Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Zaɓen Amurka da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 4/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 4 ga watan Nuwamba, 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Shugaban Isra'ila ya soki kalaman wariyar launin fata da ke yi Larabawan ƙasar

    Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya soki abin da ya bayyana a matsayin kalaman wariyar launin fata da aka yi wa Larabawan Isra’ila bayan zaɓen majalisar dokoki da aka gudanar a makon da ya gabata, yayin da yake ƙoƙarin haɗa kan shugabannin jam’iyyu domin kafa gwamnati.

    Mista Herzog na tuntuɓar shugaban kowace jam’iyya domin yanke shawarar ko Firaminista Benjamin Netanyahu ko kuma ƙawancen adawa ƙarƙashin jagorancin Gadi Eisenkot ne zai fara yunƙurin kafa gwamnatin kawance.

    Falasdinawan da ke zaune a Isra’ila sun fito zaɓe da yawa, lamarin da ya ba su damar samun adadin kujeru mafi yawa a tarihinsu a majalisar dokoki.

    Dukkanin ɓangarorin biyu dai a baya sun yi watsi da yiwuwar yin haɗin gwiwa da jam’iyyun Larabawa na Isra’ila wajen kafa gwamnati.

  2. Amy Acton ta zama mace ta farko da aka zaɓa gwamnar Ohio

    A wani sabon tarihi da aka kafa a zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka, Amy Acton ta zama mace ta farko da aka zaɓa a matsayin gwamnar jihar Ohio.

    Amy Acton ta jam'iyyar Demokrats ta doke Vivek Ramaswamy ta Republican wata fafatawa mai zafi kan kujerar gwamnan wannan jiha da ke yankin tsakiyar yammacin Amurka.

    Baya ga Acton, wasu matan da suka kafa tarihi a ranar Talata sun haɗa da Deb Haaland, wadda ta zama mace ta farko daga cikin al’ummar asalin Amurka da aka zaɓa a matsayin gwamnar jihar New Mexico, da kuma Keisha Lance Bottoms, wadda ta zama mace baƙar fata ta farko da aka zaɓa a matsayin gwamna a wata jiha bayan nasararta a jihar Georgia.

  3. Masu tunanin samun sauyin ƙiyayyar Amurka ga Iran sun yi kuskure - Mojtaba

    Jagoran Addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya ce waɗanda ke tunanin sauye-sauyen siyasar Amurka za su kawo canji a “ƙiyayyar Amurka ga Iran” suna “cikin babban kuskure”.

    Khamenei ya kuma yi barazanar cewa idan Amurka ta sake kai hari kan Iran, martanin da za a mayar “zai ƙaru zuwa wani mataki mafi girma”.

    Jagoran Addinin, wanda ya gaji mahaifinsa Ali Khamenei wanda aka kashe a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai ranar 28 ga Fabrairu, bai fito bainar jama'a ba tsawon watanni.

    Kalaman sun fito ne cikin wani rubutaccen saƙo mai shafuka shida da aka fitar a yau domin tuna mamayar ofishin jakadancin Amurka da aka yi a Tehran a shekarar 1979.

  4. Wasu shugabannin duniya na maraba da nasarar Demokrats

    Ba abin mamaki ba ne ganin cewa wasu shugabannin ƙasashen da Donald Trump ya taɓa suka ko nuna adawa da su na maraba da gagarumar nasarar da jam'iyyar Democrat ta samu a zaɓen rabin wa'adi.

    • Firaministan Sifaniya, mai ra'ayin sassauci, Pedro Sanchez, ya ce Amurkawa sun zaɓi kawar da ƙiyayya, musun sauyin yanayi da kuma fifita masu gata a cikin al'umma.
    • Shi ma takwaransa Jonas Støre, firaministan ƙasar Norway, wadda Trump ya soko a makonnin baya saboda ba ta ba shi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ba, ya ce wasu sabbin muryoyi na tasowa a Amurka waɗanda suka fi dacewa da manufofin birnin Oslo.
    • Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda Trump ya zarga da aikata kisan kare dangi kan fararen fata, ya ce zaɓukan za su kawo sabon zamani a dangantakar ƙasashen duniya.
    • A wani ɓangaren kuma, mataimakiyar shugabar Majalisar Tarayyar Turai, Christel Schaldemose, ta ce tana da fata cikin taka-tsantsan cewa sakamakon zaɓen na iya haifar da ƙarin goyon baya ga Ukraine.
  5. Amurkawa sun nuna wa Trump cewa ba sa son yaƙi - Iran

    Shugaban Majalisar Dokokin ƙasar Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, wanda ke cikin manyan masu tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Iran, ya yi tsokaci kan sakamakon zaɓen tsakiyar wa'adin mulki da aka gudanar a Amurka.

