Ministan sufurin Sifaniya ya ajiye muƙaminsa ya kuma haƙura da takara saboda hatsarin jirgin ƙasa

Asalin hoton, Reuters
Ministan Sufuri na Spain, Óscar Puente, ya yi murabus, kwanaki shida bayan hatsarin jiragen ƙasa wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 69 tare da jikkata wasu da dama.
Ya sanar da matakin nasa a Majalisar Dokoki, bayan ya bayar da bahasi kan bala'in da ya faru a ranar Larabar da ta gabata kusa da garin Urda, da ke kudancin babban birnin ƙasar, Madrid, inda wani jirgin ƙasa ya buga bayan wani jirgin da ke tsaye.
"Wani ministan sufuri a ƙasa irin Spain ba zai iya ci gaba da zama a muƙaminsa ba bayan hatsari biyu masu muni cikin ƙasa da shekara guda," in ji shi, yana mai nuni da hatsarin da ya faru a watan Janairu a kan wannan layin dogo, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 46.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Hatsarin da ya faru a makon da ya gabata na ɗaya daga cikin munanan bala'o'in jirgin ƙasa mafi muni a tarihin Turai a wannan zamani, kuma shi ne mafi munin hatsarin jirgin ƙasa a Spain tun shekarar 2013.
Puente ya sanar da matakin nasa ne a ƙarshen dogon zaman majalisar dokoki da aka yi a yammacin ranar Talata, inda ya yi bayani kan sabbin matakan tsaron layukan dogo, sannan kuma ƴan adawa suka yi masa tambayoyi masu tsauri.
Ministan ya kuma sanar da janye takarar majalisar dokokin ƙasar da yake a zaɓen ƙasar da ke tafe
"Ba wai kawai zan sauka daga muƙamina na ministan sufuri ba, na kuma janye daga takarar majalisar dokokin Sifaniya a zaɓe mai zuwa."


