BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Ko har yanzu akwai damar yin haɗaka tsakanin ƴan'adawar Najeriya?
A cikin watannin baya-bayan nan, an ga wasu fitattun ƴan siyasa da ƙungiyoyin matasa na gudanar da tattaunawa kan samar da wata gamayya da za ta haɗa ƙarfi da ƙarfin da ke faɗin ƙasar.
Arsenal na sa ido kan Mora, AC Milan na harin Endrick
Arsenal na sa ido kan Gilberto Mora, sai AC Milan da ke harin Endrick, Nottingham Forest na son Murillo.
Yadda za ku gane ko kuna fama da matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa
Kowane ɗan'adam yana da abin da kan tantance lafiyar ƙwaƙwalwarsa. Ya ƙunshi jin daɗin zukatanmu da zuciyarmu da tunani, da zamantakewa, kuma yana shafar yadda muke tunani, da ji, da kuma gudanar da ayyukan yau da kullum.
Shin Saudiyya na son rage yawan dogaro da Amurka ta fuskar tsaro?
A cikin ƴan shekarun nan, Riyadh ta fahimci cewa ƙididdigar Washington kan harkokin tsaro na sauyawa bisa canjin gwamnatoci da manufofinsu, lamarin da ya sa ya zama da wuya a ci gaba da dogaro gaba ɗaya kan tabbacin tsaron da Amurka ke bayarwa.
Atiku ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa na 2027
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Juma'a 9 ga watan Oktoban 2026
Sabbin hanyoyi 4 da Tinubu 'zai rage raɗaɗin' cire tallafin mai
Fiye da shekara uku bayan cire tallafin mai a Najeriya, tsadar fetur na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar gidaje, masu sana'o'i da masu harkokin sufuri.
Wane ne tsohon sojan Amurkan da za a nuna zartar da kashe shi kai tsaye?
An samu Nidal Hasan da laifin ya harbe tare da kashe sojojin Amurka 13 da ba su ɗauke da makami a sansanin soji na Fort Hood a shekara ta 2009, sannan ya jikkata wasu mutum 32.
'Da dala muka biya kuɗin fansa kafin a sako yaranmu'
Ɗaya daga cikin iyayen matasa masu hidimar ƙasa (nysc) 20 da aka saki bayan an yi garkuwa da su a jihar Imo, Kudu maso gabashin Najeriya ya shaida wa BBC cewa masu garkuwa da yaran sun karɓi kudin fansa da dalar Amurka kafin sakin matasan.
Me shirin gwamnati na rage farashin man fetur ya ƙunsa?
A aikace, idan NNPCL ta sayi ko ta shigo da fetur kan N1,300 a lita, za ta sayar wa masu amfani da shi a wannan farashin ko kusa da shi ba tare da ɗora ribar da take sakawa a baya ba.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Hantsi, 06:30, 10 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 10 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Ra’ayi Riga, 19:29, 9 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 1,00,00
Shiri ne a duk ranar Juma'a da ke baiwa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 9 Oktoba 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Mourinho ya ce masu sukar Mbappe abin dariya ne
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin kai tsaye a BBC Hausa daga 5 zuwa 10 ga watan Oktoban 2026.
Madrid na son McTominay, Chelsea na son Frenkie de Jong
Real Madrid na harin tsohon dan wasan Manchester United Scott McTominay, da Michael Olise, yayin da Chelsea ke son Frenkie de Jong.
United da Liverpool na son Truffert, Arsenal ta dage kan Alvarez
Manchester United da Liverpool na harin Adrien Truffert, Newcastle na son Tyler Morton yayin da Martin Odegaard na cikin jerin manyan ƴan wasan da ke shirin sabunta kwantaraginsu da Arsenal.
Yadda Messi ya yi bankwana da Argentina cikin hawaye
Tawagar Argentina ta yi bikin ban kwana da Lionel Messi, bayan ritaya daga buga mata wasanni, wanda ke kan gaba a ci mata kwallaye a tarihi.
