannin munin wannan yanayi ya kamata a yi la'akari da cewa, yanayin rayuwa shiga irin wannan yanayin ba ba tun lokacin yƙkin Napoleon a farkon ƙarni na 19.
Idan mutane na fama da matsalolin rashin kuɗi kuma suna ganain kamar cewa gwamnatoci ba su da niyyar cika alƙawarin nan na cewa al'ummar da za ta zo nan gaba sai ta fi ta baya jin dadi ba abin mamaki ba ne a ga cewa yanayin tunanin al'ummar ya fara muni.
Abin da ke damun duk wani ɗan siyasa, ƙuri'a jin ra;'ayin jama'a na nuni da cewa taɓarɓarewar tattalin arziki tana matsayi mafi girma tun shekara ta 1978 lokacin da ake fama da tsananin hauhawar farashin kayayyaki da kuma rikicin masana'antu.

Asalin hoton, PA Media
Abu na biyu shine tunanin cewa babu wani abu da ke aiki da kyau a Burtaniya, tunanin da ake yi cewa abubuwan da ake yi wa jama'a, kamar su sufuri da tabbatar da adalci da sauransu.
Wannan ba shakka a wani ɓangare ne sakamakon ƙarancin ci gaban tattalin arziki da ke haifar da matsin rayuwa.
A wannan yanayin, rashin samun ci gaba yana hana gwamnatocin da suka biyo baya daga samun kuɗaɗen shiga don saka hannun jari a cikin abubuwan more rayuwa da sauran abubuwan da mutane ke darattawa kamar ilimi da kiwon lafiya.
Abu na uku shi ne damuwar da ake fama da ita game da haɗin kan jama'a, ko kuma a ce rashin sa.
Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna sama da kashi 80% na mutane na ganin akwai rarrabuwar kawuna tsakanin ƴan ƙasar.
Mutane da yawa kuma suna jingina wannan matsala ta rarrabuwar kawuna a kan kwararowar bakin haure cikin ƴan shekarun nan.
Kuma, yawancin masu jefa ƙuri'a suna tunanin Firaministoci na baya-bayan nan ba sa fahimtar fushin su game da yadda suke jin cewa Burtaniya ta sauya.
Idan za a duba lamarin ta wani fannin, Burtaniya, kamar sauran ƙasashen Turai, har yanzu tana kokawa game da tambayar kan yadda dukkanmu za mu yi mu'amala da tare yayin da mu ka kasance al'umma da ƙabilu daban-daban.
Wataƙila ɗayan abin da ya sauya, kuma Burtaniya ba ta da bambanci a cikin wannan, shine ba kawai mutane suna fushi game da abubuwa ba ne, amma yanzu ba sa kunyar nunawa ne.
Ko laifin shafukan sada zumunta ne ko kuma wasu dalilai, jama'a na nuna kyama ga daidaikun ƴan siyasa ciki har da firaministan ƙasar, ta yadda da ba a taɓa tunani ba a shekarun baya.
Wahalar jagoranci

Asalin hoton, Getty Images
Shin yanzu ƙasar ta zama mai wuyan mulki ke nan- shin me ya sa muke daf da samun Firaminista na bakwai a cikin shekara 10?
Yawancin ƴan siyasa ba za su yi hanzarin cewa haka ba. Sun ce yayin da mulki ya ƙara wahala a duniya da ke cike da sarƙaƙiya inda al'ummomi suka rarrabu, ba abu ne mai yiwuwa ba.
Amma yayin da firaminista shida yanzu suka gaza fitar da ƙasar daga wannan ƙangin rashin kyautata kyakkyawar zato da yan ƙasar ke ciki nan tun bayan barazanar tattalin arziki na shekara ta 2008 da ƙuri'ar raba gardama ta Brexit a shekara ta 2016, ba shakka za a yi shakku kan ko firaminista na bakwai, ko ma wa nene shi, zai samu sa'ar yin hakan fiye da magabatansa.