    "Saboda lamiri ko kuma tsadar rayuwa, Amurkawa sun nuna ba sa son yaƙi, kuma muna goyon bayan wannan mataki," kamar yadda ya rubuta a shafin X.

    "Idan gwamnatin Amurka ta yi watsi da ra'ayin jama'arta domin yi wa wasu ƴan ƙasashen waje da masu yin barazana hidima, yanzu ta fahimci Amurkawa ba sa goyon bayan hakan''.

    Da yake magana da gidan talabijin na Fox News a baya, Donald Trump ya ce "dole ne mu yi wani babban abu" lokacin da aka tambaye shi kan rahotannin da ke cewa Amurka na shirin kai wasu hare-hare kan Iran, yana mai ƙara da cewa hakan na iya haɗawa da "mummunan hari".

  6. Demokrats na kafa sabon tarihi a zaɓen Amurka

    Democrat na kan hanyar ƙwace kujerun Majalisar Dattawan jihohin South Carolina da Kansas da Texas, waɗanda dukkansu a halin yanzu suna hannun jam'iyyar Republican kuma haka lamarin yake tsawon shekaru da dama.

    Rabon da jihar Kansas ta zaɓi ɗan Democrat zuwa Majalisar Dattawa yau kusan shekara 100 kenan da suka gabata, wato tun a shekarar 1932.

    Hakan ya faru ne a lokacin babban matsin tattalin arziki, kuma a shekarar ce ɗan jam'iyyar Democrat Franklin D Roosevelt ya samu gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasa.

    Ana kuma hasashen cewa ƴan takarar Democrat za su yi nasara a zaɓen majalisar dattawa da kuma na gwamna a jihar Texas, kuma duka biyun za su kasance karo na farko tun farkon shekarun 1990.

    Ɗan jam'iyyar Democrat na ƙarshe da aka zaɓa a matsayin gwamnan Texas ita ce Ann Richards a shekarar 1991.

    Ta yi wa'adin shekaru huɗu kafin ɗan jam'iyyar Republican George W Bush ya kayar da ita a zaɓe, wanda daga baya ya zama shugaban Amurka, bayan kammala wa'adinsa.

    Haka kuma, karo na ƙarshe da jam'iyyar Democrat ta lashe kujerar majalisar dattawa a jihar South Carolina shi ne a shekarar 1998.

  7. Demokrats ta ƙwace jihar Ohio daga hannun Republican

    Wannan sakamako ne mai ban mamaki kuma mai muhimmanci ga jam'iyyar Democrat a jihar Ohio, wadda ake hasashen za ta ƙwace kujera a Majalisar Dattawan Amurka tare da kuma karɓe kujerar gwamna daga hannun jam'iyyar Republican.

    Jihar ta kasance kagarar jam'iyyar Republican a tsawon lokacin mulkin Donald Trump, amma jam'iyyar Democrat ta karya wannan rinjaye nata a jihar.

    Wannan ya nuna girman nasarar da jam'iyyar ta samu a daren da ya gabata, domin jihar na daga cikin wuraren da aka fafata sosai kuma aka yi takara mai zafi.

    Trump ya ziyarci Ohio sau uku a lokacin wannan yaƙin neman zaɓe, saboda damuwar da ke akwai game da yadda jam'iyyarsa ke fuskantar.

    An bar kujerar Majalisar Dattawan ne babu mai riƙe da ita shekaru biyu da suka gabata, lokacin da JD Vance ya zama mataimakin shugaban ƙasa.

  8. Labarai da dumi-dumi, Demokrat na kan hanyar lashe zaɓen gwamnan jihar Texas

    Jam'iyyar hamayya ta Demokrats na kan hanyar lashe zaɓen gwamnan jihar Texas.

    Kafar yaɗa labarai ta CBS News ta ce ƴartakarar jam'iyyar Gina Hinojosa na kan gaba a sakamakon zaɓen da ke fitowa.

    Jam'iyyar Republican ce dai ke mulkin jihar tsawon shekaru

  9. Yaƙin Iran ne ya janyo wa jam'iyyarmu rashin nasara - Trump

    Shugaban Amurka ya ce yaƙin Iran ne ya janyo wa jam'iyyarsa ta Republican gagarumar koma-baya a zaɓen tsakiyar wa'adi na ƙasar.

    Kawo yanzu dai jam'iyyar ta rasa rinjaye a duka majalisun dokokin ƙasar biyu.

    Yayin wata hira da kafar yaɗa labarai ta Fox News, Shugaba Trump ya ce yaƙin ya haddasa tashin farashin gas a Amurka wanda kuma shi ne ya janyo wa Repblican baƙin jini.

