Manchester United na harin Toney, Fulham na neman tsawaita zaman Bassey

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na zawarcin ɗan wasan gaba na Ingila, Ivan Toney, wanda ke buga wa Al-Ahli wasa, domin ɗaukar sa a watan Janairu; sai dai wasu ƙungiyoyin gasar Premier League ma na zawarcin ɗan wasan mai shekara 30. (TeamTalk)
Ana danganta ɗan wasan baya na Najeriya, Calvin Bassey, da komawa Manchester United, amma ɗan wasan mai shekara 26 ya bayyana cewa yana tattaunawa kan tsawaita kwangilarsa da Fulham. (Standard)
Arsenal da Chelsea duk suna da sha'awar ɗaukar kocin Como, Cesc Fabregas — wanda ya taɓa buga wa kungiyoyin biyu na Landan wasa — a matsayin sabon kocinsu. (Football Insider)
Ɗan wasan tsakiya na Liverpool da Argentina, Alexis Mac Allister mai shekara 27, na matuƙar son sanya hannu kan sabuwar kwangila a Anfield, kuma tattaunawar ta samu ci gaba sosai. (Football Insider)
Arsenal da Liverpool duka suna da sha'awar Ɗaukar Jamal Musiala, Ɗan wasa mai shekarA 23, kuma za su iya Ɗaukar matakin neman ɗan wasan tsakiyar na Jamus, wanda makomarsa a ƙungiyar Bayern Munich ke tangal-tangal. (Talksport)
Paris St-Germain na iya ƙara ƙaimi wajen neman ɗan wasan gaba na Bournemouth, Eli Junior Kroupi, ɗan ƙasar Faransa mai shekara 20, bayan da abokin wasansa a tawagar ƙasa, Desire Doue mai shekara 21, ya samu mummunan rauni a gwiwa. (TeamTalk)
An danganta mai tsaron gidan Schalke 04, Loris Karius, da komawa Bayern Munich, amma ɗan wasan na Jamus mai shekara 33 ya bayyana cewa bai tattauna da kowa ba game da batun sauya ƙungiya. (Sky Sports Germany)
AC Milan ta fi nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaba na Real Madrid da Brazil, Endrick mai shekara 20, fiye da yunƙurin ɗaukar Nicolo Tresoldi, dan wasan matasan Jamus mai shekara 22 da ke buga wa Club Brugge wasa. (Gazzetta dello Sport)

























