Ƴan ƙwallo 6 da suka mutu bayan faɗuwa a filin wasa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Mutuwar ɗan wasan gaba na Tenerife, Jesus de Miguel, a baya-bayan nan ta dawo da tunanin wasu munanan abubuwan da suka faru a filayen wasan ƙwallon ƙafa a sassa daban-daban na duniya.

Ɗan wasan ya yi karo da mai tsaron ragar ƙungiyar da suke fafatawa ne a tsakiyar fili, lamarin da ya sa nan take ya faɗi, abin da ya sa aka garzaya da shi asibitin inda a can ne ya mutu.

Ƙwallon ƙafa wasa ne da ke haɗa miliyoyin mutane a faɗin duniya, amma wani lokaci farin cikin magoya baya kan koma babban baƙin ciki idan ɗan wasa ya faɗi a filin wasa kuma ya kasa sake tashi.

A tsawon tarihin wasan, akwai ƴan wasan da suka rasa rayukansu yayin da suke yin abin da suka fi so, wato buga ƙwallon ƙafa.

A wannan muƙala mun duba wasu ƴanƙwallo shida da suka mutu yayain da suke fafatawa a tsakiyar fili.

Jesus de Miguel - 2026

De Miguel, mai shekara 30, ya rasu ne a ranar Talata, 3 ga Nuwamban 2026, bayan ya samu munanan raunuka a wasa na rukuni na biyu na ƙasar Spain da aka buga tsakanin Tenerife da FC Andorra.

Ya samu raunukan ne bayan wani mummunan karo da mai tsaron ragar abokan hamayya, Jesus Owono.

Lamarin ya sanya De Miguel cikin jerin ƴan wasan da suka rasa rayukansu sakamakon abubuwan da suka faru yayin wasa.

Juan Izquierdo - 2024

Juan Izquierdo ya kasance ɗan wasan baya na ƙungiyar Nacional na ƙasar Uruguay.

Ya rasu a ranar 27 ga Agustan 2024 yana da shekara 27 a duniya, bayan ya faɗi kwatsam a lokacin wasan Gasar Copa Libertadores tsakaninsu da ƙungiyar São Paulo ta ƙasar Brazil.

Lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Agustan 2024, yayin wasan zagaye na 16 na gasar.

Izquierdo ya faɗi a filin wasa bayan ya kamu da bugun zuciya, lamarin da ya sa aka garzaya da shi asibiti domin yi masa gaggawar magani.

Duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi, yanayinsa jikinsa ya munanan, inda cikin ƴankwanaki ya rasu sakamakon tsayawar aikin zuciya da numfashi, yanayin da ke da alaƙa da matsalar bugun zuciya ba yadda ya kamata ba.

Phil O'Donnell - 2007

Phil O'Donnell kyaftin ne na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Scotland, Motherwell, kuma gogaggen ɗan wasan tsakiya ne wanda ya taka leda a ƙungiyoyin Celtic da Sheffield Wednesday.

Ya rasu ne a ranar 29 ga Disamban 2007 yana da shekara 35, bayan ya faɗi a filin wasa yayin wasa da Dundee United.

Lamarin ya faru ne a mintunan ƙarshe na wasan yayin da Motherwell ke kan gaba da ci 5-3.

O'Donnell na shirin fitowa daga wasan bisa umarnin mai horar da shi lokacin da ba zato ba tsammani ya faɗi kafin a kammala canjin ɗan wasan.

Ma'aikatan jinya na gaggawa sun ba shi agajin farko a filin wasa na kusan minti biyar kafin a kai shi motar asibiti da ke jiran sa a wajen filin wasan, sai duk da haka ya mutu, sakamon abin da likitoci suka bayyana da bugun zuciya.

Antonio Puerta - 2007

Antonio Puerta na ɗaya daga cikin fitattun matasan ƴan wasan ƙwallon ƙafa a ƙasar Spain.

Yana cikin tawagar Sevilla da ta lashe gasar UEFA Cup a shekarar 2007.

A ranar 25 ga Agustan 2007, yayin wasan La Liga da Getafe, Puerta ya faɗi a filin wasa bayan ya kamu da bugun zuciya.

An ba shi taimakon gaggawa a wurin sannan daga bisani aka kai shi asibiti, amma yanayinsa ya ci gaba da taɓarɓarewa.

Bayan kwana uku, ya rasu yana da shekara 22 a duniya sakamakon gaza aiki na wasu sassan jikinsa bayan doguwar matsalar tsayawar aikin zuciya.

Cristiano Junior - 2004

Ɗan wasan Brazil mai shekara 25 a lokacin, wanda kuma shi ne ɗan wasan ƙwallon ƙafa mafi yawan albashi a Indiya a wancan lokaci, ya yi karo da mai tsaron ragar ƙungiyar abokan hamayya yayin da yake zura ƙwallo wa ƙungiyarsa ta Dempo, saura minti 12 a tashi daga wasan ƙarshe na gasar Federation Cup ta 2004 a Bangalore.

Junior, wanda ya koma Indiya da burin samun isassun kuɗaɗen da zai gina wa mahaifiyarsa gida a ƙasarsu ta haihuwa, Brazil, ya faɗi kuma ya suma.

Ya dai samu taimakon gaggawa daga abokin wasansa na gaba a ƙungiyar, Santi Martins, ɗan Najeriya.

Martins ya kasance a gefensa har sai da motar asibiti ta ɗauke shi zuwa asibiti.

Sai dai an tabbatar da mutuwarsa da isarsa asibitin, bayan ya samu bugun zuciya.

Marc-Vivien Foé - 2003

Marc-Vivien Foé ɗan wasan tsakiya ne daga ƙasar Kamaru wanda ya kuma taka leda a ƙungiyoyin Manchester City, West Ham United da Lyon.

Ya rasu a ranar 26 ga Yunin 2003 yana da shekara 28 a duniya, a wani lamari da ya kasance cikin mafi girman firgici a tarihin ƙwallon ƙafar ƙasashen duniya.

Lamarin ya faru ne yayin da ƙungiyar Kamaru ke wasa da Colombia a wasan kusa da na ƙarshe na gasar FIFA Confederations Cup da aka gudanar a birnin Lyon na ƙasar Faransa. Foé ya faɗi kwatsam a tsakiyar wasan bayan ya kamu da bugun zuciya.

Ma'aikatan agajin gaggawa sun garzaya wurinsa tare da ƙoƙarin ceto rayuwarsa ta hanyar yi masa matsawar kirji (CPR) da kuma ba shi iskar oxygen.

An ci gaba da ƙoƙarin dawo da bugun zuciyarsa na kusan minti 45, amma ba a samu nasara ba. Daga baya aka tabbatar da rasuwarsa.