Raunin da Raya ya ji ba mai muni bane in ji Arteta, Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta tashi 2-2 a gidan Newcastle United a wasan mako na 11 a Premier League.
A karawar ce mai tsaron ragar Arsenal, David Raya ya ji rauni da ta kai an sauya shi a fafatawar.
An yi ta fargabar cewar Raya zai yi jinya mai tsawo, kafin ya koma taka leda, to sai dai bayan gwaje-gwajen da aka yi masa, an ce raunin bai yi muni ba.
Ga abinda kociyan Arsenal, Mikel Arteta ya ce
"Abin takaici ba zai kasance cikin shirinmu na gobe ba saboda bai kai ga samun cikakkiyar lafiya ba. Amma alamu na nuna cewa matsalar ba ta da tsanani sosai. Muna buƙatar ƙarin gwaje-gwaje, amma abin fargaba ne idan aka yi la’akari da irin radadin da yake ji nan take bayan faruwar lamarin.
Dukkanmu mun damu sosai a lokacin, amma yanzu da alama yanayin ya fi yadda muka yi tsammani kyau."