    ''Mutane suna ji a jikinsu saboda suna sayen gas da tsada'', in ji shi.

    Shugaban na Amurka ya kuma ce dole Amurka ta yi wani abu kan Iran

    "Ba za mu bari su mallaki makamin nukiliya ba," a cewar Shugaba Trump.

  10. A shirye nake na yi aiki da Demokrats - Trump

    Yayin da ƴan takarar jam'iyyar Democrat ke ci gaba da samun nasara a zaɓukan tsakiyar wa'adin mulkin Amurka, Shugaba Donald Trump ya ce zai karɓi tsakamakon zaɓen.

    Cikin wata hira da Jaridar New York Times, Shugaba Trump ya ce a shirye yake "ya amince da wannan sakamakon", kuma yana shirye ya yi aiki tare da jam'iyyar adawa.

    "Gaskiya, muna sa ran yin aiki tare da su," in ji shi.

    "Mai yiwuwa mu cimma wata matsaya tare."

  11. Ministan sufurin Sifaniya ya ajiye muƙaminsa ya kuma haƙura da takara saboda hatsarin jirgin ƙasa

    Ministan Sufuri na Spain, Óscar Puente, ya yi murabus, kwanaki shida bayan hatsarin jiragen ƙasa wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 69 tare da jikkata wasu da dama.

    Ya sanar da matakin nasa a Majalisar Dokoki, bayan ya bayar da bahasi kan bala'in da ya faru a ranar Larabar da ta gabata kusa da garin Urda, da ke kudancin babban birnin ƙasar, Madrid, inda wani jirgin ƙasa ya buga bayan wani jirgin da ke tsaye.

    "Wani ministan sufuri a ƙasa irin Spain ba zai iya ci gaba da zama a muƙaminsa ba bayan hatsari biyu masu muni cikin ƙasa da shekara guda," in ji shi, yana mai nuni da hatsarin da ya faru a watan Janairu a kan wannan layin dogo, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 46.

    Hatsarin da ya faru a makon da ya gabata na ɗaya daga cikin munanan bala'o'in jirgin ƙasa mafi muni a tarihin Turai a wannan zamani, kuma shi ne mafi munin hatsarin jirgin ƙasa a Spain tun shekarar 2013.

    Puente ya sanar da matakin nasa ne a ƙarshen dogon zaman majalisar dokoki da aka yi a yammacin ranar Talata, inda ya yi bayani kan sabbin matakan tsaron layukan dogo, sannan kuma ƴan adawa suka yi masa tambayoyi masu tsauri.

    Ministan ya kuma sanar da janye takarar majalisar dokokin ƙasar da yake a zaɓen ƙasar da ke tafe

    "Ba wai kawai zan sauka daga muƙamina na ministan sufuri ba, na kuma janye daga takarar majalisar dokokin Sifaniya a zaɓe mai zuwa."

  12. Demokrats na kan hanyar ƙwace majalisun dokokin Amurka

    Babbar jam'iyyar hamayya ta Demokrats a Amurka na kan hanyar ƙwace iko da majalisun dokokin Amurka biyu.

    Yayin da sakamakon zaɓen ke ci gaba da fitowa Demokrats ta samu kureru 53 cikin 100 na majalisar dattawan ƙasar.

    Yayin da majalisar wakilai zuwa yanzu ta samu kujeru 224, yayin da Republican ta samu 134 cikin kujeru 358 da aka kammala fitar da sakamakonsu a yanzu.

    Zuwa yanzu dai ana dakon sakamakon zaɓen kujerun majalisar wakilai 77.

    Jagoran jam'iyyar, wanda kuma shi ne tsohon shugaban ƙasar, Barack Obama ya ce sakamakon alama ce da ke nuna cewa ƙarara Amurkawa na buƙatar chanji.

  13. Jam'iyyar Trump na shan mummunan kaye a zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka

    Jam'iyyar Republican ta Shugaba Trump na ci gaba da shan gagarumin kaye a zaɓukan tsakiyar Amurka.

    Yayin da sakamakon zaɓen ke ci gaba da fitowa, jam'iyyar hamayya ta Demokrats ta kama hanyar ƙwace rinjayen majalisar dattawa da ta wakilan ƙasar.

    Kafin wannan zaɓen dai jam'iyyar Republican ce kje da rinjaye a duka majalisun biyu.

    Tun kafin zaɓen ne dai masu nazarin siyasar ƙasar suka yi hasashen Demokrats za ta ƙwace iko da majalisar wakilai, amma ba a yi zaton za ta ƙwace iko a majalisar dattawa ba.

  14. Sallama

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki, musamman sakamakon zabukan tsakiyar wa'adin Amurka.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.