'Abu uku da Messi zai yi bayan ritaya daga ƙwallon ƙafa'
Messi zai buga wa Argentina wasan karshe a wasan sada zumunci da Benin. BBC Sport ta duba menene abu na gaba ga ɗan wasan mai shekara 39?
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Me ya sa aka kafa ƙungiyar Izala, kuma mene ne aƙidunta?
Izala na daga cikin manyan ƙungiyoyin addinin Musulunci da suka yi tasiri sosai kan harkokin wa'azi, ilimi da rayuwar addini a arewacin Najeriya cikin shekaru da dama.
Biranen duniya 10 mafiya ƙayatarwa a 2026
Rahoton Oxford Economics World Cities Index na 2026 ya bayyana matsayin birane 1,000 a duniya, bisa la'akari da wasu muhimman fannoni guda biyar: shugabanci da tattalin arziki da albarkatun ɗan Adam da muhalli da kuma ingancin rayuwa.
Yadda BBC ta gano gidan Putin na gaɓar teku da ake yi wa gyara na sirri
Wannan wuri ne mai natsuwa da salama da ke birnin Sochi. A tarihi, manyan shugabannin Tarayyar Soviet da Rasha irin su Nikita Khrushchev da Leonid Brezhnev da kuma Boris Yeltsin, wanda ya jagoranci Rasha bayan rushewar Tarayyar Soviet, sun yi amfani da wurin.
Gwamnatin Najeriya za ta rage farashin man fetur na wata ɗaya
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Alhamis 8 ga watan Oktoban 2026
Motsa jiki 5 da za su kare ku daga samun matsala a wuyanku
Yana da kyau lokaci zuwa lokaci a dinga duba irin nauyin da ke kan ɗan'adam.
Wane ne Nana Patekar, fitaccen jarumin fina-finan Indiya da ya rasu?
Patekar na daga cikin fitattun jaruman da suka yi shuhura a harkar fina-finan Indiya. Ya lashe Kyautar Fina-finai ta Ƙasa ta Indiya (National Film Award) har sau uku, kuma an san shi da taka rawar jaruman da ke da sarƙaƙiya, waɗanda galibi suke da zafin hali. Ya kuma taka muhimmiyar rawa a fina-finan Marathi da kuma wasan kwaikwayo na dandali.
Sir Wicknell: Attajirin da ya mutu ya bar baya da ƙura
Wicknell Chivayo, attajirin ɗan Zimbabwe da ya rasu a makon jiya tare da matarsa Lucy Muteke a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu, mutum ne da ya raba kan jama'a tsakanin masu yabonsa da masu sukar sa tun yana raye, kuma har bayan rasuwarsa ana ci gaba da muhawara a kansa.
Shin sulhun Sanata Barau da Abba Bichi zai ɗore?
Taron sulhun wanda ya gudana a Abuja a ranar Laraba, mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature ya ce shugabannin biyu sun samu damar tattauna saɓanin da ke tsakaninsu.
Ƴansiyasa 5 da suka yi wa Tinubu alƙwarin miliyoyin ƙuri'u a 2027
Daga arewacin ƙasar zuwa kudanci, an ji alƙawuran da suka kai miliyoyin ƙuri'u, yayin da wasu masu ruwa da tsaki ke cewa za su tabbatar da gagarumar nasara ga shugaban ƙasar.
Ƙasashen da Amurka ta yi amfani da sansanonin sojinsu a yaƙin Iran
Muhimmancin sansanin Fairford shi ne tun daga farkon yaƙin baya-bayan nan, ya zama sansanin da aka yi amfani da shi kai tsaye wajen ayyukan Amurka a cikin yankin Iran.
Yadda kogi ya tafi da yara uku ƴan gida ɗaya a Abuja
Wani mummunan ibtila'i ya auku a yankin Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja, inda wasu yara uku 'yan gida ɗaya suka rasa rayukansu bayan ruwa ya tafi da su a wani kogi.
Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan ISWAP 25 a tafkin Chadi
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Laraba 7 ga watan Oktoban 2026
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































