Ukraine ta kai hari kan tashoshin wutar lantarki a Crimea

Asalin hoton, Reuters
Wani hari da jiragen saman Ukraine suka kai kan yankin Crimea da Rasha ta mamaye ya haifar da katsewar wutar lantarki a babban birninsa, Sevastopol, in ji gwamnan da Moscow ta naɗa Mikhail Razvozhayev.
Ukraine ta ce jiragenta marasa matuƙa sun kai hari a babban tashar wutar lantarki a birnin a cikin dare a ranar Talata.
Razvozhayev ya yi gargaɗin cewa wasu yankuna za su kasance cikin dudhu har zuwa yammacin Laraba.
Kyiv dai na ci gaba da kai hare-hare kan tashoshin wutar lantarki a yankunan da Rasha ke riƙe da su domin lalata hanyoyin da Rasha ke samun kuɗaɗen shiga da kuma ƙoƙarin tilasta wa shugaba Putin ya zauna kan teburin tattaunawa.
Birnin Sevastopol mai tashar jiragen ruwa muhimmin birni ne da ke taimakawa tattalin arziki yankin.























