Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su wane ne za su ci gajiyar tallafin N50,000 na gwamnatin Najeriya?
Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin tallafin kuɗi na wata-wata domin rage raɗaɗin tsadar rayuwa da ke ƙaruwa.
A cikin shirin tallafin da Ma'aikatar Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci ta sanar a wata sanarwa ranar Juma'a 30 ga Oktoba, ta ce gwamnati za ta riƙa bai wa kowane gida naira 50,000 a duk wata.
Ministan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Bernard Doro, ya ce shirin bayar da tallafi NERSI wani yunƙuri ne na shugaban ƙasa da aka tsara domin bayar da taimakon kuɗi cikin gaggawa ga miliyoyin 'yan Najeriya masu rauni.
A cewarsa, an ƙaddamar da shirin ne domin sassauta tasirin hauhawar farashin abinci da sauran muhimman kayayyaki.
Tsadar kayayyakin da ke ƙaruwa a faɗin duniya na ci gaba da matsa wa al'ummar Najeriya lamba.
Su wane za su amfana kuma ta yaya gwamnati za ta tuntuɓe su?
Kasancewarka ɗan Najeriya ba yana nufin cewa kowa ko kowane gida zai amfana daga wannan shirin karɓar naira 50,000 kyauta a kowane wata ba.
Dole ne mutum ya kasance cikin marasa galihu.
Mista Doro ya yi bayani game da mutanen da za su amfana daga wannan shiri.
"Ƙarƙashin wannan shiri, mutanen da suka cancanci amfana za su riƙa karɓar naira 50,000 a kowane wata, wanda zai samar da taimako kai tsaye domin biyan buƙatu na yau da kullum da rage nauyin tsadar rayuwa," in ji shi a cikin sanarwar.
A cewar ministan, za su riƙa duba shirin lokaci zuwa lokaci domin su ɗauki matakan da suka dace na sauƙaƙa wa ƴan ƙasa kan tsadar rayuwa.
Ya ƙara da cewa za a sanar da waɗanda ke cin gajiyar shirin kai tsaye kafin a yi wani sauyi.
Ministan ya kuma ce suna aiki tare da cibiyoyin hada-hadar kuɗi masu lasisi.
Ya ce an yi hakan domin tabbatar da cewa shirin yana gudana cikin tsaro, sauri ba tare da jinkiri ba, kuma ana isar da kuɗin bisa gaskiya ga waɗanda suka cancanta.
Masu amfana za su samu saƙonnin waya daga waɗannan kamfanoni.
Saƙon zai nemi amincewarsu kafin a tura kuɗin kai tsaye zuwa asusun ajiyarsu na banki ko walat ɗinsu na wayar salula.
Ministan ya bayyana cewa masu amfana ba sa buƙatar neman shiga shirin, biyan wani kuɗi, ko yin rajista ta hannun wasu wakilai domin samun damar cin gajiyar shirin.
Yaya za a kare shirin daga masu damfara?
Mista Doro ya gargadi 'yan Najeriya da su yi taka-tsantsan da masu damfara.
Ya shawarci duk wanda zai amfana daga shirin da kada ya ba ko ya bayyana wa kowa lambar sirrinsa (PIN) ko lambar BVN.
"Idan ba ka da tabbacin wani saƙo, ko wani ya nemi kuɗi daga gare ka, ka kira layin taimakon NERSI na hukuma a 0700-022-2222," in ji shi.
Ministan ya ce NERSI wani ɓangare ne na shirye-shiryen tallafa wa jama'a na gwamnatin tarayya da ake da su, yayin da zai taimaka wajen ƙarfafa samar da daidaiton tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa shirin ya yi daidai da manufar Renewed Hope Agenda ta Shugaba Bola Tinubu.
Haka kuma ya nuna aniyar gwamnati ta aiwatar da shirin cikin mutunci, gaskiya da adalci.
Wannan ne karo na uku da gwamnatin Najeriya ke ƙaddamar da wani shirin tallafi cikin wata guda saboda tsadar rayuwa.
A watan Oktoba, gwamnatin Najeriya ta samar da rangwamen man fetur na tsawon kwanaki 30, amma a gidajen man NNPCL ne kawai za a iya samun rangwamen.
'Yan kwanaki da suka gabata, gwamnatin Najeriya ta bayar da alawus-alawus na sufuri na naira 70,000 ga ma'aikata, lamarin da ya haifar da saɓani tsakanin Nigeria Labour Congress (NLC) da Trade Union Congress (TUC).
TUC ta ce ba za ta amince da tayin ba, tana mai cewa gwamnati ta fi dacewa ta ƙara albashi, amma NLC ta ce TUC ba ta da ikon ƙin abin da ba ta shiga cikinsa ba.